Sada Zumunci
Mahimancin sada Zumunci
Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,a shiryen da ya gabata mun dauko bayyani kan mahimancin sada Zumunci sai hali ya yi mana lokacinsa, domin mahimancin wannan maudi'I bari mu ci gaba da shi, kafin nan bari mu saurari tanadin da a kayi mana a kan faifai.
******************************Musuc*****************************
Masu saurare, sada zumunci na daga cikin kyawawen dabi'un da girman matsayin ya sanya Allah madaukakin sarki ya tabbatar da shi kusa da tsoron shi, kamar yadda Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) ya bayyana mana cikin riwayar da Shekh Ayyashi yardar Allah ta tabbata a gareshi ya kawo cikin Tafsirinsa, yayin da aka tambayi Imam (a.s) kan fadar Allah madaukakin sarki (ku ji tsoron Allah wanda kuke tambayar(taimako a tsakaninku) da Shi, kuma (kuji tsoron hakkokin)Zumunta. Hakika Allah ya kasance mai kiwo ne a gareku) suratu Nisa'I karshen Aya ta farko,sai Imam (a.s) ya amsa da cewa shine zumuncin da Allah tabaraka wa ta'ala ya umarci Mutane da sada shi kuma ya girmama shi, shin ba ka ga ba yadda ya sanya shi tare da shi ba) baya ga sama zumunci tsakanin mutane an yi umarni ga zumunci na ma'anawi wato zada zumunci ga Mumunai da shugabaninsu Iyalan gidan Annabta (amincin Allah ya tabbata a garesu), A cikin Tafsirin Ayyashi, an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Sadik(a.s) ya ce:(Zumunci ya nada babban matsayi a wajen Allah, yana cewa Ya Ubangiji ka yi salati ga wanda ya sadani, kuma ya yanke ga wanda ya yankeni, shine sada Zumunci ga iyalan Annabi Muhamad tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, kuma zada zumuncin ko wani mumuni shine fadar Allah madaukakin sarki (Da wadanda suke sadar da abin da Allah ya yi Umarni da sadar da shi(shi ne Zumunci) suke kuma tsoron Ubangijinsu,kuma suke tsoron mummunan hisabi) suratu Ra'adi Aya ta 21, har ila yau daga cikin misdakin zumunci, sada shi ga makusanta, masoya da kuma abokanan Imani da hakan nada falala masu yawan gaske kamar yadda shugaban shiriya Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya shiryar da mu, cikin hadisin da aka ruwaito cikin Littafin Kurbatu Isnad:(Hakika kyautata na kore mumuna, kuma hakika Sadaka na kashe fishin Ubangiji, shi kuma Zumunci na kara yawan kwanika, kuma yana kore talauci, fadar La Haula wala kuwata illa billah (ma'ana babu wani karfi face na Allah) waraka ne na rashin lafiya 99 ).kamar yadda daga cikin Albarkar dake tattare da Zumunci,Karin yawan arziki da kuma wanzuwar soyayya a tsakanin Al'umma,Hakika cikin Littafin Kurbul Isnad an ruwaito wani hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:(sada Zumanci yana kara yawan kwanuka, ya na kara yawan dukiya kuma yana sanya soyayya a cikin Ahli) kamar yadda cikin Littafin Khisal na shekh Saduk an ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(duk wanda yake so Allah madaukakin sarki ya yawalta masa dukiyarsa ya kuma kara masa yawan shekarunsa to ya zada zumunci), a bangaren Lada da kyakyawan sakamako na ranar kiyama ga mai sada zumunci , hakika an ruwaito hadisi cikin Litattafai da dama masu inganci daga cikin su Littafin Amaly na shekh Saduk (Y.t) daga Ma'aikin Allah (s.a.w) ya ce:(duk wanda ya ziyarci dan uwansa da niyar sada Zumunci Allah zai rubuta masa Ladan shahidi dari (wato Ladan wanda ya rasu ta hanyar Allah) kuma duk takon da zai yi za a rubuta masa Lada dubu 40 a kuma goge masa zunubai dubu 40 kuma a daukaka darajarsa kamar na Bawan Allah da ya kwashe shekaru 100 yana bauta cikin hakuri), Masu saurare ba boyayyan abu ba ne ga kowa wannan girman Lada ya kan cika ga wanda ya dabi'antu da wadannan kyawawen dabi'u saboda kusancinsa da Ubangiji, a cikin Littafin Amaly na shekh Saduk an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Zainul Abidin (a.s) ya ce:( babu wani mataki da Allah madaukakin sarki ya fi so kamar matakai guda biyu, mataki na farko wanda mumuni zai yi wajen jihadi saboda Allah, na biyu kwa kuma shine zama Zumunci).
***********************Musuc*****************************
Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai fara ne da riwayar Shekh Saduk yardar Allah ta tabbata a gareshi cikin Littafinsa Alkhisal daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka y ace:(Hakika a cikin Aljanna a kwai wani matsayi da babu wanda zai isa zuwa gare shi sai Shugaba Adali, ko kuma mai sada Zumunci, ko mai yawan Iyali kuma mai hankuri). Kamar yadda daga cikin Albarkatun dake tattare da sada zumunci yak an zamanto hanyar karbar kyawawen aiyuka, a cikin Littafin Zuhdu na shekh Husain bn Saeed, an ruwaito ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam sadik (a.s) ya ce:(hakika sada Zumunci yana tsarkake aiyuka, yana kuma yawalta dukiya, ya na sanya sasauci da sauki ga hisabi,yana kuma kare bala'I da kuma kara shekaru).a cikin Littafin Uyunul Akhbar an ruwaito hadisi daga Imam Ridha (a.s) ya ce:(duk wanda yake so Karin yawan kwanuka a duniya kuma a yawalta masa Arzikinsa to ya sada zumunci) har ila yau cikin Littafin Amaly na shekh Saduk an ruwaito hadisi daga shugabanmu Mumunai Aliyu bn Abi talib (a.s) ya cewa daya daga cikin sahabinsa mai suna Nufu AlBakkali yardar Allah ta tabbata a gareshi, ya ce masa:( Ya Nuf ka sada zumunci sai Allah madaukakin sarki ya kara maka yawan shekarunka a Duniya), kuma Hakika cikin Litattafai da dama masu Inganci kamar su Dala'ilu na humairi, da Rijalu Kashi da saurensu an ruwaito hadisi daga Muyasar yardar Allah ta tabbata a gare shi domin shi yana daga cikin sahaban shugabanin shiriya Bakir da Sadik amincin Allah ya tabbata a gare su ya ce:(na shiga wajen babban Ja'afar Imam Bakir (a.s) mun kasance jama'a guda a gurin Imam sai aka Ambato zada zumunci da kuma makusanta, sai Abu Ja'afar (a.s) y ace min Ya Muyasar hakika karshen ajalinka ya zo ba so day aba so biyu ba sai aka jinkirta maka shi saboda zumuncinka ga 'yan uwanka).a wata riwayar kuwa ta daban an daya daga cikin shugabanin shiriya Imam Sadik ko imam Bakir (A.s) ya ce masa (Ya Muyasar hakika ina zton kai mai sada zumunci ne ga makusatanka, sai na ce na'am haka ne fansar kaina a gareku, domin na kasance ina aiki a kasuwa kuma albashina shine dirhami biyu, idan an bani sai in baiwa kanwar ma'aifiyata dirhami guda kuma in baiwa kanwar ma'aifina dirhami guda, sai Imam (a.s) ya ce mani hakika karshen ajalinka ya zo har so biyu amma ake jinkirta shi).da fartan Allah madaukakin sarki ya bamu ikon dabi'antuwa da wannan dabi'a mai kyau ta zumunci mu yi koyi da zababbun halittu Muhamad tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka.
*****************Musuc*******************
Masu saurare, ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo jiki, a nan za mu dasa sai kuma a maku da nag aba da yardar Allah za a jimu dauke da ci gaban shirin, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala,nike muku fatan alheri, wassalama alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.