May 21, 2017 19:17 UTC

shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira

Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,Shirin na yau zai yi bayyani kan kyakkyawar dabi'ar amfani da Ni'imar Duniya ta kyakkyawar hanya kamar Lafiyar da Allah madaukakin sarki yayi wa Mutum, da makamantan hakan wajen aikata aiyukan alheri.amma kafin shiga cikin shirin sai a dakace da wannan.

*****************************Musuc*******************************

Masu saurare barkanmu da sake saduwa, Shirin na yau zai fara da Littafin Amaly na Shekh Tusy inda a cikin sa aka ruwaito hadisi daga Masoyinmu Ma'aikin Allah tsira da amnicin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya fadawa shahararen sahabinsa nan Abi Zarir-Gaffari cewa:( Ya Aba Zar da dama daga cikin Mutane suna yaudarar kansu domin ba sa amfani da Ni'imomi guda biyu,Lafiya da kuma Lokacin da ba sa wani aiki, Ya Aba Zar ka rabautu da biyar kafin biyar ya riske ka, Yarintarka kafin tsufa ya riske ka, lafiyarka kafin rashin rashin lafiya ta riske ka, wadatarka kafin talauci ya riske ka, lokacin da baka komai kafin ka shagaltu da wani aiki, rayuwarka kafin mutuwa ta riske ka).Hakika masu saurare duk wanda bai dabi'antu da wannan dabi'a ya yaudaru kuma ya yi hasara Duniya da Lahira kamar yadda Shugaban mu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) ya bayyana cikin riwayar da aka ruwaito a Littafin Ma'anil-Akhbar yana mai cewa:(mayaudari shi ne wanda ya yaudari shekarunsa Awa bayan Awa), Masu saurare hakika dabi'antuwa da wannan kyakkyawar dabi'a na kyakkyawan amfani da Ni'imar rayuwar Duniya wajen aikata aiki na gari, yana kare Mutum daga hasara a ranar Alkiyama kuma yana dawo da mafi girman Albarka, a Duniya da Lahira, kamar yadda Shugabanmu Amiri Muminin Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya shiryar da mu, Hakika cikin Littafin Kafi an ruwaito hadisin daga Imam Zainul-Abidin (a.s) ya kasance yana nanata wannan fada a cikin wa'azinsa ( Rayuwar Duniya kamar kamar kwanaki  uku ne a tsakanin ku, Ranar da kake cikinta da kuma wanda ta fice jiya da ba zai dawo ba har abada,idan ka kasance ka aikata aiki na alheri cikinsa ba za kayi bakin ciki da ficewarsa ba, za kuma ka yi farin ciki da abinda ka aikata cikin ranar fice, idan kuma ka fice iyaka cikin sa hasarar ka za ta kasance mai tsanani na ficewarsa da kuma fice iyaka da kayi cikinsa.kuma bayan Imam (a.s) ya Ambato halin Mutum cikin ranaikunsa , sai ya ci gaba da bayyanin hanyar dabi'antuwa da kyakkyawan amfani na kwanikan mutum wato shekarunsa yana mai cewa ko nemi taimakon Allah na kokarin wajen aikata kyawawa.Imam (a.s) ya ce :(ka yi aiki, aikin Mutuman da ba shi da wani fata na wasu kwanuka, face ranar da ya  wayi gari cikinsa da kuma Darensa, ka yi aiki, domin Allah mai taimako ne a kan hakan). Masu Saurare, Hakika Hadisai da dama sun yi tabbaci a kan dabi'antu da wannan kyakkyawar dabi'a gami da mahimancin ta, a duk lokacin da shekarun Mutun suka ja, ko da yake wajibi ne ma tun da farko,a cikin Littafin Kafi, an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Muhamad Bakir (a.s) ya ce:(Idan Mutum ya kai shekaru 40, sai ace masa ya riki damararsa domin babu wani uziri a gare shi, kuma Dan shekaru 40 bai fi hakki na kiyayewa ba a kan Dan Shekaru 20, domin duk abinda ake nema guda ne , ka yi aiki da abinda ke gabanka, kadda ka damu da fifikon Magana da kuma abinda Mutane ke fada kanka). Masu saurare wani Nassin na daban kuma ya bayyana cewa rashin dabi'antuwa da wannan kyakkyawar dabi'a ta Imani alamar fita daga ganki ne daga kangin Duniya, 'yan tuwa daga kanginta shi ne mabudin dabi'antuwa da dabi'ar kyakkyawar amfani da Lokutan Duniya, a cikin Littafin Kafi an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:(Dan kaso shi ne wanda ya kange kansa da abinda ke cikin Duniya kadai daga neman Lahira ).

**************************Musuc*************************

Masu Saurare barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa shirin na zababbun aiyuka na zo muku ne kai tsaye daga sashen Hausa na muryar jumhoriyar musulinci ta Iran dake nan birnin Tehran, ci gaban Shirin zai fara da hadisin Shugaban Halittu (s.a.w.a) wacce aka ruwaito a cikin Littafin Man La Yahduruhul-Fakih yana mai cewa:(albarka ta tabbata ga wanda ya yi tsahon shekaru, ya kuma kyautata aiyukansa da makomarsa yayin da Ubangijinsa ya yarda da shi, Bone kuma ya tabbata ga wanda yayi tsahon shekaru, amma ya munana aikinsa da kuma makomarsa yayin da Ubangijinsa madaukaki ya yi fishi da shi). Domin haka dabi'antuwa da dabi'ar kyakkyawan amfani na lokacin Bawa na yin sanadin rabauta da yardar Allah da kuma tsira daga mumunar makoma gami da fishin Ubangiji madaukakin sarki, Hakika Masu Saurare Hadisai da dama sun shiryar da mu cewa dabi'antuwar da dabi'ar kyakkyawar amfani da lokacin Mutum na Duniya ta hanyar kyawawen aiyuka na daga cikin dabi'un masu tsoron Allah, da suka kasance Shugabani na Masoyan Allah madaukakin sarki, A cikin Littafin Guraru Hikam na Amidy an ruwaito hadisi daga Shugaban Masu tsoron Allah, Imam Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya ce:(hanyar masu tsoron Allah amfani da lokaci da kuma kyakkyawan guziri) a wannan Hadisi masu Saurare, Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) na bayani ne kan mahimancin amfani da Lokaci da ya kamata mutum ya ci moriyar lokacin sa wajen zuba jari da kuma kuziri na rayuwarsa ta Lahira, har ila yau cikin Littafin Guraru Hikam, an ruwaito hadisi daga Imam Ali (a.s) inda a cikin sa yake wasici ga ko wani Mumuni yana mai cewa:(Ka riki daga kanka domin kanka, kuma ka rike guziri na ranarka saboda Gobanka, ka yi mfani da Lokacin dake ciki) ma'anar wannan hadisi shi ne Mutum ya yi kyakyawan aiki saboda kansa kuma ya yi kyakkyawan guziri ta hanyar kyawawen aiyuka saboda gobansa wato ranar Lahira kuma ya yi amfani da Lokacin da yake da shi a nan Duniya wajen aikata alheri kafin ya rasa wannan dama.Masu Saurare kamar yadda wannan kyakkyawar dabi'a na daga cikin fitatun dabi'un Mumunai da suka kasance kansa domin Allah da kuma ranar Lahira, Ya zo cikin Littafin Mizanul-Hikima daga Shugabanmu Imam Hasan Mujtaba (a.s) a wani bangare na wasiyarsa yana cewa:(Ya Kai Dan Adam ba ka gushe cikin rushe shekarunka tun bayan da ka fado daga cikin Ma'aifiyarka, domin haka ka riki don Allah da abinda ke hanunka, ma'ana shi ne ka kara guziri da aiyuka na alheri a cikin rayukar ta Duniya a kan abinda ke hanuka, domin shi Mumuni yana aiki ne domin yin guzirin na ranar Lahira  , shi kuma kafiri yana aiki ne domin jin dadin Duniya). Masu saurare daga misdakin dabi'antuwa da wannan kyakkyawar dabi'a a aikace kasancewar Mumuni yana gina rayuwarsa ta Lahira da ta kasance  madawwamiya ta hanyar amfani da Ni'imar rayuwar Duniya, domin ita kanta mai kushewa ce, cikin Littafin Kafi, an ruwaito Hadisi daga Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) ya ce:( nawa daga cikin masu neman Duniya da har abada ba za su sameta ba, kuma wanda ya sametan ba ,Hakika ya rabu da ita, kadda ka shagalta kanka wajen neman ta ta hanyar aikinka,ka nema ta a wajen mai bayar da ita da kuma mamallakinta, nawa daga cikin masu tsananin riko da kuma kwadayinta ta hallakar da su, ka shagaltu da abinda ka samu cikin ta wajen neman Lahirarka).

**********************Musuc***************************

Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.