Apr 17, 2017 05:21 UTC

Shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira

Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, a Shirye da ya gabata, mun yi bayyani kan dabi'ar yiwa kai hisabi, ganin mahimancin sa shirin na Yau ma zai dora daga cikin muka dagata a shirin da ya gabata, amma kafin nan sai a daka ce mu da wannan.

***************************Musuc*****************************

Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, shirin na Yau zai fara da wasiyar Anabta wacce ke shiryar da mu zuwa misdaki na mahimancin dabi'antuwa da dabi'ar yiwa kai hisabi ta hanyar sanar da mu yadda ya kamata mu yi riko da wannan dabi'a kafin gudanar da wani aiki da muka kudiri aikatawa  ba wai bayansa ba kamar yadda ya kasance a cikin kwakwalan dayawa daga cikin mu kan fahimtar yiwa kai Hisabi. A cikin Littafin Kafi an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) ya ce:(Wani Mutum ya je wajen Ma'aikin Allah (s.a.w.a) sai Ya ce Ya Ma'aikin Allah ka yi mini wasiya, sai Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya ce shin za kayi amfanin da wasiyar idan nayi maka? Ya fada masa wannan Jumula har so uku sai Mutuman ya ce Na'am ya Ma'aikin Allah , Sai Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce Hakika ina yi maka wasici da cewa Idan  ka gudiri aikata wani  aiki to kayi tunanin karshen sa, idan ya kasance a kwai shiriya ciki, sai ka aikata, idan kuma akwai cutuwa cikinsa to sai ga hannu da aikata shi).Masu saurare, ba boyayyen abu a gare ku yadda Ma'aikin Allah tsira da amincin su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa yayi ta maimaita tambayarsa saboda mahimancin aiki da wasiya, a hakikanin gaskiya yana ishara ne kan mahimancin dabi'ar yiwa kai Hisabi domin haka ne shahararen malamin nan shekh Faidu Kashani ya yi ta'aliki bayan da ya nakalto wannan hadisi a cikin Littafin Alwafi yana mai cewa wannan wasiyar ta Anabta na daga cikin dabi'ar yiwa kai Hisabi kai ma ita ce Shugabanta. a hakikanin gaskiya aiki da wannan misdaki na yiwa kai Hisabi na daga cikin tabbacin yakar son zuciya  da kuma kiyayeta a kan shari'ar Ubangiji, da wannan ma'ana ne Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi talib (a.s) ya yi ishara a cikin hadisin da aka ruwaito a Littafin Guraru Hikam yana mai cewa:(ka yaki zuciyarka kuma kayi mata hisabi tun kafin hisabin ranar kiyama, ka kuma nema ta da hakin Ubangiji, wanda ya fi kowa rabauta daga cikin Mutane shi ne wanda ya gaggauta yiwa kansa Hisabi). Masu Saurare, abin fahimta a cikin wadannan Nassosi masu albarka shi ne dabi'antuwa da dabi'ar yiwa kai Hisabi tun kafin aikata wani aiki  da kuma bayansa hanya ce ta gyara zuciya da kuma tsiratar da ita daga duk wani sharri, Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib(a.s) kamar yadda ya zo a wurare da dama cikin Littafin Guraru Hikam ya na mai cewa:(ribar yiwa kai hisabi shi ne gyarar zuciya, ku yiwa kanku Hisabi tun kafin ayi muku, ku yi ma kan ku Hisabi da aiyukanta kuma ku bukace ta da aikata farilan da aka wajabta mata ta kuma daukan guziri a wannan gida mai gushewawato Duniya ga gidan da ba ya gushewa wato Lahira).

*****************************Musuc**************************

Masu saurare barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa shirin na zo muku ne kai tsaye daga sashen Hausa na muryar Jumhoriyar musulinci ta Iran dake nan birnin Tehran, ci gaban shirin zai fara da hadisin Anabta da Shekh Saduk yardar Allah ta tabbata gare shi ya ruwaito cikin Littafin Ma'anil-Akhbar daga Masoyinmu, shugabanmu mai shiryarwa zababben Allah amincin Allah ya tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(Ambaton Allah dare da rana ya fi alheri a kan sara da takobi ta hanyar Allah madaukakin sarki, duk wanda ya ambaci Allah dare da rana kuma ya tuna abinda ya kasance kansa cikin Dare daga mumanan aiyukansa ya kuma nemi gafara ya tuba, zai fadaka kamar an tayar da shi daga barci, duk wanda ya ambaci Allah da dare, ya kuma yi bitar abinda ya kasance a kansa na wannan Rana kamar yadda ya sarrafa rayuwarsa ta hanyar da bai dace ba, da kuma yadda ya bata lokacinsa ta hanyar kin umarnin Ubangiji, ya nemi gafara Ubangiji madaukakin sarki, ya tuba, Hakika an gafarta masa zunufinsa).Masu saurare, wasiyar Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ta bayyana cewa mabudin dabi'antuwa da dabi'ar yiwa kai hisabi shi ne da farko kodayi wajen ambaton Allah a ko wani lokaci, na biyu kuwa, aiki da wasiyar Alkur'ani mai tsarki inda ta kira ko wani Mutum ya koma zuwa ga kansa da kuma fitirarsa da kuma yin tunani kan abinda ya aikata idan mai kyau ne ya kara azama wajen ci gaba da aikata irin wannan aiki, na uku kuma shi ne gaggauta yin istigfari da neman tuba ga Allah madaukakin sarki dangane da zunubin da Bawa ya aikata domin ya tsarkaka daga zunubansa ya kuma rabauta da gafarar Allah da yardarsa.

Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi talib (a.s) ya yi tabbaci a kan kodayin Mumuni na kaiwa ga kamala a lokacin da ya kebe na yiwa kansa hisabi domin cimma ribar dake cikinta, Hakika ya zo cikin Littafin Guraru Hikam , Imam (a.s) ya ce:( babu abinda ya fi hakki ga Mutum da ya kasance yana wata Sa'a da babu wani abu da zai shagaltar da shi a cikin ta, ya yiwa kansa Hisabi, ya fahimci abinda ya samu a cikin ta, ma'ana ya fahimci abinda ya aikata cikin Dare da rana da wannan yini). Masu Saurare Hakika Shugabanmu Imam Muhamad Bakir amincin Allah ya tabbata gare shi ya yi wasici cikin Hadisin da aka ruwaito cikin Littafin Kafi na Sikatul-Islam Kulaini ga daya daga cikin sahabansa kan cewa kadda wani abu ya shagaltar da shi dangane da wannan kyakkyawar dabi'a na yiwa kai Hisabi yana mai cewa:(Ya Babban Na'aman kadda Mutane su shagaltar da kai daga kanka, domin akwai al'amarin da zai same ka koma bayan su, ma'ana shi ne mumunan sakamako na rashin yiwa kai hisabi zai riske shi, kadda ka shagaltar da kanka dare da rana da kaza da kaza ba tare da tunanin karshin al'amarinsa ba, Hakika a tare da ku, akwai wadanda suke kula da aiyukanka ma'ana wadanda  suke rubutawan ka  na alheri da na Sharri, ka kyautata, domin Ni ban ga wani aiki mafi kyau da Mutum ya kamata ya gaggauta aikata shi ba kamar istigfari da neman tuba zuwa ga Allah madaukakin sarki  na dukkanin zunubi ba) da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu ikon yiwa kawunanmu hisabi tare da yawaita Istigfari da neman Tuba Dare da Rana domin albarkar riko da Sunar Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da kuma wulayar Iyalan Gidansa tsarkaka.

**********************Musuc***************************

Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.