Mar 04, 2016 16:41 UTC
  • zababun Aiyuka-Kuzari wajen neman Halal

shirin na yau zai yi bayyani kan mahimancin kuzari a yayin neman arziki na halal


Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,shirin na yau zai yi bayyani kan mahimancin kuzari a yayin neman arziki na halal, kuma hakan ya shafi dukkanin bangarorinsa na zahiri da badini, amma kafin mu shiga shirin ga wannan.


***************************Musuc************************


Masu saurare, hakika Allah madaukakin sarki ya yabawa masu irin wadannan dabi’a mai kyau inda ya kira su da masu gaskiya a cikin ayoyi da dama na Alkur’ani mai tsarki, a cikin suratu Hashari, Aya ta 8, Allah madaukakin sarki ya ce:(ga mabukata masu hijra wadanda aka fitar da su daga gidajensu da dukiyoyinsu (duk suka bar su) suna neman falalar daga Allah da yarda,suna kuma taimakon (Addinin )Allah da Manzonsa, wadancan su ne magaskanta) wadannan sune masu neman falalar ubangiji ta hanyar yin hijra da kuma bayar da gudin muwarsu ga Addinin Allah gami da manzonsa, kamar yadda Alkur’ani  mai tsarki ya yabi masu neman falalar Allah ta hanyar yin bulaguro domin kasuwanci, a cikin suratu Muzzammilu Aya ta 20, Allah tabaraka wa ta’ala ya ce:(Ya tabbata cewa daga cikinku a kwai wadanda za su kasance marassa lafiya, wadansu kuma suna tafiya  a bayan  Kasa don fatauci suna neman falala daga Allah, wadansu kuwa suna yin yaki saboda Allah, to sai ku karanta abinda ya saukaka daga gare shi (Alku’ani) ku kuma tsayar da Salla,ku kuma ba da zakka, kuma ku baiwa Allah rantse kyakkyawa. Kuma abin da kuka gabatar wa kanku na wani Alheri to za ku same shi wurin Allah, shi ya fi alheri ya kuma fi girman lada.)


Masu saurare, hadisai da dama sun shiryar da mu cewa kokari wajen neman halal na kasancewa sanadiyar samun buwaya da kuma daukaka, hakika shekh saduk a cikin littafinsa na Man La Yahdurul fakih, ya ruwaito hadisi daga Mu’ala bn Khanis ya ce:( babban Abdullah Imam Sadik (a.s) ya ganni ina sauki a yayin da na yi lattin zuwa kasuwa sai ya ce mini ka gaggauta isa zuwa neman buwaya da daukakarka), a cikin littafin kafi an ruwaito hadisi daga shugaban mumunai Aliyu bn Abi talib (a.s) ya ce:(ku yi kasuwanci domin a cikinsa a kwai arzikinsu daga abinda ke hanun mutane) har ila yau an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) yayin da daya daga cikin sahabansa ya shaida masa cewa ya bar kasuwanci , sai Imam (a.s) ya ce masa ko minene dalilinsa na yin hakan? kada ku daina kasuwa, ku nema daga falalar Allah madaukakin sarki).a cikin littafin Man La Yahdurul Fakih, an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Bakir (a.s) ya ce:(duk wanda ya nemi duniya cikin karrama  mutane, da kuma bukatar wadatar da iyalansa da kuma tausayin makobtansa, ranar kiyama zai hadu da Allah madaukakin sarki, fuskarsa tana haske kamar wata a daren Badar wato ranar goma sha hudu). Imam Bakir (a.s) ya yi ishara da dabi’un kakansa Murtada (a.s) da kuma kyakkyawar niyarsa dangane da wannan dabi’a, ya ce: shugaban mumunai Aliyu bn Abi talib (a.s) ya kasance ya na fita cikin mawuyacin zafi domin neman halal, ya ce ya na son Allah ya gansa yana wahala wajen neman halal). Har ila yau a wata riwayar ta daban Amiru mumunin (a.s) ya bayyana cewa:(hakika Allah yana son masu wahala wajen neman arzikinsu  na halal).


******************************Musuc*************************


Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai yi bayyani kan mahimancin ambaton Allah yayin neman halal, domin yin hakan na daga cikin kyawawen dabi’un da Allah madaukakin sarki yake so ga bayinsa, a cikin suratu Jumu’a Aya ta 10,Allah madaukakin sarki ya ce:(sannan idan aka idar da salla, sai ku bazu a cikin kasa, ku kuma nemi falalar Allah, ku kuma ambaci Allah da yawa don ko kwa rabauta)shekh Tabrasi cikin tafisirinsa na Majma’ul bayan, ya ruwaito  hadisi daga ma’aikin Allah (s.a.w) ya ce:(duk wanda ya ambaci Allah cikin ikhlasi a kasuwa yayin da mutane suka gafala da kuma shagala wajen harakokin kasuwancinsu, Allah madaukakin sarki zai rubuta masa lada dubu kuma ya gafarta masa ranar kiyama,). A cikin littafin Man La Yahdurul Fakih, an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce :(duk wanda ya ambaci Allah a kasuwa Allah zai gafarta masa iya adadin ahalinsa). wani hadisi na daban kuma ya bayyana girman ladan dake tattare da ambaton Allah madaukakin sarki a yayin kasuwanci, a cikin littafin Kafi an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce : idan dayanku ya kammala salar farilla ya kuma fito daga cikin masallaci sai ya tsaya a kofar masallacin sannan ya ce:(ya Ubangiji ka kirani kuma na amsa kiranka, na yi kuma sallar da ka rubutamin, zan bazu cikin kasar kamar yadda ka umarce ni,ina tambayarka daga falalarka aiki da umarninka kuma in kiyaye abin zai janyo fishinka, da kuma riko da Arzikinka don rahamarka ). Har ila yau daga cikin misdakin ambaton Allah a yayin neman halal, a cikin littafin Man La Yahduruhul fakih, an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) a yayin da yake bayyani kan ma’anar wannan Aya (Su Mazaje ne wadanda kasuwanci da saye da sayarwa bas a shagalartar da su daga ambaton Allah)suratu Nur Aya ta 37, imam (a.s):(sun kasance ‘yan kasuwa idan lokacin salla ya yi sais u bar saye da sayarwa sannan su gaggauta amsa kiran ubangiji su je su yi salla kuma su sunada girman ladan da ya fiye musu abinda za su sayar). Masu saurare ko shakka babu bukatuwa da ambaton Allah a yayin kasuwanci yana tunatar da mutune tare da kare sa daga fadawa cikin gafala na cin haram, yayin da yake yiwa Imam Ali (a.s) wasici, ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(Ya Ali! Ababe guda uku ba za su sauka daga kan wannan Al’umma ba, juyayi ko kuma taimakon dan uwa cikin dukiyarsa, yiwa mutane adalci a karan kansa,da kuma ambaton Allah a ko wani hali……..idan ya ga zai shiga cikin haram zai ji tsoron Allah madaukakin sarki ya guje shi), a cikin Littafin Almahasin an ruwaito hadisi daga shugabanmu Muhamad Bakir (a.s) inda yake ishara kan Addu’ar da mutune ya kamata ya karanta a yayin da zai shiga kasuwa ko kuma ma’aikatarsa ya ce:(Ya Ubangiji ina tambayarka daga falalarla, kuma ina neman kariya daga gareka daga Zalinci,asara da kuma sabo ), a karshe masu saurare bar i mu karanto wasiyar da shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya yi wa daya daga cikin sahabansa( na hare ku da tsoron Allah, da kuma abinda ake samu a wajen Allah,wallahi babu wani abu da muke umurtarku sai abinda muke umartar kawunanmu da su, mu horeko da kokari gami da kuzari,idan kuma kun yi sallar Assuba, ku watsu a cikin kasa, ku gaggauta neman Arziki, ku nemi halal, domin Allah tabaraka wa ta’ala zai arzutaku kuma ya taimake ku a kan hakan)


************************Musuc***************************


Masu saurare a nan za mu dasa aya, ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe sai kuma a maku na gaba za a jimu dauke da wani sabon shirin, a madadin wadanda suka tallafawa shirin har ya kammala ni da shirya kuma na gabatar nike muku fatan alheri, wassalama alekum warahamatullahi ta’ala wa barka tuhu.