Mar 04, 2016 16:47 UTC
  • zababun Aiyuka-Mahimancin kyautatawa

shirin na yau zai yi bayyani kan mahimancin kyautatawa domin yin hakan na daga cikin kyawawen dabi’un musulinci

Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,shirin na yau zai yi bayyani kan mahimancin kyautatawa domin yin hakan na daga cikin kyawawen dabi’un musulinci, amma kafin mu shiga cikin shirin bari mu saurari wannan.
*****************************Musuc****************************
Masu saurare daga cikin mafi girman albarkatun dake tattaure da dabi’ar Ihsani ko kuma kyautatawa, samun rabauta da soyayyar Allah madaukakin sarki, kamar yadda Ayoyi da dama na Alkur’ani mai tsarki suka yi ishara da hakan, a cikin suratu Bakara Aya ta 195,Allah madaukakin sarki ya ce:(ku kuma ciyar (da dukiyoyinku)cikin hanyoyin Allah, kada kuma ku jefa kanku cikin hallaka, kuma ku kyautata, hakika Allah yana son kyautatawa). A cikin suratu Ali Imrana Aya ta 134Allah madaukakin sarki ya ce:(wadanda suke ciyarwa cikin halin yalwa da matsi da masu hadiye fishi,da masu yafe wa mutane. Allah kuwa yana son masu kyautatawa) kamar yadda daga albartun dabi’ar kyautata, kari daga taimakon Allah,karamci da kuma rahamarsa ta musaman, a cikin suratu A’arafi Aya ta 161, Allah madaukakin sarki ya ce:(kuma ku tuna lokacin da aka ce (da iyayensu) ku zauna a wannan Alkarya, kuma ku ci gaba daga kare ta a duk inda kuke so, kuma ku ce Allah ka shafe mana kurakuranmu, kuma ku shiga kofar kuna masu sujada, za mu gafarta muku zunubanku.Da sannu za Mu kara (rabon) kyautatawa), a cikin suratu Ali imarana Aya ta 148 Allah madaukakin sarki ya ce:(sai Allah ya ba su ladan duniya da kuma kyakkyawan ladan lahira (shi ne Aljanna) Allah kuwa yana son masu kyautatawa) har ila yau cikin suratu A’arafi Aya ta 56 Allah tabaraka wa ta’ala ya ce:( hakika rahamar Allah kusa take da masu kyautatawa) masu ayoyi da dama sun bayyana cewa masu wannan dabi’a za su rabauta da karfafawar Allah kan aiyukan da suke yi tare kuma da taimakon su a kan aiyukansu tare da kyautatawarsu da kuma al’amuransu, a cikin suratu Nahli Aya ta 127 da kuma ta 128 Allah madaukakin sarki ya ce:(kuma ku yi hakuri (bisa abinda ya same ka), ba kuwa z aka iya hakurin ba sai da taimakon Allah,kada ranka ya bace a kansu, kada kuma ka zama cikin kunci game da abin da suke kullawa*Hakika Allah Yana tare da wadanda suke jin tsoron Sa da kuma wadanda suke masu kyautatawa ne) kamar yadda Allah yake kare bayinsa da suka dabi’antu da wannan dabi’a daga cutuwa kuma ya canza mu su lullebe su da Rahamarsa gami da gafararsa,a cikin suratu Tauba Aya ta 91 Allah tabaraka wa ta’ala ya ce:(babu wani laifi a kan raunana ko marassa lafiya, ko kuma wadanda ba su sami abin da za su ciyar ba(don talauci), matuka dai sun tsarkake zuciyarsu ga Allah da Manzonsa. Babu wata hanya(ta dora laifi) ga masu kyautatawa. Allah kuwa Mai gafara ne Mai jin kai) kamar yadda rabauta daga hikimar ubangiji na daga cikin shiriyar Ubangiji da Allah madaukakin sarki yak e so gamasoyansa da suka dabi’antu da dabi’ar kyautatawa. A cikin suratu Yusuf Aya ta 22 , Allah tabaraka wa ta’ala ya ce:(lokacin kuma da karfinsa ya kawo sai muka bashi hikima da ilimi. Kamar haka Muke saka wa masu kyautatawa)
************************Musuc*****************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa,ci gaba shirin zai bayyani kan yin biyyaya ga iyaye tare kuma da kyautata musu, domin hakan na daga ababen da Allah madaukakin sarki ya yi wasici a kan kansa , hakika ayoyi dadama sun yi ishara da hakan bayan ibadar Allah madaukakin sarki , Allah ya kebenta yin biyayya ga ma’aifata tare da kuma kyautata musu, saman ya gabatar da yin hakan ga Salla gami da zakka.a cikin suratu Bakara Aya ta 83, Allah tabaraka wa ta’ala ya ce:(kuma (ku tuna) lokacin da muka daura alkawari da Bani-Isra’ila (kan) kada ku bauta wa (kowa) sai Allah, kuma ku kyautata wa ma’aifa da makusanta da marayu da miskinai kuma ku rika yi wa mutane kyakkyawar magana, ku tsaida salla ku ba da zakka, sannan  kuka bada ba ya sai kadan daga cikinku,alhali kuwa kuna masu bijerewa da (alkawarin)) kamar yadda dabi’antuwa da wannan dabi’a ke daga wasiyoyin Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ga Al’ummarsa domin hakan na daga cikin alamar Imani,hakika cikin littafin Kafi, sikatu Islam Kuleini ya ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s)ya ce:(wani Mutune ya je wajen Ma’aikin Allah (s.a.w) ya ce ya Ma’aikin Allah ka yi mani wasici, sai ya ce masa kada ka hada bautar Allah da kowa koda za kona ka da wuta da kuma duk irin azabar da z aka fuskanta zuciyarka ta kasance mai nutsuwa da imani, kuma ma’aifanka ka yi musu biyayya, biyayyarka da su ta kasance suna raye ko kuma sun koma ga Allah, idan suka umarce ka da ka fita daga cikin iyalanka da kuma dukiyarka to ka bi umarninsu,domin yin hakan na daga Imani).wannan ita ce wasiyar annabta wadda take wasiya ce daga Allah madaukakin sarki, a cikin suratu An’ami Aya ta 151 Allah madaukakin sarki ya ce:(ka ce (da su) ku taho in karanta muku.” Kada ku tara wani abu da shi, kuma a kyautata wa ma’aifa, kada kuma ku kashe ‘ya’yanku don talauci, da ku da su Mu za Mu arzuta ku, kuma kada ku kusanci munanan (ayyuka) na sarari da na boye, kuma kada ku kashe ran da Allah ya haramta (kashe shi) sai dai idan da wani hakki. wannan (Allah) ya yi muku wasiya da shi don ku hankalta.) masu saurare yin biyayya ga iyaye na daga cikin mafi girman dabi’u da suke samar wa mai shi yardar Allah madaukakin sarki, ya kuma gabatar da shi har a kan jihadi wanda na daga cikin abebeb da suke budewa Bawa kofofin Aljanna, a cikin littafin Kafi an ruwaito hadisi daga Imam ja’afaru Sadik (a.s) ya ce:(wani mutune ya je wajen ma’aikin Allah (s.a.w) ya ce Ya Ma’aikin Allah ni mai kwadayin yin jihadi, sai Annabi (s.a.w) ya ce masa ka yi jihadi saboda Allah, hakika idan aka kashe ka za ka kasance rayayye a wajen Allah ana kuma arzutar da kai,idan kuma baka mutu ba, hakika ladanka zai kasance wajen Allah,idan kuma ka dawo, z aka koma gida an  karkare zunubanka ka kasance kamar yadda ma’aifiyarka ta aifeka, sai wannan Mutune ya ce Ya Ma’aikin Allah, iyayena su nada yawan shekaru kuma sun ce ina fidda mudu kewa don haka suke kiyayya da fita ta, sai ma’aikin Allah ya ce ka zauna tare da ma’aifanka, na ransa da wanda raina ke hanunsa debe masu kewa na yini da dare guda ya fi alheri ga yin jihadi na Sunna).har ila yau masu saurare, biyayya ga iyaye na daga cikin ababen da suke sanya wa samun soyayyar ma’aikin Allah(s.a.w) da kuma karamcinsa, a cikin littafin Kafi, an ruwaito hadisi daga Amar bn Hayan ya ce na baiwa babban abdallah imam sadik (a.s) kan irin biyayyar da Dana Isma’il yake min sai Imam (a.s) ya ce:(hakika na kasance ina son shi kuma wannan labari da ka bani ya kara soyayyar da nike masa, wata rana ‘yan uwar ma’aikin Allah (s.a.w) ta shayarwa wato wacce suka sha nono guda ta zo wajen sa, lokacin da ya ganta ya ji dadi yana mulmushi har ya sanya ta farin ciki, ya buda shunfudar da yake zaune a kanta ya zauta da ita, sannan ya juya gurin da take zaune yana tayi mata zance har ta yi dariya har lokaci da ta tashi da tafi, amma lokaci da dan uwanta ya zo bai yi masa kamar yadda ya yi mata, sai aka tambaye sa kan dalilin da yayi wa ‘yaruwarsa amma bai yiwa dan uwansa na shayarwa ba, sai Ma’aikin Allah (s.a.w) ya ce domin ta fi shi yin biyayya ga ma’aifansu), masu saurare da wannan hadisi muka kawo karshen shin na yau wassala alekum ……..