zababun Aiyuka-girmama iyaye 4
a shiryen shiryen da ya gabata mun yi bayyani kan mahimancin girmama iyaye , domin mahimancin wannan maudi'I za mu ci gaba daga inda muka tsaya
Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,a shiryen shiryen da ya gabata mun yi bayyani kan mahimancin girmama iyaye , domin mahimancin wannan maudi'I za mu ci gaba daga inda muka tsaya,kafin nan bari mu saurari tanadin da aka yi mana a kan faifai.
******************Musuc******************************
Masu saurare, hakika Allah madaukakin sarki ya ja hankali bayinsa da su kula sosai wajen girmama iyaye wanda hakan shi zai sanya a samu kyakyawar makoma a cikin suratu Ahkabi, Aya ta 15 da ta 16 Allah madaukakin sarki ya ce :(kuma mu yi wa mutum wasiya da kyautatawa uwarsa ta dauke (a shi) a wahalce.Daukan cikinsa da yaye shi wata talatin,sai lokacin da ya cika karfinsa ya kai shekara arba'in ya ce, 'Ya Ubangijina ka kisma min yadda zan gode wa ni'imarka wadda ka ni'imtata a gareni da kuma ga ma'aifana, kuma ka (kisma min) yadda zan yi aiki kyakkyawa wanda za yarda da shi,kuma ka kyautata min cikin zuriya ta,hakika ni na tuba gare ka kuma hakika ni ina daga musulmi* wadancan (su ne) wadanda Muka karbar musu mafi kyaun abin da suke aikatawa daga gare su Muka kuma yafe munanan ayyukansu cikin bin komai sai abin da ake yiwo min wahayi, kuma ba wani abu ba ne ni face mai gargadi mabayyani), hakika hadisai da dama sun yi ta'akidi na girmama ma'aifiya, giramamawa da fiyayya ta musaman,a cikin Littafin Kafi an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:(wani mutune ya zo wajen Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka sai ya ce ya ma'aikin Allah wanene ya dace in fi yi masa fiyayya da girmamawa? Sai Ma'aikin Allah ya ce ma'aifiyarka, sai mutumam y ace sannan kuma hwa: sai ya ce ma'aifiyarka, har so uku , a karo na hudu ma'aikin Allah ya ce ma'aifinka), kamar hadisi na daban dake bayyana mana biyayya ga ma'aifiya ya fi tasiri sosai wajen kafirta zunubai da kuma samun rabauta gafarar Ubangiji, hakika Shekhin malamin nan da ya shahara wajen zuhudu wato tsantsaini da daudar Duniya Husain bn Saeed Ahwazi, cikin Littafinsa mai suna kitabu Zuhdu ya ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Zainul abidin ya ce wani mutune ya je wajen Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce Ya Ma'aikin Allah babu wani nau'in zunubi da ban yisa ba a nan Duniya, shin a kwai wata hanya ta tuba? Sai Ma'aikin Allah (s.a.w) ya ce shin daga cikin ma'aifanka a kwai wanda yake raye? Sai wannan mutum ya ce eh ma'aifina yana raye sai ma'aikin Allah ya ce to ka je wajensa ka kanji, Imam zainul Abidin (a.s) ya ce bayan wannan mutuman ya tafi sai ma'aikin Allah ya ce da ma ma'aifiyarsa ce, ma'ana ya na nufin da ma'aifiyarsa ce take raye da biyayarsa a gareta ta kasance mafi girman tasiri wajen karbar tubarsa).masu saurare a bangare guda,wasu hadisai sun kwadaitar da mu da dabi'antuwa da dabi'ar biyayya da kuma girmama iyaye,wajibi ga ma'aifa su taimakawa 'ya'yansu ta yadda za su tashi da tarbiya mai kyau kuma su yi musu biyayya, kuma taimakon zai kasance na kyakkyawar mu'amala tare da su, hakan zai sanya su rabauta da rahamar Allah ta musaman, a cikin Littafin Amaly shekh Saduk ya ruwaito hadisi daga ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce (Allah ya ji kan mutuman da ya taimakin ma'aifinsa a kan biyayya ga Allah, Allah taimakin ma'aifin da ya taimakin Dansa a kan yiwa Allah biyayya,Allah taimaki makobcin da ya taimaki makobcinsa a kan biyayyarsa, Allah taimaki abokin da taimaki abokinsa a kan biyayyar Allah), a cikin da aka ruwaito cikin Littafin Khisal, shugabanmu Imam ja'afaru Sadik (a.s) ya ce:(ku yi bi ma'aifanku, 'ya'yanku sais u bi ku).
*******************Musuc*******************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai fara da kyawawen dabi'un Annabawa (a.s) domin duk wanda yake girmama iyayensa kamar yay i koyi ne da kyawawen dabi'un Annabawa da mursalai (a.s), cikin suratu Maryam Aya ta 13 da ta 14, Allah madaukakin ya ce:((Muka hore masa) tausayi daga gare Mu, da tsarkin (zuciya)ya kuma kasance mai tsoron (Allah)*kuma sai biyayya ga mahaifansa, bai kuma zamanto mai tsaurin rai mai saba wa (umarnin Allah) ba ). Har ila yau cikin wannan sura mai albarka daga Aya ta 30 zuwa ta 32, Allah madaukakin sarki ya ce:(Annabi Isa (a.s)) ya ce (da su) hakika ni bawan Allah ne, ya bani Littafi ya kuma mayar da ni Annabi.*Ya kuma sanya ni mai albarka a duk inda nake,kuma ya umarce ni da yin sallah da kuma bada zakka, matukar ina da rai*kuma mai biyayya ga ma'aifiyata, bai kuma sanya ni mai girman-kai mai sabo ba). abin fahimta ga wadannan Ayoyi masu albarka ,dabi'antuwa da dabi'ar girmama iyaye na daga cikin alamomin tsoron Allah,da kuma tsarkaka daga mumunar dabi'ar girman kai, sabo da shakiyanci ,da fatan Allah madaukakin sarki ya tsare mu da su gaba daya.masu saurare, idan wannan ya bayyana a garemu za su fahinci cewa sabawa iyaye na daga cikin alamomin girman kai, da shakiyanci domin haka ne nassosi da dama suka yi hani da shi, domin a kasance rahama ga mutane da kuma garkuwa daga cutuwa.a wani hadisi na daban an bayyana cewa wanda yake kin girmama ma'aifansa zai hadu da sakamakonsa a nan duniya tun kafin ya je Lahira,a cikin Littafin Amaly na shekh saduk, an ruwaito hadisi daga ma'aikin Allah (s.a.w) ya ce:(uku daga cikin zunubai, ana gaggauta ganin munanan sakamakonsu tun a nan duniya, ba a sai ta kai ga Lahira ba, , sãɓã wa iyayensu, zalintar mutane da kafircewa kyautatawa )ma'ana mayar da kyautatawa da mumuna.a cikin Littafin Ilalu Sara'I'I an ruwaito wani hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:(saba wa iyaye na daga cikin manya manyan zunubai).
Har ila yau a cikin Littafin Ilalu Shara'I'I, an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Aliyu bn Musa Aridha (a.s) ya ce:(Allah ya haramta sabawa iyaye, domin saba masu yana yin sanadiyar fita daga samun taufiki na yin da'a ga Ubangiji madaukakin sarki, girmama iyaye, kaucewa kafircewar ni'ima da kuma kin godiya,) da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu ikon girmama iyayenmu da yi musu biyyaya domin samun taufiki a duniya da Lahira.
******************Musuc************************
masu saurare ganin lokacin da ake debawa shirin ya karo jiki, a nan za mu ja birki sai kuma a maku na gaba da yardar Allah za a jimu da ci gaba da shirin, kafin nan nake cewa a huta Lafiya, wassalama alekum warahamtullahi ta’ala wa barkatuhu.