Mar 04, 2016 16:48 UTC
  • zababun Aiyuka-Kyautatawa Iyaye

shirin da ya gabata mun yi bayyani kan mahimancin yiwa iyaye biyyaya, shirin na yau zai dora daga inda muka tsaya


Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,a shirin da ya gabata mun yi bayyani kan mahimancin yiwa iyaye biyyaya, shirin na yau zai dora daga inda muka tsaya, amma kafin nan ga wannan.


******************Musuc******************************


Masu saurare, yin biyayya da kuma girmama iyaye da ma'aifa na daga cikin kyawawen dabi'un musulinci da Ubangijinmu mai Rahama ya yi umarni da shi a cikin ayoyi da dama na Alkur'ani mai tsarki, sannan kuma ya sanya shi hanyar samun rabauta da gafarsa gami da yardarsa. A cikin suratu Isra'I Aya ta 23 zuwa ta 25 Allah madaukakin sarki ya ce: (Ubangijinka kuwa ya hukunta cewa kada ku bauta wa (wani) sai shi, da kuma kyautatawa ga iyaye,ko dai ya zamana dayansu ne ya manyanta tare da kai, ko kuma dukkaninsu,to kada ku ce musu tir, kada kuma ka daka  musu tsawa , ka yi musu Magana ta tausayawa* ka kuma kaskantar da kai gare su don kyautatawa, ka kuma ce Ubangiji ka ji kansu kamar yadda suka raine ni ina dan karami*Ubangijinku ne mafi sanin abin da yake zukatanku, idan kuka zamanto managarta to hakika Shi ya tabbata Mai gafara ne ga masu biyayya gare shi),  shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) ya bayyana ma'anar kyautatawa Iyaye a cikin hadisin da aka ruwaito cikin Littafin Kafi na sheikh Kulaini yayin da daya daga cikin sahabansa ya tambaye shi ma'anar fadar Allah madaukakin Sarki (da kuma kyautatawa ga iyaye)sai Imam (a.s) ya amsa da cewa ka kyautata zama da su ka zamanto mai yi musu biyayya a ko wani hali matukar dai ba sabon Allah madaukakin sarki ba ne, kada kuma ka tilasta musu har ta kai sun tambayeka wani abu ko da ya kasance sun wadata da abinda ya rataya a kanta na kayi musu, shin ba kaji fadar Allah madaukakin sarki ba (Ba za ku sami Aljanna ba har abada sai kun ciyar da abin da kuke so)suratu Ali-Imrana Aya ta 92.abin da Imam (a.s) yake nufin da hakan kuwa shi ne mutune ya kaskantar da kansa wajen bayarwa ko kuma wadatar da ma'aifansa da duk wani abu na alheri a gare su, ko da kuwa sun kasance mawadata ne, sai Imam (a.s) ya ci gaba da cewa ma'anar fadar Allah madaukakin sarki (ko dai ya zamana dayansu ne ya manyanta tare da kai, ko kuma dukkaninsu,to kada ku ce musu tir, kada kuma ka daka  musu tsawa ) ko da sun gajiyar da kai ko wahalar da kai, kada ka ce da su tir, kuma kada ka daka musu tsawa idan sun bukeka ko kuma sun dokeka (ka yi musu Magana ta tausayawa) idan suka bukeka ka ce da su Allah ya gafarta muku, wannan shine  tattausar Magana daga gareka,sai Imam (a.s) ya ci gaba da cewa ma'anar fadar Allah madaukakin sarki (ka kuma kaskantar da kai gare su don kyautatawa) kada  ka yi musu dibar da bai da ce ba matukar ba na tausayi da girmamawa ba ne,kada kuma ka daga muryarka a kan maganarsu, ko kuma hanunka a kan su, kada kuma ka gabace su ko kuma ka shiga gabansu idan kuna tafiya).Allama Tabrasi cikin tafsirinsa mai suna majma'ul bayyan  kalkashin tafsirin wannan Aya ya ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Ridha (a.s) ya ce:(mafi karancin laifin sabawa ma'aifa shine yi masu tsaki ko kuma ce musu tir,da kuma Allah madaukakin sarki ya san a kwai wata kalama da ta fi wannan sauki da ya yi hani da ita) har ila yau a cikin wani hadisi na daban da Sikatu Islam Kulaini ya ruwaito cikin Littafinsa Alkafi, shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya bayyana mana misdakin yin biyyaya da kuma girmama iyaye ya ce:(babu wani shamaki ga mutune wajen kyautatawa  ma'aifansa, suna raye ku kuma suna mace, ya yi sallar nafilar da niyar Allah madaukakin sarki ya kan ladan garesu, ko kuma ya bayar da sadaka a maimakonsu,, yayi aikin hajji a maimakon su, ko kuma yayi azumi da niyar Ladan ya isa garesu, duk wanda yake aikata aiki na Alheri ga iyayensa, zai samu ladan makamancinsa kuma madaukakin sarki zai kara masa alheri mai yawa saboda biyayyasa ga ma'aifansa). Kamar yadda hadisai da dama ke kodayar da mu da dabi'antuwa da wannan kyakyawar dabi'a mai girma na girmama iyaye ko da kuwa sun kasance ba mumunai ba ne, hakika cikin littafin kafi an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Aliyu bn Musa Arridha (a.s) yayin da daya daga cikin sahabansa ya tambaye shi, shin muna iya yiwa ma'aifanmu Addu'a ko da kuma ba su fahimci gaskiya ba, sai Imam (a.s) ya amsa masa da cewa:( ka yi musu Addu'a, ka kuma yi musu sadaka, idan kuma sun kasance suna raye kayi musu biyayya ka yi kyakkyauwar mu'amala tare da su, domin ma'aikin Allah madaukakin sarki ya ce: hakika Allah ya tayar da ni domin rahama da tausayi ba don kuma sabawa ba).


***************Musuc********************


Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, a cikin suratu Lukma Aya ta 14 da kuma ta 15, Allah madaukakin sarki ya ce:(kuma mun yi mutum wasiyya game da iyayensa:ma'aifiyarsa ta dauki cikinsa rauni a kan rauni, yaye shi kuwa a cikin shekaru biyu ne, saboda haka ka gode min da kuma iyayenka, makoma gare ne take*idan kuwa suka matsa maka kan kayi tarayya da Ni game da abin da b aka da hakikarsa, to kada ka bi su, kuma ka yi zaman duniya da su cikin kyakkyauwar mu'amala,ka kuma bi hanyar wanda ya kama zuwa gare Ni da biyayya.sannan kuma zuwa gare NI ne kawai makomarku, sai in ba ku labarin abin da kuka kasance kuna aikatawa)


Wadannan Ayoyi masu albarka na ishara kan mahimancin godewa ma'aifa ko kuma iyaye, gode musu daidai yake da godewa Allah madaukakin sarki, wajibi ne ga ko wani mumuni ya godewa iyayeyansa ta ko wani hali, kuma ya yi kyakkyawar mu'amala da su da kuma kyautata musu, ko da kuwa ya ki yay i musu biyayya a lokacin da suka bukace shi ya bauta wa wanin Allah, ko kuma ya hada bautar Allah da waninsa . A cikin Littafin Kafi an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) yayin da wani mutune ya tambaye shi kan mu'amala da ya kamata ya yi tare da ma'aifansa alhari akidarsu ta yi babban da juna, sai Imam (a.s) ya ce (kayi musu biyayya kuma ka kyautata musu, ka yi mu'amala da su kamar yadda kake mu'amala da sauren musulmai).


Masu saurare, wannan umarnin ubangiji ne da bai kamata wani ya saba shi ba ta ko wani hali kamar yadda za mu fahimta a hadisin da aka ruwaito  cikin Littafin Alkhisal daga shugabanmu Imam Bakir (a.s) ya ce :(ababe guda uku da Allah madaukakin sarki bai amince ga kowa ba yayi sako sako da su, na farko, rikon amana ta mumuni ne ko fajiri, cika alkawari ga mumuni ko fajiri, sai kuma biyayya da kuma girmama ma'aifa mumunai ne ko kuma fajirai ne). rashin iltizami da giramma iyaye ko da kuwa Azzalumai ne ya kan yin sanadiyar kin karbar sallar mai wannan hali, kamar yadda shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya bayyana mana cikin riwayar da aka ruwaito a Littafin Kafi, Imam (a.s) ya ce:(duk wanda ya kalli ma'aifansa kallon gaskanci don suna Azzalimai allah ba zai karbi Sallar sa ba)


Masu saurare, hakika hadisaida dama sun yi jan hankali sosai na dabi’antuwa da kyawawen dabi’un girmama iyaye musaman ma a lokacin da suka manyanta suka kuma yi rauni kamar yadda Alkur’ani mai tsarki yayi ishara da hakan, wannan dabi’a na daga cikin hanyoyin dake sanya bawa ya rabauta da gidan Aljanna kuma ya cira daga shiga wuta,a cikin littafin Kafi an ruwaito hadisi daga Ibrahim bn Shu’aib ya ce na cewa babban Abdallah Imam Sadik (a.s) hakika ma’aifina ya girmanta, jikinsa yayi rauni har ta  kai ba ya iya komai sai dai mu mun masa, idan yanada wata Haja sai mun dauke sa mu kai sa, sai Imam (a.s) ya ce kadda ka kajiya, ka bashi abinci da hanunka, idan ma har yanada bukatar da ta fi haka, ka yi masa , domin Aljanna ta wajabta a gareka ranar gobe).


masu saurare ganin lokacin da ake debawa shirin ya karo jiki, a nan za mu ja birki sai kuma a maku na gaba da yardar Allah  za a jimu da ci gaba da shirin, kafin nan nake cewa a huta Lafiya, wassalama alekum warahamtullahi ta’ala wa barkatuhu.