Dabi'ar Yiwa Kai Hisabi 2
Shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,
Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,Shirin na Yau zai yi bayyani kan daya daga cikin mafi kauna na kyawawen dabi'u a wajen iyalan gidan Anabta tsarkaka, watau dabi'ar Yiwa kai hisabi a ko wata Rana, kamar yadda muka yi muku alkawari a shirin da ya gabata mun kebe shirye shirye da dama domin bayyani kan wannan Maudi'I saboda mahimancin sa, amma kafin shiga cikin Shirin sai a daka ce mu da wannan.
******************************Musuc**************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, Shirin na Yau zai fara da wani Hadisi da aka ruwaito daga Shugaban Halittu Masoyi kuma zababben Allah mai shiryarwa amincin Allah ya tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka, inda a cikin sa ya shiryar da mu kan cewa dabi'antuwa da dabi'ar yiwa kai hisabi na daga cikin mafi mahimancin hanyoyi na rabauta da jin dadi na hakika a Duniya da Lahira, Hakika cikin Littafin Risalatu Muhasibatu-Nafs na Shekh Ibrahim Kaf'ami yardar Allah ta tabbata a gare shi, an ruwaito Hadisi daga Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya ce:(ku kayyade kawunanku wajen yi musu Hisabi, ku kuma mallake su ta hanyar saba musu, sai ku amintu a wajen Allah daga fargaba gami da tsaro sannan ku cimma sauki na kyakkyawan fata daga gare shi,Hakika madaurin kayyade rai shi ne yi masa Hisabi, kuma ana mallakarsa ne ta hanyar yin galaba a gare sa, mafi rabo cikin Mutane wanda ya gaggauta yiwa kansa Hisabi kuma ya nema masa hakinsa Safiya da marece). Hakika Masu saurare dabi'antuwa da wannan dabi'a mai girma na a matsayin cimma daya daga cikin Ni'imomin ubangiji da ya lullube bayinsa Mumunai, a cikin Littafin Guraru Hikam an riwato hadisi daga Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya ce:(Duk wanda ya yiwa kansa hisabi ya rabauta, duk kuma ya yiwa kansa hisabi ya ci riba, babu mai fatan alheri face wanda ya shagaltu da kansa watau wajen yi masa hisabi da kuma bukatunta gami da yaki na nisantar sabon Allah), haka ne, kamar yadda aka ce dabi'antuwa da wannan kyakkyawar dabi'a wasila ne na cimma martabar masu tsoron Allah, Ya zo cikin Littafin Risalatu Muhasibatu-Nafs daga Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya ce:(Mutum ba zai kasance daga cikin Mumunai ba har sai ya yiwa kansa hisabi ya sani daga ina cinsa da shansa da suturarsa suke fitowa).Masu saurare, Nassosi da dama sun bayyana mana cewa, dabi'antuwa da kyakkyawar dabi'a na yiwa kai hisabi alama ce ta cikar hankali, ya zo cikin Hadsin Nabawi a littafin Risalatu Muhasibatu-Nafs fadar Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan sa tsarkaka (Mai cikekken Hankali shi ne wanda ya gaggauta yiwa kansa Hisabi saboda abinda zai riska bayan Mutuwa da bukatunta), Hakika Masu saurare, kamar yadda dabi'antuwa da wannan dabi'a mai girma hanya ce a aikace na tsira daga Makircin Nafsul Ammaratu-bissu'I, da kuma gyaran kai ta hanyar sanin aibinta, Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) cikin Littafin Guraru Hikam ya bayyana cewa:(Duk wanda ya gaggauta yiwa kansa hisabi ya amintu daga yaudara, duk wanda kuma ya yiwa kansa hisabi zai fahimci laifinsa ya kuma nemi gafara ya tuba zuwa ga Allah ya gyara kurakuransa).
**********************Musuc***************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa shirin na zababbun aiyuka na zo muku ne kai tsaye daga sashen Hausa na muryar Jumhoriyar musulinci ta Iran, Hakika Masu saurare mai shiryarwa, Zababben Allah amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya shiryar da mu cewa dabi'ar yiwa kai hisabi ita ce tushen dabi'a na biyu da ya kamata ko wani Mumuni dake neman tsira ya dabi'antu da ita, a cikin Littafin Khisal na Sheikh Saduk, an ruwaito Hadisi daga Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya ce:(ga ko wani mai hankali matukar dai bai kasance wanda aka yi galaba a kansa, ya riki wasu awo'I, daga cikin su wata Awa ya yi munajati da Ubangijinsa watau ya karanto Addu'o'I, wata Awar kuma ya yiwa kansa hisabi, wata Awar kuma yayi tunani a cikinta dangane da halintun Allah, wata Sa'ar kuma ya kebance da ita domin duba irin rabon da ya samu na halal, wannan sa'a ita take taimakon wadancan sa'o'in da suka gabata kuma ta hada zukata), Masu saurare Annabin Rahama (s.a.w.a) ya shiryar da mu cewa dabi'antuwa da dabi'ar yiwa kai hisabi shi ne tabbatar da sharudan Imani, hakika cikin Littafin wasa'il an ruwaito Hadisi daga babban Jikan Annabin Rahama watau Imam Hasan Mujtaba (a.s) ya ce:(Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce: Bawa ba zai kasance Mumuni ba har sai ya yiwa kansa hisabi mafi tsananin Hisabi daga Sharikin Sharikinsa), yiwa kai hisabi daya ne daga tushen alamar gasganta Imani da ranar Alkiyama gami da ranar Hisabi, kamar yadda Shugabanmu Imam Zainul-Abidin (a.s) ya yi ishara da hakan, Hakika ya zo cikin Littafin Sara'ir na babban malamin fikhun nan Ibn Idris yardar Allah ta tabbata a gare shi kan cewa Imam (a.s) ya ta jadadda wannan fada a cikin wa'azinsa( Ya Dan Adam hakika ba za ka kushe cikin alheri ba, matukar dai ka kasance mai yiwa kanka wa'azi, da kuma yiwa kai hisabi ka kuma bashi mahimanci,Ya Dan Adam Hakika Kai Matacecce ne kuma za ta tayar da kai, za ka kuma tsaya a gaban Allah, sai ka tanadi amsar da zaka bashi).Masu saurare kamar yadda daga cikin albarkar dake tattare da dabi'ar yiwa kai Hisabi, taimakon Mumuni na dabi'antuwa da falalar tsoron Allah kuma wannan shi ne mafi martaba na siffofin Masoyan Allah, kamar yadda ya zo cikin Littafin Misbahul-Shari'a daga Shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:(Ka rufe kofofin gabobinka daga abinda zai cutar da su zuwa zuciyarka , kuma ya zubar da mutuncinka a gaban Allah, kuma ya biyo baya da hasara gami da Nadama ranar Alkiyama da kuma kunya kan abinda ya raunata na munana, mai tsoron Allah yana bukatar tushe ko asali guda uku, yafiya daga cutarwar bayi, ya kasance yabo da fallasa a wurinsa duk daya ne watau yabon da Mutane za su yi masa ko kuma fallasa a wurinsa duk daya ne, tushen tsoron Allah dawwama a kan yiwa kai Hisabi) da fatan Allah madaukakin sarki ya arzuta mu da wannan kyakkyawar dabi'a ta yiwa kai Hisabi tare da neman gafara gami da istigfari a gare shi dan albarkar riko da wulayar iyalan gidan Anabta tsarkaka.
**********************Musuc***************************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.