zababun Aiyuka-Mahimancin Tausayi
shirin na yau zai bayyani a kan tausayi a kan rahama ga dukkanin halittun Allah domin shima na daga cikin kyawawen dabi’un da Allah madaukakin sarki ke so
Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, da ni Aminu Abdu ke gabatar da shi,shirin na yau zai bayyani a kan tausayi a kan rahama ga dukkanin halittun Allah domin shima na daga cikin kyawawen dabi’un da Allah madaukakin sarki ke so.
********************Musuc************************
Masu saurare,Rahama na daga cikin dabi’un Allah Tabaraka wa ta’ala kuma dabi’antuwa da wannan dabi’a na yin sanadiyar samun rabauta da soyayyar Allah madaukakin sarki, kamar yadda masoyinmu mai shiryarwa kuma zabebben Allah (s.a.w) ya shiryar da mu a cikin riwayar da shekh Tusy ya ruwaito cikin littafinsa Amaly ya ce:(hakika Allah madaukakin sarki mai tausayi ne kuma yana son duk mai tausayi), dabi’antu’antuwa da wannan dabi’a na daga cikin sifofin mabiyan masu gaskiya ga Annabawa gaba daya kamar yadda Allah madaukakin sarki ke fada cikin littafinsa mai tsarki a suratu Hadidi Aya 27 (sannan muka bibiyar da manzanninmu a gurabansu, Muka kuma bibiyar da (Annabi) Isa Dan Maryamu muka kuma bashi Injila, kuma muka sanya tausayi da jin kai a zukatan wadanda suka bi shi….) kamar yadda wasici da wannan dabi’a mai girma na daga cikin alamomin imani na gaskiya, a cikin suratu Baladi Aya ta 17 da kuma ta 18, Allah madaukakin sarki ya ce:(sannan kuma ya zama daga wadanda suka bada gaskiya,suka kuma yi wasiya da hakuri, kuma suka yi wasiya da tausayi*wadancan su ne ma’abota dama (wato dacewa)). Masu saurare, dabi'antuwa da wannan dabi'a na na yin sanadin samun rabauta da rahamar ubangiji ranar da Dukiya gami da 'ya'ya bas a amfani, sayyid Kutubuddin Rawanda cikin Littafinsa Adda'awat ya ruwaito Ma'aikin Allah (s.a.w) ya ce (idan ya kasance Ranar Alkiyama, mai kira zai kira, wanda ke cikin Kabari zai tashi:ya ce Ya Ubangiji ka ji kai na,sai a amsa masu da cewa,idan kun ji kan mutane a duniya za a ji kanku a yau).bayan haka, shugaban mumunai Aliyu bn Abi talib (a.s) ya bayyana cewa daga ma’anar dabi’ar tausayi da jin kai ya fice fage dukiya ko abin Duniya ta shafi dukkanin tausayi har sanya kyakkyawan fata da cikin zukatan da suka karaya, a cikin Littafin Guraru Hikam wa Duraru Kalam an ruwaito hadisi daga Imam Ali(a.s) ya ce:(idan dukiyarka ta kasa wajen taimakawa masu rauni , ka wadatasu da tausayi gami da jin kai) har ila yau hadisan iyalan gidan Ma’aikin Allah tsarkaka sun bayyana tabbacin jin kai ga sahabanmu, a cikin littafin Kurbul Isnad, an ruwaito hadisi daga Annabi Muhamad tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(ku ji kan shugaban mutanan da ya zamanto wanda ake milka, da mai kudin da ya talauce da kuma mai masanin da ya bace cikin zamanin Jahilai) har ila yau a cikin littafin Alkhisal, an ruwaito hadisi daga Imam Sadik (a.s) ya ce:( hakika ina jin kan mutane uku kuma hakki ne a jikansu, na farko mai milkin da kaskanci ya same shi bayan buwaya, da mai kudin da bukata ta same shi bayan arzuki, sai kuma malamin da yake tsoron Ahlinsa da jahilai) kamar yadda daga cikin dabi’ar tausayi gami da jin kai, tseto ga mabukaci da ya bada abinda ya mallakada kuma wanda ya gaji, a cikin littafin Khisal an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah (s.a.w) ya ce :(dukkanin kyautatawa sadaka ce,kuma wanda yayi umarni ga alheri kamar ya aikata shi ne, Allah na son taimakon wanda ke cikin bakin ciki da wanda zuciyarsa ta karaya)a cikin littafin Amaly na shekh Tusiy, an ruwaito wani hadisi, inda a cikin Imam Ali (a.s) yayin da yake kan gadon mutuwa yay i wasici da cewa:(ina yi muku wasiya da kyakkyawar makobtaka, girmama bako,jin kai wanda ya gaji da kuma mutanan da suka fada cikin ibtila’I, ku kuma sada zumunci, ku so miskinai da majlisinsu ko kuma gurin zamansu)
***************************Musuc*******************************
Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai yi bayyani kan yin musabaka wajen sada zumunci, domin dabi’antuwa da wannan dabi’a na a matsayin misdakin amincewa da karbar daya daga cikin kautar Allah madaukakin sarki kamar yadda shugabanmu Imam Sadik (a.s) yayi ishara da shi, a cikin hadisin da shekh Mufid ya ruwaito cikin Littafinsa mai suna Arrauda, imam (a.s) ya ce: (mumani kautar Allah madaukakin sarki ne gad an uwansa mumuni, idan ya sanya shi farin ciki, hakika ya karbi kautar da Allah madaukakin sarki ya bashi, idan kuma ya yanke ziyartarsa kuma ya kaurace masa,to hakika ya yi watsi da kautar Allah madaukakin sarki) muna neman tsari da Allah madaukakin sarki na yin watsi da kautarsa ta hanyar yanke zumanci da kuma kauracewa ‘yan uwanmu, mu kuma saya Iblis la’ancecce ya ci gaba da far’a, a cikin Littafin kafi an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik(a.s) ya ce:(ba zai kushe Iblis yana cikin fara’a ba a lokacin da musulmai biyu suka kauracewa junansu, amma duk lokacin da suka hadu sai guwarsa ta yi sanyi,fatansa ya tsinke yana fadar cewa kaucona da wannan bala’i)masu saurare daga cikin dabi’ar sada zumanta, yin musabaka wajen sake sada zumunci, idan ya yanke, domin yin hakan rigangeniya ne na rabauta a gidan Aljanna, a cikin littafin Kafi an ruwaito hadisi daga ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(duk musulmi biyu da suka kauracewa juna kwanaki uku, za su fita daga Addinin Islama da kuma wulaya, kuma duk wanda ya rigayi dan uwansa yima magana, ya riga shi rabauta da gidan Aljanna a ranar hisabi), a bangare guda kauracewa juna da yanke alaka a tsakanin musulmi yana hana karbar kyawawen aiyuka, hakika ya zo cikin wasiyar Ma’aikin Allah (s.a.w) ga Abi Zar Algaffari yardar Allah ta tabbata a gare shi a hadisin da aka ruwaito cikin Littafin Amaly na sheikh Tusy, Ma’aikin Allah (s.a.w) ya ce:(Ya Aba Zar, ka kiyaye kauracewa Dan uwanka mumuni, domin aiki bay a karbuwa tare da kauracewa, idan kuma ya kasance ya zamanto maka dole da ka kaurace masa, to kadda ka kaurace masa sama da kwanaki uku, domin duk wanda yam utu a cikin halin kaurecewa dan uwansa, wuta ce tafi dacewa da shi).
Masu saurare, hadisai da dama sun bayyana yin rigai wajen sake kula zumanci ga wanda suka kauracewa juna musaman ma ga wanda aka zalunta,zai zamanto dalilin samun rabuta da nasarar ubangiji, a gefe guda guma akasin hakan zai kasance dalilin fushin ubangiji, a cikin Litattafan Kafi, Tuhuful Ukul da saurensu, an ruwaito hadisi daga Imam Ja’afaru Sadik (a.s) ya ce:(wallahi ba za su rabu mutane biyu daga cikin mabiyanmu a kan suna gab aba, sai daya daga cikinsu la’ana da bara’a ta wajabta a kansa ba, kai mai yuyuwa La’anar ta wajaba a kan dukkaninsu guda biyun).har ila yau a cikin wani hadisi na daban Imam Ja’afaru Sadik (a.s) ya ce :(na ji babana Imam Muhamad Bakir (a.s) yana cewa:idan mutane biyu daga cikin mabiyanmu suka yi rikici,idan daya ya nuna galaba a kan dan uwansa, wanda aka zalintar ya koma wajen abokin rikicin nasa sannan yace masa Ya Dan uwana na yi kuskure ka yafe min, har ya samu ya katse kauracewar da ta shiga tsakaninsa da dan uwansa, hakika, Allah tabarka wa ta’ala mai hukunci kuma mai adalci ne yana karbar wanda aka zalinta daga Azzalimi).
***********************Musuc*******************************
Masu saurare, anan za mu dasa aya, ganin lokacin da aka debawa shirin ya zo karshe, sai kuma a maku na gaba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin dukkanin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala, ni madugun shirin nike muku fatan Alheri, wassalama alekum warahamatullahi