Mahimancin girmama iyaye
May 21, 2016 02:03 UTC
A shiryen shiryen da ya gabata mun yi bayyani kan mahimancin girmama iyaye , saboda mahimancin wannan maudi'I yau ma za mu ci gaba daga inda muka tsaya
Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,a shiryen shiryen da ya gabata mun yi bayyani kan mahimancin girmama iyaye , saboda mahimancin wannan maudi'I yau ma za mu ci gaba daga inda muka tsaya,kafin nan bari mu saurari tanadin da aka yi mana a kan faifai.****************************Musuc***************************
Masu saurare, shirin na yau zai fara da kalaman hasken shiriya ma'aikin Allah tsira da aminccin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, a cikin riwayar da aka rauwaito cikin Littafin Amaly na shekh Tusy, inda yake bayyana girman ladan dake tattare ga wanda ya dabi'antu da dabi'ar girmama iyaye, Ma'aikin Allah (s.a.w) ya ce:(babu wani yaro mai biyayya ga ma'aifansa da zai dibi ma'aifansa cikin tausayi sai ya kasance an rubuta masa a ko wani diba daya Lada na aikin Hajji, sai aka ce Ya Ma'aikin Allah ko da a ko wata rana ya kale su so dari?sai Ma'aikin Allah (s.a.w) ya ce:Na'am Allah shine mafi girma kuma mafi tsarkaka).har ila yau cikin wannan Littafi na Amaly, an ruwaito wani hadisi daga Ma'aikin Allah (s.a.w) ya ce:(kallon malami ibada ne, kallon shugaba mai adalci ibada ne, kallo irin na tausayi ga ma'aifa ibada ne, da kuma kalon dan uwanka saboda Allah madaukakin sarki ibada ne), masu saurare a cikin wani hadisi na daban , shekh Tusy ya ruwaito makamancin wannan hadisi daga shahararen sahabin nan Abi Zarilgaffari (yardar Allah ta tabbata a gareshi) shidai wannan hadisi ya hada misdakin shugaba Adali, ma'aifi ga Al'umma da kuma iyaye a Nasabi,hakika an ruwaito hadisin da Sanadin Hajar Almazdi ya ce:(wata rana na isa garin Makka sai na samu Abu Zaru Algaffari yardar Allah ta tabbata a gareshi, kuma hakika a wannan lokaci, Umar bn Khatab ya zo aikin hajji a tare da shi a kwai wani gungu na sahabai daga cikin Ansar da Muhajirin daga cikin su har da Aliyu bn Abi Talib (a.s), daga cikin mutanan dake cikin harami a wannan lokaci na kasance ina zaune a kusan Abi Zar, sai ga Aliyu bn Abi Talib(a.s) ya fice ta gabanmu sannan ya nemi wani guri a gabanmu ya kabarta salla, sai Abu Zar ya kwara masu ido yana kallonsa sai na ce Allah yay i maka Rahama Ya Abar Zar wani irin kallo ne kake yiwa Imam Ali (a.s) Akwai abinda kake yi masa fargaba? Sai Abu Zar ya ce: ina yi masa wannan kallo ne domin na ji ma'aikin Allah (s.a.w) yana cewa:(kallon Aliyu bn Abi Talib Ibada ne, kallon irin na tausayi da rahama ga iyaye ibada ne, kuma kallon Littafi wato Alkur'ani ibada ne, kallon Ka'afa wato Dakin Allah Ibada ne).masu saurare wannan hadisi mai albarka yana tunatar da mu da shahararren hadisin nan na cikin khudubar da Ma'aikin Allah (s.a.w) yay i wa Dan Uwansa kuma wasiyinsa Aliyu bn Abi Talib(a.s) inda y ace:( Ya Ali Ni da Kai iyayen wannan Al'umma ne), baya ga haka ma, hadisai da dama sun yi wasiya bisa wasiyar da Ayoyin Alkur'ani mai tsarki su kayi na yin biyayya da kuma girmama iyaye tare kuma da hani mai tsanani na saba musu, wannan hani kuma ya shafi dukkanin iyaye da sune suka aifi mutune ko kuma iyaye na nasabi kamar Nabiyul Akrman da iyalan gidansa Ma'asuman amincin Allah ya tabbata a gare shi baki daya.
*******************Musuc*****************************
Masu saurare, barkanmu da sake saduwa,ci gaban shirin zai yi bayyani kan mahimancin sada zumanci domin shi na daga cikin tsarkakun dabi'un da Allah madaukakin sarki ya yi wasici a kansa kuma yace yana son masu wannan dabi'a kamar yadda shugaban mursalai tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka yayi ishara da shi,a cikin litattafan Sahifatu Ridha da Uyunul Akhbaru Ridha (a.s) an ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka yace:( duk wanda ya mini tabbacin abu guda zan yi masa tabbacin abubuwa guda Hudu, wanda ya sada zumunci, zai samu soyayyar Allah madaukakin sarki, ya kuma fadada Arzikinsa, ya kara masa yawan kwanakinsa kuma ya sanya shi cikin Aljannar da ya yi masa Alkawari) kamar yadda dabi'antuwa da dabi'ar sada zumunci ya kan zamanto sababin rabauta da yardar iyalan gidan Annabta da Rahama wato iyalen gidan Manzon Allah tsarkaka, kuma yardarsu , yardar Allah madaukakin sarki ne, hakika Shekh Tusy cikin Littafin Amaly ya ruwaito hadisi daga salihin Bawan nan Dawud Arruka ya ce :(na kasance ina zaune wajen babban Abdullahi Imam Sadik(a.s) sai ya ce min Ya Dawud hakika an kwada mana aiyukanku ranar Alkhamis, sai naga daga cikin aiyukan da aka gwada min naka a kwai sada zumunci da ka yi ga Dan Uwanka , hakan kuma ya sanya ni farinciki, hakika na san ziyarar da ka kai masa ta fi sauri ga karshen rayuwarsa, Dawud Arruka ya ce: ya kasance ina Dan uwa da bas hi da halaye masu kyau , lokacin da labarinsa ya same ni da kuma munanan halayansa ga iyalensa , sai na gaggauta kai masa ziyara tare da kaiwa iyalinsa taimako, kafin na bar cikin garin Makka, lokacin da na isa garin Madina sai babban Abdullahi Sadik (a.s) ya bani labarin abinda na yi kafin na bar garin Makka.
Masu saurare, dabi'antuwa da dabi'ar sada zumunci koyi ne ga shugaban kyawawen dabi'u Mustapa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, a cikin Littafin Gaiba na Shekh Saduk an ruwaito hadisi daga Salimatou baiwar Imam Sadik (a.s) ta ce na kasance wajen babban Abdullahi Ja'afaru bn Muhamad (a.s) yayin da yake gwadon mutuwa, bayan ya suma kuma ya falfado , sai ya ce ku baiwa Hasan bn Ali wanda ake kira da Aftas dinari 70, ku baiwa wane da wane dinare kaza da kaza. Wato shi Aftas ya kasance yana cutar da Imam Sadik (a.s), a kwai lokacin da ya yi kokarin yi masa kisan killa, domin haka , ita baiwar ta Imam (a.s) ta yi mamaki kan yadda Imam ya dage ga taimakonsa, sai ta ce: shin z aka taimakawa Mutuman da ya yi yukurin kashe ka? Sai Imam Sadik (a.s) ya amsa mata da cewa shin kina so ka in kasance cikin Mutanan da Allah madaukakin sarki ya ce a kansu:(Da Wadanda suke sadar da abin da Allah ya yi umarni a sadar da shi (shi ne zumunci), suke kuma tsoron Ubangijinsu, kuma suke tsoron mumunan hisabi) suratu Ra'ad Aya ta 21, haka ne ya kai Salima hakika Allah madaukakin sarki ya halici Aljanna ya kuma tsarkake ta,da tsarkin kamshinta, kuma ba a kai ga jin kamshinta sai an yi tafiya ta shekara dubu, mai sabawa iyaye da wanda ya yanke zumunci ba ya samu rabutar jin kamshinta). Har ila yau daga cikin girman tasiri sada zumunci, albarkarsa ta kan shafi mumuni da wanda ma ba mumuni ba, a cikin Littafin Biharu Anwar, an ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da aminicin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa:(sada zumunci ya kan yi sanadin gina ko gyara gidaje kuma yana karawa mai yinsa yawan shekaru ko da kuma ya kasance ba ya daga cikin zababbu ) wato koda ba mumuni ba ne, har ila yau wannan dabi'a mai kyau na zamanto sanadin samun gafarar Ubangiji da kyakkyawar makoma. Kamar yadda Ma'aikin Allah (s.a.w) ke cewa:(sada zumunci yana sassauta hisabi kuma garkuwa ne ga mumunar mutuwa) da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu ikon saka zumunci amincecce gareshi.
*****************Musuc*******************
Masu saurare, ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo jiki, a nan za mu dasa sai kuma a maku da nag aba da yardar Allah za a jimu dauke da ci gaban shirin, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala,nike muku fatan alheri, wassalama alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.