May 03, 2016 14:16 UTC

Hedikwatar tsaron Najeriya ta fitar da wata sanarwa da ke ankarar da jama’a kan yadda ‘yan ta’addar boko haram ke jan hankalin matasa ta hanyar basu lamani, musamman a shiyyar Arewa maso Gabashin kasar.

yau shirin na maida hankali ne kan wata sanarwa da hedkwatar tsaron Najeriya ta fitar wace ke ankarar da jama’a kan yadda ‘yan ta’addar boko haram ke jan hankalin matasa ta hanyar basu lamani, musamman a shiyyar Arewa maso Gabas. 

Wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin ma’aikatar tsaron kasar Janar Rabe Abubakar ta ce tuni kungiyar Boko Haram ke daukar Matasa ta hanyar ba su rancen kudi.

Sanarwar ta ce kungiyar na janyo hankalin masu kananan sana’oi kamar masu sana’ar dinki da mahauta da wasu sana’o'in hannu.

Bayanai sun nuna cewa ana yaudarar matasa da kudi a matsayin jari amma ba biya zasuyi ba, ana hakane kuwa domin ayi dabarar janyosu jiki a tura musu mummunan akida.

To idan dai za'aayi la'akari da yadda wannan kungiyar ta boko haram tayi mubayi'a ga kungiyar 'yan ta'adan (IS) hakan zai iya zama babban kalubale ga yankin yammacin Afirka bama wai Najeriya ba kawai, duba da yadda talauci da halin kunci da rashin aikin yi da matasan yankin ke fama da shi.

Ma’aikatar tsaron ta Najeriya ta bukaci al’umma musamman a yankin arewa maso gabashi su yi takatsantsan da dubarun da ‘Yan Boko Haram din ke bi na kokarin sun samu sabbin mabiya baya an tarwatsa su.

Sannan sanarwar ta gargadi mutane su kaucewa karbar rance daga hannun wadanda hukuma ba ta san da zamansu ba.



Tags