Apr 09, 2017 05:17 UTC

Shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,

Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, Shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,a shirin na Yau za mu yi bayyani kan daya daga cikin hasken Shiriya na Ahlul-bait (a.s) wanda yake kira zuwa dabi'antuwa da dabi'un Masoya Allah da suke samar da dukkanin Alheri tare kuma da tsira da dukkanin sharri, daga cikin irin wadannan kyawawen dabi'u, a kwai dabi'ar yiwa kai Hisabi, kuma hakika mun kebance shirye-shirye da dama  na bayyani kansa saboda mahimancin sa. Amma kafin mu shiga cikin shirin, a dakace mu da wannan.

******************************Musuc*******************************

Masu Saurare, za su fara shirin da wasiyar Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) dake bayyani kan dabi'antuwar Mumuni da dabi'ar yiwa kai Hisabi, wanda hakan na daga cikin mahiman hanyoyin na rabauta da karamar haduwa da wadanda Allah madaukakin sarki ya yabe su cikin wannan Ayoyi masu albarka:((Hasken) yana cikin dakuna (watau masallatai) wadanda Allah ya yi umarni a daukaka a kuma ambaci sunansa a cikin su.(wasu Mazaje) suna tasbihi gare Shi a cikin su safe da yamma*(Su) mazaje ne wadanda kasuwanci da saye da sayarwa bas a shagaltar da su daga Ambaton Allah da kuma tsai da salla da ba da zakka, suna tsiron ranar da zukata da idanuwa suke raurawa*(suna haka ne) don Allah ya saka musu mafi kyan abin da suka aikata, kuma ya kara musu daga falalarsa.Allah kuwa yana arzuta wanda ya so ba da iyaka ba) suratu Nuri daga Aya ta 36 zuwa Aya ta 38.Hakika masu Saurare wadannan Ayoyi masu albarka suna yi mana ishara da cewa wadanda aka Ambato da cikin su Allah madaukakin sarki yana yi musu kyakkyawan sakamako daga abin da suka aikata kuma yana yi musu kari daga falalarsa ba tare da wani hasabi ba kuma wannan shi ne mafi martaba na arzikin Ubangiji, to ta yaya za mu rabauta da irin wannan falala? Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya amsa mana wannan tambaya a cikin wannan Nassi da aka ruwaito cikin Littafin Nahjul-Balaga, inda a cikin sa aka ce Imam (a.s) ya kasance yayin da ya karanto wannan Aya yana fadar cewa:(Majaze ne wadanda Kasuwanci da saye da sayarwa bas a shagaltar da su daga Ambaton Allah, da ka misaltaku da hankalinka cikin mikaminsu abin godewa da kuma mazauninsu da ya kasance abin shaida, Hakika sun watsa diwanin aiyukan su, sun kuma shagaltu wajen yiwa kansu Hisabi a kan ko wani aikinsu kadan ne ko kuma babba ne, wanda aka Umarce su da shi, idan suka yi sako sako wajen aikata shi, wanda kuma aka hane su da shi suka  fice iyaka kansa, sai su gaggauta zuwa ga Ubangijinsu cikin Nadama da I'itirafi) Sannan Imam (a.s) cikin bayyanin albarkar dake tattare da wadannan salihan Bayi 'yantattu masu yiwa kansu hisabi tun a nan Duniya ya ci gaba da cewa:(da za ka ga ma'abuta Shiriya da kuma hasken Duhu, Hakika Mala'iku sun kewaye su, kuma Nutsuwa ta sauka gare su, dukkanin kofofin alheri na Sama sun bude musu, kuma ai yi musu alkawarin matsayi na Karamci)sannan a karshen Kalamansa, Imam Ali (a.s) ya kira mu da mu yi koyi da wadannan 'yantattu da kuma shagaltuwar ko wane daga cikin da aibinsa ko laifinsa maimakon ya dinga kallon laifi ko aibin wani yana mai cewa:(Ka yiwa kanka hisabi saboda kanka watau saboda masalahar kanka, domin wata ran ita ma ta nada hisabin kanta ).

***********************Musuc*******************************

Masu saurare barkanmu da sake saduwa kuma kadda a sha'afa shirin na zo muku kai tsaye daga Sashen hausa na muryar Jumhoriyar musulinci ta Iran dake nan birnin Tehran,ci gaban shirin zai fara da Wasiyar Anabta wanda Shekh Saduk yardar Allah ta tabbata a gare shi ya ruwaito cikin Litattafansa Amaly da kuma Ma'anil-Akhbar daga Masoyin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka daga cikin Wasiyoyin da yayiwa babban Sahabin nan Abu Zar Algaffari yardar Allah ta tabbata a gareshi ya ce:( Ya Aba Zar ka yiwa kansa Hisabi kafin ayi maka domin shi ne mafi raunin hisabi na ranar gobe,ka auna kanka kafin a auna ka, ka shiryawa kanka cikeli mai girma kafin ranar da za a auna maka cikelinka, ranar da babu abu da zai buya a wajen Allah,Ya Aba Zar mutum ba zai kasance daga cikin masu tsoron Allah ba har sai ya zamanto mai yiwa kansa tsananin Hisabi daga hisabin abokin abikinsa, ya san daga ina Ina yake samun abincinsa, daga ina yake samun abin shan sa, daga ina yake samun sutturarsa, Shin daga Halal ne ko daga Haramun ne.Ya Aba zar Duk wanda wand aba ruwan sa ko kuma yayi burus daga inda yake samun kudunsa, Allah ba sai damu daga ina sai sanya shi wuta ba). Hakika Masu saurare wannan Nassi mai albarka ya bayyana mana cewa Dabi'antuwa da Dabi'ar yiwa kai Hisabi na daga cikin mahiman hanyoyin da suke tsirar da Mutum da kuma samun babban rabo ranar Hisabin Ubangiji a aikace, da kuma tsira da wahalhalun ranar Alkiyama kamar yadda Shugaban Masu Kadaita Allah Imam Ali (a.s) ya bayyana mana a cikin Littafin Nahjul-Balaga:(Duk wanda ya yiwa kansa Hisabi ya ci riba, duk kuma wanda ya gafala da hakan yayi hasara,duk kuma wanda ya ji tsoro ya amintu, duk kuma wanda ya dauki darasi daga abinda ya gani ko ya ji to yayi basira, duk kuma wanda yayi Basira ya fahimtu, duk kuma wanda ya fahimtu ya samu ilimi) kamar yadda Dabi'antuwa da wannan Dabi'a mai girma na daga cikin hanyoyin da suke sanyawa Allah tabaraka wa ta'ala amsar Addu'ar Bawa gami da tsira daga bala'in tashin kiyama, wannan shi ne abinda Shugaban Imam Sadik (a.s) ya shiriyar da mu a cikin ruwayar da aka ruwaito a Littafin Kafi na Sikkatu Islman Kulaini (idan dayanku yana bukatar idan ya tambayi Ubangijinsa wani abu ya bashi, to ya yanke kauna daga Mutane gaba daya, kadda ya kasance ya nada wani fata a wajen wani face a wajen Allah madaukakin sarki, idan Allah madaukakin sarki ya fahimci hakan daga cikin Zuciyarsa ba zai tambayi wani abu a gare shi ba face ya bashi, ku yi wa kanku hisabi kafin a yi muku hisabi ranar Alkiyama, domin Ranar tashiin Alkiyama a kwai Maukifi ko kuma wurin bincike hamsim ko wani wuri kuma na a matsayin zama na shekarau dubu, sannan sai ya karanto wannan Aya, Allah madaukakin sarki  ya ce:(Wadanda Mala'iku tare da Jibirilu suka hawa zuwa gare Shi a cikin wata rana (wadda) gwargwadonta yake daidai da shekara dubu hamsin) suratu Ma'ariji Aya ta 4.

Masu Saurare daga cikin mu a kwai wanda baya so ya kasance daga cikin Zuriyar Iyalan Gidan Annabin Rahama Muhamad (s.a.w.a)?Shakka babu dukkaninmu muna fatan hakan.to mu dabi'antu da dabi'ar yiwa Kai hisabi a zukatanmu, damin yin hakan na daga cikin hanyoyin samun rabauta da kasancewa tare da iyalan gidan Anabta tsarkaka kamar yadda Shugabanmu Imam Musa Kazim (a.s) yake yi mana bushara a hadisin da aka ruwaito cikin Littafin Kafi, Imam (a.s) y ace:(ba ya daga cikinmu wanda yay a yiwa kansa hisabi ko wata Rana, idan ya aikata aiki mai kyau sai Allah yay i masa kari, idan kuma ya yi sabo  ko ya aikata wani mumunan aiki, sai yayi Istigfari watau ya nemi tubar Allah madaukakin sarki a kan hakan)

*********************Musuc***************************

Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya jiki, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.