Mar 26, 2017 03:47 UTC

Shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,

Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, Shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, A Shirye-shiryen da da ya gabata mun yi bayyani kan dabi'ar gaggauta tuba ga Allah madaukakin sarki, domin mahimancin wannan maudi'I shirin na Yau ma zai ci da wannan dabi'a , amma kafin shiga cikin Shirin ga Wannan.

**********************Musuc************************

Masu saurare, Nasossi da dama sun shiryar da mu kan cewa dabi'ar dawwama a kan Istigfari na daga cikin hanyoyin da Allah madaukakin sarki ya Ni'imta bayinsa da su domin kariya daga Azaba kamar yadda ya bayyana wa Annabin mai girma tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka cewa Lallai shi mai gafara mai jin kai ne, a cikin Suratu Anfal Aya ta 33, Allah madaukakin sarki ya ce:(Allah kuwa bai zamanto mai yi musu azaba ba alhali kai kana cikin su, kuma Allah ba za ya yi musu azaba ba alhali suna neman gafara) Hakika cikin Tafsiru Kanzul Daka'ik an ruwaito Hadisi daga Shugabanmu Imam Muhamad Bakir (a.s) ya ce:(Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa da kuma Istigfari sun kasance garkuwa biyu daga Azaba a gare ku. Mafi girman garkuwar a gare ku ya fice sai ya yi saura Istigfari watau neman tuba, domin ku yawaita yin Istigfari domin shi mai shafe Zunubai ne sannan sai ya karanto wannan Aya mai albarka ta cikin suratu Anfal wacce ta gabata). Masu saurare, kamar yadda aka ruwaito cikin Tafsiru Kanzul Daka'ik da sauransu, an ruwaito Hadisi daga Shugabanmu Amiru Mumunin Aliyu bn Abi Talib (a.s) da yake bayyani kan yawaita Istigfari ko kuma neman tuba a matsayin wani taufiki da kuma samun rabo na Ubangiji wanda yake samar da amana ga mai yin istigfarin.Imam (a.s) ya ce:(Ya kasance a doron kasa, aminci biyu daga cikin amincin Allah subhanahu wa ta'ala, kuma Hakika a dauke daya daga cikin su sai aka barku da guda to ku rike shi, amincin guda da aka dauke shi shi ne Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka, amma kun ga amincin da ya yi saura gare ku, shi ne Istigfari, watau nemam tuba Allah madaukakin sarki yace:( Allah kuwa bai zamanto mai yi musu azaba ba alhali kai kana cikin su, kuma Allah ba za ya yi musu azaba ba alhali suna neman gafara), kamar yadda Shugaban masu shiryarwa,zababban Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya shiryar mu kan cewa dabi'antuwa da dabi'ar dawwama a kan Istigfari na daga kyawawan aiyuka da Ibada, Hakika cikin Littafin Raudatul-Muttakin an ruwaito Hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da amnicin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(Istigfari watau neman gafara da fadar لاإله إلا الله watau babu wani abin bautawa da gaskiya sai Allah su ne mafi alkherin Ibada sannan sai ya karanto wannan Aya mai albarka(sannan ka sani Hakika cewa babu wani abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ka nemi gafara game da zunubanka da kuma ga mumunai maza da kuma mumunai mata, Allah kuma ya san makomarku da kuma matabbatarku) suratu Muhammadu Aya ta 19.

********************Musuc**********************************

Masu Saurare barkanmu da sake saduwa kuma kadda a sha'afa shirin na zababbun aiyuka na zo muku ne kai tsaye daga sashen Hausa na muryar Jumhoriyar musulinci ta Iran dake nan birnin Tehran, ci gaban shirin zai kawo muku wasu herin Nassosi da suke bayyani kan kyakkyawar dabi'ar dawwama a neman gafara da Istigfari,a cikin Littafin Uyunul Akhbar, an ruwaito Hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(duk wanda Allah madaukakin sarki ya ni'imce she da wata Ni'ima to ya yi godiya ga Allah, duk kuma wanda arzikinsa ke zuwa kadan kadan to ya yawaita Istigfari watau neman gafarar Allah, duk kuma wanda wani lamari ya sanya shi bakin ciki, to ya yawaita fadar لا حول ولا قوة الا بالله watau babu wata dabara ko wani ƙarfi fãce daga Allah).masu saurare, wannan hadisi mai albarka yayi ishara kan alakar dake tsakanin dabi'ar godiyar Allah madaukakin sarki dake a matsayin mafi girman dabi'ar 'yantattu da kuma dabi'ar neman gafara , kuma yin hakan  na a matsayin girman wannan kyakkyawar dabi'a, Hakika dawwama kan dabi'ar neman gafara ko Istigfari yak an yi sanadiyar saukar da arzikin Ubangiji na zahiri da badini, kamar yadda aka bayyana cewa dabi'ar godiya tana yin sanadiyar Karin arzuki, a cikin Littafin Guraru Hikam an ruwaito Hadisi daga Shugaban Musu kadaita Allah Imam Ali (a.s) ya ce:(Istigfari ko Neman gafara yana kara arzuki). Masu Saurare Hakika Shugabanmu Iman Ja'afaru Sadik (a.s) ya bayyana mana cewa Shaidan da mabiyansa na wasiwasi na daga cikin mahiman batutuwan da suke katange Mutum daga dabi'antuwa da wannan kyakkyawar dabi'a mai albarka. Hakika cikin Littafin Amalil-Saduk an ruwaito Hadisi daga Shugabanmu Imam Sadik (a.s)ya ce a yayi da wannan Aya mai albarka ta sauka:( Da kuma wadanda suke aikatamummunan aiki ko suka cuci kansu, sukan tuna Allah, sannan su nemi gafara game da laifukansu, ba kuwa mai gafarta laifuka sai Allah, ba kuma za su ci gaba bisa abin da suka aikata ba, alhali suna sane) suratu Ali Imrana Aya ta 135.Iblisu sai yau wani Dutsu a birnin Makka ana ce masa Dutsun Saur, sai ya yi kara da babbar muryarsa na kiran Rundunarsa, sai suka taru a gare shi sai ya ce: an saukar da wannan Aya wane ne daga cikin zai nauki nauyinta? Sai Ifritu daga cikin Shaidanai ya ta shi sannan ya ce: ni zan dauke ta ta kaza da kaza,watau ya bayyana irin salon sa da kuma hanyoyin da zai bi na toshe hanyar Allah, sai Iblis ya ce b aka dace da wannan ba, sai wani daga shaidanai shima ya ta shi ya bayyana irin nasa makirinci da zai bi wajen tushe hanyar ta Ubangiji, shi ma Iblis yace masa kaima ba ka dace da wannan Aya ba, sai waswasil-khanas watau shaidan mai wasi-wasi mai buya mai zabura ya tashi ya cewa Ni da ita, sai Iblis ya tambaye shi zai yaudare su in kuma kwadaita su har sai sun fada cikin Sabo, idan kuma suka aikata Sabo sai in mantar da su Istigfari watau neman gafara, sai Shaidan ya ce masa Hakika kai ka da ce da ita, an wakilta maka ita har zuwa ranar Alkiyama) da fatan masu saurare, Allah ta'ala ya kiyaye musu daga Sharin Shaidan da Rundunarsa ya kuma bamu damar neman gafara da Istigfari cikin ko wani hali da yanayi dan albarkar riko da tafarkin Annabi Muhamadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da kuma na iyalan gidansa tsarkaka.

**********************Musuc***************************

Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.