Mar 05, 2018 18:17 UTC

Yau Litinin 28-Esfand-1396H.Sh=01-Rajab-1439H.K=19-Maris-2018M

01-Masu sauraro ko kun san cewa yau ce daya ga watan Rajab na wannan shekara ta 1439 Hijira kamaryya. Watan Rajab yana da daraja sosai. Da shi da wattanin Shaaban da Ramadan suna da daraja musamman ga wanda yake son samun kusanci ga Allah wajen azuminsu. Yana daga cikin falalar wadannan watannin manzon Allah yana cewa watan Rajab watan ubangiji na ne, sai kuma shaaban wata nane Ramadan kuma watan al-umma ta. A cikin watan ne aka aiki manzon Allah (s) a matsayin annabi manzo. Sannan a cikinsa ne aka haifi Amirul Muminina Aliyu dan Abitalib (a) .

02-Masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1382 da suka gabata a rana irin ta yau wato 01-Rajab-57H.K. Bisa wasu ruwayoyi a rana irin ta yau ce aka haifi Imam Mohammad Bakir limami na 5 daga cikin limamai masu tsarki daga cikin iyalan gidan manzon Allah (a) a Madina. Bayan shahadar mahaifinsa Imam Aliyu Zainul Abidin (a) ragamar jagorancin al-ummar kakansa ya koma gare shi. Sannan ya zo dai lokacinda daular bani umayya ta fara rauni. Don haka Imam Muhammad Bakir (a) ya yi amfani da wannan damar wajen yada ilmin addini da na zamani a cikin al-ummar musulmi. Yana da dalibai masu yawa a fannonin ilmi da dama. Muna taya al-ummar musulmi murnar ranar haihuwar tauraro na 5 daga cikin taurari masu tsarki daga iyalan gidan manzon Allah (s).

03-Daga karshe masu sauraro ko kun san cewa shekaru 1076 da suka gabata a rana irin ta yau wato 01-Rajab-363H.K. Numan bin Muhammad Tamimi babban malamin addini dan kasar Mirocco ya rasu. An haife shi a shekara ta 259 H.K. a kasar Morocco bayan kammala karatu a gida, kan mazhanar malikiyya ya hadu da malaman daular Fatumiyya na kasar Masar, wadanda suka maida shi mazhabar shia Isma'iliyya. Numan ya ruke babban matsayi na muftin wannan mazhabar ya kuma rubuta litattsafai da dama . daga cikinsu akwai "Attaunhid wal-imamah" da'a'umul Islam" da kuma sharhul Akhbar.

 

Tags