May 07, 2017 19:23 UTC

Shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,

Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira, a Shirye-shiryen da suka gabata, mun yi bayyani kan dabi'ar yiwa kai hisabi, kuma shakka babu daga cikin mahimam dabi'un masoya Allah, shi ne wannan dabi'a ta yiwa kai hisabi da hakan zai kai Mutum zuwa ga kamala gami da dukkanin alheri, yau ma shirin zai ci gaba da shi, amma kafin nan sai a daka ce mu da wannan.

***************************Musuc*****************************

Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, hakika amfanin Mumuni da Lokacinsa kan abinda yake maslaha a gare shi, na daga cikin mahiman haskaken dabi'antuwa da dabi'ar yiwa kai Hisabi kafin zartar da wani aiki, wannan shi ne abinda Nassosi da dama suka shiryar da mu, daga cikin su hadisin da aka ruwaito cikin Littafin Khisal daga Shugabanmu kuma Masoyinmu Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka cikin wasiyar da ya yiwa wasiyinsa Aliyu bn Abi Talib (a.s) yana mai cewa:(Ya Ali ga gaggauta amfani da Abu Hudu kafi abu hudu su cimmaka, yarintarka  kafin tsufanka, lafiyarka kafin rashin lafiyarka,wadatarka kafin talaucinka,rayukarka kafin mutuwarka).Wannan a hakikanin gaskiya masu saurare na a matsayin amsar kiran Alkur'ani mai tsarki, Allah (s.w) ya ce:(Kuma Ka nemi gidan Lahira ta hanyar abin da Allah ya ba ka, kadda kuma ka manta rabonka na Duniya, kuma ka kyautata kamar yadda Allah ya kyautata maka, kada kuma ka nemi yin barna a bayan kasa, Hakika Allah ba ya son masu barna) suratu Kasasi Aya ta 77 abinda ake nufin da hakan shi ne kadda Mutum ya gafala da neman Lahira daga abinda Allah madaukakin sarki ya bashi na jin dadi da kuma ni'imar Duniya kamar yadda yake a bayyane cikin wannan Aya da ta gabata.a cikin Littafin Ma'anil-Akhbar an ruwaito hadisi daga Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya ce:(ma'anar fadar Allah madaukakin sarki (kadda kuma ka manta rabonka na Duniya) kadda ka manta da Lafiyarka da karfinka da lokacin da ba ka komai, da Yarintarka gami da walwalarka wajen neman Lahira). Masu Saurare a wani hadisin na daban da aka ruwaito cikin Littafin Hidayatul-Umma, Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya bayyana mana hanya a aikace wajen yiwa kai wa Hisabi a yayin da yake amsa tambayar da aka yi masa na cewa: ta yaya Mutum zai yiwa kansa Hisabi?Sai ya ce: Idan ya tashi da safe sannan ya kai marece sai ya koma ga kansa ya kuma ce Ya kai raina Hakika wannan rana ta fice ba za ta dawo har abada ba, kuma Allah madaukakin sarki zai tambayeka kan abida ka yi cikin wannan yini, minene ka aikata a cikin sa, shi ka ambaci Allah ko ka gode masa? Shin ka biya bukatun mumunai a cikinsa?shin ka kiyaye shi wajen bayyanawa Iyalanka da ya'yanka Addini? shin ka rike bakinka daga cin naman Dan uwanka Mumuni?shi ka taimakawa Musulimi? Mi ka aikata a cikinsa? Sannan Imam (a.s) ya ci gaba da cewa, ya ambaci abinda ya kasance cikin sa wato yinin, idan ya tuna abinda ya yi na alheri cikin sa sai godewa Allah ya kuma girmama shi kan damar da ya basa na aikata hakan, idan kuma ya tuna sabon da ya yi cikinsa ko kuma wata kasawa wajen cikar hakin Ubangiji sai ya nemi gafarar Allah, ya kuma dauki niyar a kan barin wannan sabo da kuma sake maimaita irinsa).

******************************Musuc**************************

Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa shirin na zo muku ne kai tsaye daga sashen Hausa na muryar Jumhoriyar musulinci ta Iran dake nan birnin Tehran,A ci gaban shirin za mu fara da wata wasiya wacce take kwadaitar da Mumuni na ya dabi'antu da wannan kyakkyawan dabi'a wacce ta kasance daga cikin mahiman hanyoyin da suke kai Bawa ya rabauta da karamar haduwa da wadanda Allah madaukakin sarki ya yabe su kamar yadda ya zo cikin Alkur'ani mai tsarki, Allah madaukakin sarki ya ce:((haske) yana cikin dakuna (watau masallatai) wadanda Allah ya yi umarni a daukaka a kuma ambaci sunansa a cikinsu,(wasu Mazaje) suna tasbihi a cikinsu safe da yamma*(Su) Mazaje ne wadanda kasuwanci da saye da sayarwa ba sa shagaltar da su daga ambaton Allah da kuma tsai da salla da ba da zakka, suna tsoron ranar da zukata da idanduna suke raurawa*(Suna haka ne) don Allah ya saka musu mafi kyan abin da suka aikata, kuma ya kara musu daga falalarsa. Allah kuwa yana arzuta wanda ya so ba da iyaka ba)Suratu Nuri daga Aya ta 36 zuwa Aya ta 38. Masu saurare a bayyane yake wadanda aka Ambato a wadannan Ayoyi masu Albarka, Allah madaukakin sarki zai saka musu da mafi kyau daga abinda suka aikata kuma ya yi musu kari daga falalarsa ba tare da hisabi ba, abinda ake nufi da kari shi ne ya arzuta su da mafi martaba na arzukinsa, to abin tambaya a nan ta yaya za mu cimma wannan matsayi? Hakan shi ne abinda Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi talib (a.s) ya amsa mana a cikin Littafin Nahjul-Balaga, a yayin da yake tilawar fadar Allah madaukakin sarki (Mazaje ne wadanda kasuwanci da saye da sayarwa ba sa shagaltar da su daga ambaton Allah da kuma tsai da salla da ba da zakka) sai ya ce da za ka misalta su da hankalinka cikin matsayinsu abin yabo da kuma wuraren zamansu bayanane, Hakika sun watsa Litattafan aiyukan su, kuma sun shagaltu da yiwa kansu Hisabi ga ko wani aiki karami ko babba da aka umarce su da shi, idan suka samu cewa sun yi sakaci wajen cika su ko kuma sun fice gona da iri sai su gaggauta komawa zuwa ga Allah madaukakin sarki cikin Nadama kuma suna neman yafiya gareshi, Sannan Imam (a.s) ya ci gaba da bayyana albarkatun yiwa kai hisabi na wadannan salihan Bayi 'yantattu yana mai cewa(daga ka gansu ka ga Alamomin shiriya, hasken Duhu da Mala'iku ke kaskantar da kai a gare su, kuma an saukar da nutsuwa a gare su , an kuma bude musu kofofin sammai, an yi musu tanadi da mazauni na karama, daga karshe Imam (a.s) ya kira mu da mu yi koyi da wadannan 'yantattu , mu kuma shagaltu da laifukanmu a maimakon shagaltuwa da na wasunmu, yana mai cewa: ka yiwa kanka Hisabi saboda kanka wato saboda maslahar kanka, domin watarai  daga cikin rayuwa ta nada nata hisabin). Da fatan Allah madaukakin sarki ya arzuta da wannan kyakkyawar dabi'a don albarkar riko da wulayar iyalar gidan Anabta tsarkaka.

**********************Musuc***************************

Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.