zababun Aiyuka-Kiyayye Sirrin Mutum
shirin na yau zai yi bayyani kan mahimancin kiyaye sirrin Mutane domin yin hakan na daga cikin kyawawen dabi’un musulinci
Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,shirin na yau zai yi bayyani kan mahimancin kiyaye sirrin Mutane domin yin hakan na daga cikin kyawawen dabi’un musulinci, amma kafin mu shiga cikin shirin ga wannan.
*******************Musuc*********************************
Masu saurare, hadisai da dama sun umarci musulci da su halarci mazlisi ko gurin zaman dake rike wa juna Amana kuma su kaucewa majlisin da ake bankado da sirrin mutane, daga cikin wasicin da shugaban halittu Muhamad Dan Abdullah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya yiwa babban sahabinsa Aba Zarur Gaffari ya ce:(Ya Aba Zar, Majlisi ko gurin zama shine wanda yake rike da amana, fallasa sirrin dan uwanka khiyana ne don hakan ka kiyayi hakan) masu saurare daga cikin misdakin wannan hali kyau boye duk wani abu da Mutune zai yi ga sirrin wasunsa da bas a so wasu su san da shi,a cikin Littafin Al’Ikhtisas shekh Mufid yardar Allah ta tabbata a gareshi, ya ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Ali (a.s) ya ce:(an haka dukkanin alherin duniya da Lahira wajen boye sirri da gaskanta zababbu daga cikin bayin Allah, kuma an hada dukkanin sharri wajen saurare zantukan mutane gami da yin abotaka tare da malalata) a cikin wani hadisi na daban kuma za mu fahimci cewa dabi’antuwa da dabi’ar kiyaye da boye sirri dan uwa na daga cikin dabi’antuwa da dabi’un Allah madaukakin sarki, fallasa sirrin mutune yak an yin sanadiyar fishin Allah madaukakin sarki,hakika cikin littafin Al’ikhtisas an ruwaito hadisi daga shugaban mu Imam Sadik (a.s) ya ce:(duk wanda ya samu labarin wani sabo ko kuma kuskure na dan uwansa mumuni, ya fallasa bai boye ba, kuma bai roka masa gafara a wajen Allah ba, zai kasance a wajen ubangiji kamar wanda ya aikata sabon, kuma yanada zunubin duk wanda ya ci gaba da fallasa wannan abu)
Masu saurare mumunar dabi’ar ta fallasa sirrin mutane ta kan kasacewa sanadiyar cikin gungun da Allah madaukakin sarki zai yi musu azabar mai radadi ba wai a ranar Lahira kawai ba, har ma tun daga nan duniya kamar yadda ya zo cikin Al’kur’ani mai tsarki, a cikin Littafin Ikabul A’amal,sheikh Saduk ya ruwaito hadisi daga Muhamad bn Mudail ya ce wa Imam Musa Alkazim (a.s) fansar kaina a gareka,wani mutune daga cikin ‘yan uwana ya fada mani abu da nike kyamarsa sai na tambayesa kan inda ya samu labarin sai yaki ya gyayamin yana cewa hakika batun ya fito daga bakunan da ba sa karya, yaya zan yi ?sai Imam Kazim (a.s) ya amsa masa da cewa:(Ya Muhamad jinka da ganinka ya yi maka karya kan abinda ka ji daga wajen dan uwanka, kadda ka rike shi a zuci, ya rusa soyayyar dake tsakaninku,sai ka kasance daga cikin mutanan da Allah madaukakin sarki yake cewa ( Hakika wadanda suke son yaduwar mumunan abu game da wadanda suka yi imani suna da (sakamakon) azaba mai radadi a duniya da Lahira, kuma Allah (shi) yake da sani,ku kuma ba abinda kuka sani)suratu Nur Aya ta 19, a bangare guda wasu hadisai sun bayyana cewa rashin dabi’antuwa da dabi’ar kiyaye sirrin mutane da kuma kokari wajen zubar da mutuncin mumuni a idanun mutane yak an fitar da mai yin hakan daga wulayar Allah da taimakonsa, a cikin littafin kafi an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:(duk wanda ya dauko wani zance na mumuni da niyar tozarta shi ko kuma bata sunansa tare da zubar da mutuncinsa a idanun Mutane, Allah zai fitar da shi daga cikin wulayarsa sannan ya sanya shi cikin wulayar shaidain da kuma shi kansa shaidan ba zai amince da soyayyarsa ba).
*****************************Musuc****************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai yi bayyani kan mahimancin tsarkake kai daga yada Alfahsha gami miyagun kalamai tare kuma da yin la’ana zaki ga bayin Allah,a cikin suratu Nur Aya ta 19, Allah madaukakin sarki ya ce:( Hakika wadanda suke son yaduwar mumunan abu game da wadanda suka yi imani suna da (sakamakon) azaba mai radadi a duniya da Lahira, kuma Allah (shi) yake da sani,ku kuma ba abinda kuka sani) wannan Aya mai albarka na yin hani kan yada mumanan labarai a tsakanin Al’umma, a cikin Littafin Ikabul A’amal na shekh Saduk, an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(duk wanda ya ji wani mumunan labari kuma ya yada shi, kamar wanda ya zo da shi ne, kuma duk wanda ya ji kyakkyawan labari ya yada shi kamar wanda ya aikata shi ne), har ila yau a cikin wata riwaya ta daban Manzon Allah(s.a.w) ya ce:(duk wanda ya yada mumunan labari,zai kasance kamar wanda ya aikata shi da farko, kuma duk wanda ya shafawa mumuni wani mumunar abu, ba zai mutu ba, har sai ya fada cikin wannan mumunan abun da ya shafawa dan uwansa mumuni). Masu saurare, hadisai da dama sun hana la’ana ko zaki ga wanda bai canci a zake shi ko kuma a la’ance shi ba, domin zakin ko la’ana zai koma kan wanda yayi shi. A cikin Littafin Kurbul Isnad, an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:(idan La’ana ta fita da cikin baki, za ta kira kai kawo tsakanin wanda ya yita da kuma wanda aka yiwa, idan ta hanu da wanda aka yiwan ya caccanci a yima to sai ta fada kansa, idan kuma bai caccanci hakan ba, to zai ta koma kan wanda yayi ta, domin shi ya fi caccanta da ita, ku kiyayi la’antar mumuni, domin la’antarku za ta dawo muku). Amma abin ya shafi zaki, hakika Alkur’ani mai girma ya hanemu da shi, kai har ma da abin bautar mushrikai, domin kadda yin hakan ya yi tasiri a garesu har ya dawo suna zakin abin bautarmu, a cikin suratu An’ami Aya ta 108, Allah tabarka wa ta’ala ya ce:(kada kuma ku zagi wadanda suke bauta wanin Allah, sai su zagi Allah saboda shisshigi ba tare da sanin (girmansa) ba. Kamar haka ne Muka kawata wa kowace al’umma ayyukansu (na alheri da na sharri) sannan (kuma daga karshe) warin Ubangijinsu ne makomarsu, sannan ya basu labarin (irin ) abin da suka kasance suna aikatawa),a cikin littafin kafi, an ruwaito hadisi daga Manzon Allah (s.a.w) inda mutune ya je wajensa ya ce ya yi masa wasici, daga cikin wasiyar da ya yi masa ya ce:(kada ka zaki mutane domin zaki yana gadar da kiyayya a tsakaninku) har ila yau a cikin wani hadisin, an tambayi shugabanmu Imam Kazim (a.s) a kan mutane biyu dake zakin junansu, sai ya ce:(wanda ya fara daga cikinsu shi ne ya fi zalunci, zunubinsa da zunubin abokin fadansa yana kansa matukar bai nemi gafara daga wanda ya zalintar ba) a karshe bari mu karkare shirin da kalamin Amiru mumunin Aliyu bn Abi talib (a.s) da aka ruwaito cikin littafin Nahjul-balaga (hakika ina muku kyamar ku kasance daga cikin masu yawan zagi, saidai da kun gwada aiyukanku da kuma anbatun halinsu ya fi zama alheri, idan wasu suka zake ku kuce musu zakin ku ya koma muku…..)
******************************Musuc*******************************
Masu saurare a nan za mu dasa aya, ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe sai kuma a maku na gaba za a jimu dauke da wani sabon shirin, a madadin wadanda suka tallafawa shirin har ya kammala ni da shirya kuma na gabatar nike muku fatan alheri, wassalama alekum warahamatullahi ta’ala wa barka tuhu.