Oct 03, 2017 09:01 UTC

Yau Jumma'a 14-Mehr-1396H.SH=15-Muharram-1439H.K=06-Octoba -2017M.

01-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 850 da suka gabata a rana irin ta yau wato 15-Muharram-589H.K. Aka haifi Aliyu bin Musa bin Jaafar wanda aka fi saninsa da Sayyeed bin Tawoos a birnin Hilla na kasar Iraqi. Ibn Tawoos ya fara karatun sharer fage a mahaifarsa, sannan ya je birnin Bagdaza inda ya kamala karatunsa a gaban manya manyan malamai na zamaninsa. Daga karshe Ibn tawoos ya zama malami mafi shahara a zamaninsa ya kuma wallafa litattafai da dama saga cikinsu akwai littafi mai suna «اللهوف» dangane da waki'ar karbala. Sai kuma «سعدالسعود» و «الاقبال بصالح الاعمال» daga katshe Ibn Tawoos ya rasu a shekara ta 664 H.K. yana dan shekara 75 a duniya.

02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 44 da suka gabata a rana irin ta yau wato 06-Octoba-1973M. Aka fara yaki na 4 tsakanin Larabawa da HKI, a wannan yakin dai sojojin masar sun yi wa sojojin HKI ba zata a mashigar ruwa ta Swis inda suka kwace ts suka kuma shiga yankin Sinaa. Yahudawan sun yi asarori masu yawa a hannun sojojin Siria da Masar. Daga baya Amurka da tsohuwar tarayyar Soviet sun shiga tsakani aka dakatar da bude wuta sannan aka maida batun ga MDD.

03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 36 da suka gabata a rana irin ta yau wato 06-Octoban-1981M. Wasu sojojin kasar Masar masu kishin addinin karkashin jagorancin Khalid Islambuli sun kasha shugaban kasar Masar na lokacin Mohammad Anwar Saadad. Dalilin kashe shi, shi ne yerjejeniyar sulhu tsakanin masar da HKI mai suna Yerjejeniyar Camp Deviv da ya rattabawa hannu a shekara ta 1978, inda a ciki ya amince da samuwar HKI. Kulla wannan yerjejeniyar ya fusata kasashen musulmi da larabawa. Khalid ya kasha Saadad ne a lokacinda ake fareti a gabansa a birnin Alkahira. Bayan kisan an kasam sojoji kimani 3000 aka gurfanar da su a gaban kotun soje wacce ta yankewa da dama daga cikinsu hukuncin kisa.

 

Tags