zababun Aiyuka-girmama iyaye 3
a shiryen shiryen da ya gabata mun yi bayyani kan mahimancin girmama iyaye , domin mahimancin wannan maudi'I za mu ci gaba daga inda muka tsaya
Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,a shiryen shiryen da ya gabata mun yi bayyani kan mahimancin girmama iyaye , domin mahimancin wannan maudi'I za mu ci gaba daga inda muka tsaya,kafin nan bari mu saurari tanadin da aka yi mana a kan faifai.
******************Musuc******************************
Masu saurare, za mu bude shirin na yau da riwayar Sikatu Islam Kulaini (Y T) a cikin Littafin Kafi daga salihin Bawan nan Zakariya bn Ibrahim (Y.T) ya ce:(na kasance bisa addinin Nasara, sai na musulinta na kuma yi aikin Hajji, na shiga wajen Abi Abdullah Imam Sadik (a.s) sai na ce masa na kasance bisa Addinin Nasara, amma a yanzu na musulinta , sai Imam Sadik (a.s) ya ce da ni minene ya sanyaka ka musulinta? Sai n ace masa fadar Allah madaukakin sarki (kuma kamar haka Muka yiwo maka wahayin(Alkur'ani) daga Umarninmu, ba ka zamanto ka san mene ne Alkur'ani ko kuma Imani ba,sai dai kuma Mun sanya shi haske ne haske ne da muke shiryer da wanda Muke so daga bayinmu da shi. Hakika kuma kai lallai kana shiryarwa zuwa ga tafarki madaidaici) suratu Shura Aya ta 52sai Imam (a.s) ya ce hakika Allah ya shiriyar da kai,Allah kuma ya kara shiryar da kai har so uku, bayan haka sai ya ce da ni ka tambayi abinda ka ke so ya kai dana ,Zakariya bn Ibrahim ya ce Ya Imam hakika ma'aifina da ma'aifiyata suna kan addinin nasara, har ma da iyalena, kuma ma'aifiyata tana da rashin lafiya na rashin gani, shin na iya kasancewa tare da su, har ma inci abinci cikin kwanonku?sai Imam (a.s) ya tambayeni shin suna cin naman Alade?sai na ce masa A'a hasali ma ko tabashi basa yi.sai Imam (a.s) ya ce babu laifi, ka kasance tare da ma'aifiyarka kuma ka yi mata biyayya ka kuma giramata sosai ka dauke mata dukkanin dawainiyarta , idan kuma ta rasu kada ka bar waninka da al'amuranta, ka kasance kai da kanka ne za ka jibinci Al'amuranta. Masu saurare salihin Bawan nan Zakariya bn Ibrahim ya yi riko da wasiyar shugabanmu Imam Sadik (a.s) yayi wa ma'aifiyarsa da take fama da cutar makabta hidma, kuma hakan ya kasance sanadiyar shiriyarta.a cikamakin wannan riwaya , Zakariya bn Ibrahim ya ce a yayin da na koma Kufa, sai nake yiwa ma'aifiyarta hidma cikin tausayi da girmamawa, in bata abinci da hanu na, in wanke maka kayanta, in yi mata wanka da hanuna,sai ta ce ya dana!ba ka kasance kana yi mini hidma da kuma daukan nayauniya ta da a bay aba ka min irinta ba yayin da kake Addininmu (wato kirista) abinda nake gani kare ka tun bayan da ka shiga Addinin musulnci ya sabawa abinda kake min lokacin da kake Addinin mu wato na kirista. Sai na ce da ya ma'aifiyata,wani mutune ne daga cikin iyalan Annabinmu ya Umarce da ni da nayi maki hakan.sai ta ce wannan mutune Annabi ne? sai nace mata a'a amma shi Dan Annabi ne. sai ta ce ya Dana wannan Annabi ne, domin wannan na daga wasiyar Annabawa. Sai na ce mata ya ma'aifiyata babu wani Annaabi da zai kasance ko kuma za a tayar bayan Annabinmu, shi wanda ya umarce ni da wannan Dan Annabi ne.sai ta ce Ya kai Dana Hakika Addinka wato Addinin musulinci shine mafi alheri daga cikin Addinai ka koyar da Ni, sai na koyar da ita , ita ma kuma ta musulinta,, na koya mata Salla, ta yi sallar Azzahr, La'asar, Magriba da kuma Isha'I,sai Mala'ikan mutuwa ya ziyarce ta a wannan Dare, ta kira ni ta ce ya kai Dana ka sake fada minin abinda ka koyar da ni ayayin da zan karbi addinin musulinci, sai na fada mata ta sake maimaitawa, sannan ta mutu, lokacin da safiya ta yi, musulmi ne suka yi mata sutura, kuma ni da kaina na yi mata salla kuma na sanya ta a kabarinta. A cikin Littafin Khisal , shekh Saduk ya ruwaito wani hadisi daga shugabanmu Imam Ridha (a.s) ya ce:(hakika Allah madaukakin sarki ya yi umarni da ababe uku da kuma ba sa tabbatuwa sai da ababe uku na daban, yayi umarni da salla da kuma zakka, duk wanda ya tsaida salla ya kuma hana zakka ba a karbar sallarsa, ya yi umarni da a gode masa da kuma ma'aifa, duk wanda ya ki godewa ma'aifansa wato yaki ya yi musu biyayya , bai godewa Allah ba, sannan kuma ya yi Umarni da tsoronsa da kuma sada zumunci, duk wanda ya ki sada zumunci, ba ya tsoron Allah madaukakin sarki).
*******************Musuc**************************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa,daga cikin girmar albarkar da mai yiwa iyayen biyayya sau da kafa zai samu, kusanci da Ubangiji, kamar yadda shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya shiryar da mu cikin riwayar da shekh Saduk ya ruwaito cikin Littafinsa Amaly,Imam (a.s) ya ce:(yayin da Annabi Musa Dan Imrana yana munajati da Ubangijinsa madaukakin sarki sai ya ga wani Mutune kalkashin Al'arshin Allah, sai ya ce ya Ubangiji wanene wannan da aka ajiye shi a kalkashin Al'arshinka? Sai tabarka wa ta'ala ya ce wannan ya kasance mai biyayya ga ma'aifansa ) har ila yau daga cikin albarkatun da mi yiwa iyaye biyayya ke cimmawa, cira daga talauci a Duniya da kuma magagin mutuwa, a cikin Littafin Amaly na shekh Tusy an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:(duk wanda yake so Allah madaukakin sarki ya saukaka masa magagin mutuwa ko kuma ya mutu cikin sauki ba tare da ya sha wahala ba, to ya kasance mai sada zumunci da kuma yiwa iyayensa biyayya, idan ya kasance hakan , za a saukaka masa magagin mutuwa kuma talauci ba zai same shi ba a rayuwarsa har abada), har ila yau daga cikin tabbacin sakamako na cira daga talauci har abada a Duniya daga wadanda suke yiwa iyayensa biyayya,riwayar da shekh Saduk ya ruwaito cikin littafin Uyunul Akhbaru ridha (a.s), cikin hadisi mai tsaho da yake bayyani kan kisar Sanuwa da Allah madaukakin sarki ya umarci Bani Isra'ila su yankata, an anbato cewa a karshen lamarin bayan tambayoyi ga Annabi Musa (a.s) an umarci bani Isra'ila da su saye sanuwar da ake nufi a kimar daidai yaunin sanuwar da Zinari wacce aka saya a hanun wani matashi daga Bani Isra'ila da Allah madaukakin sarki ya wadata shi da wannan dunbun arziki albarkacin biyayyasa ga ma'aifinsa. Yayin da ya kulla wata yarjejjeniya mai riba,a lokacin da ya je daukan wani sashen abinda yake bukata domin wannan mu'amala ta tabbata, sai ya tarar da ma'aifinsa yana kwana kuma abin na kalkashin filo na ma'aifinsa, ganin ma'aifinsa na kwana,sai ya dangana da wannan riba, ya ki tayar da ma'aifinsa, bayan da ya tashi kuma ya fahimci abinda ya yi sai ya bashi wannan Sanuwa da babu irinta a yankin bakin baya.a yayin da Annabi Musa (a.s) ya fahimci hakan sai ya cewa Sahabansa :(ku diba sakamakon biyayya ga iyaye inda ya kai ahlinsa).
Masu saurare, har ila yau daga cikin kisar da ta gabata,za mu fahimnci mahimanci da kuma sakamakon yin biyayya ga iyaye wanda kuma shine rabauta da taimakon Allah na musaman , wannan kuma shine abinda shugabanmu , kuma shugaban shiriya Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya shiryar da mu, cikin riwayar da aka ruwaito cikin Littafin Alkhisal ya ce:(ababe guda hudu, duk wanda ya kasance a cikinsu, Allah madaukakin sarki zai sanya shi a rahamarsa kuma ya sanya shi cikin Aljanna, na farko, kyawawen dabi'u da zai rayu cikin mutane, tausayi ga wadanda suke cikin tsanani, girmama ma'aifa da kuma yi musu biyayya, kyautatawa ga wadanda ake milka,ma'ana masu milki ko kuma iyayen gida su tausayawa wadanda suke milka ko kuma wadanda suke aiki a kalkashinsu) masu saurare, kamar yadda girmama iyaye na daga cikin hanyoyin da suke kai mumuni zuwa mafi kololuwar martaba na rabauta da gidan Aljanna, Shekh Tusy cikin Littafinsa Amaly ya ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Bakir (a.s)ya ce:(ababe guda duk wanda ya kasance daga cikin mumunai a cikinsa Allah madaukakin sarki zai sanya shi a mafi kololuwar martaba , a gurin da yafi ko wannan matsayi da karama, da farko duk wanda ya shayar da marayya ,ya kasance masa Uba,na biyu duk wanda ya tausayawa mai rauni ya kuma taimake shi ya kuma wadatar da shi, na uku duk wanda ya ciyar da iyayensa, ya tausaya musu, ya kuma yin masu biyayya cikin girmamawa ba tare da ya bata masu rai ba,na hudu, wanda bai wahalar da Mutuman da ke kalkashinsa ba, Bawa ne ko mai yi masa Hidima ne, sannan kuma ya taimaka sa a aikin da ya sanya shi, ba tare da kuma sanya shi a aikin da zai wahalar da shi sosai ba).
******************************Musuc***************************
Masu saurare ganin lokacin da ake debawa shirin ya karo jiki, a nan za mu ja birki sai kuma a maku na gaba da yardar Allah za a jimu da ci gaba da shirin, kafin nan nake cewa a huta Lafiya, wassalama alekum warahamtullahi ta’ala wa barkatuhu.