Sada Zumunci (2)
A shirye shiryen da suka gabata mun yi bayyani kan mahimancin sada Zumunci amma ganin mahimancin wannan maudi'I za mu ci gaba da shi
Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,a shirye shiryen da suka gabata mun yi bayyani kan mahimancin sada Zumunci amma ganin mahimancin wannan maudi'I za mu ci gaba da shi, kafin nan bari mu saurari tanadin da a kayi mana a kan faifai.
******************************Musuc*****************************
Masu saurare, a cikin wannan shiri za mu kawo muku wasu sashen riwayoyi da suke bayyani kan falalar Zumunci tare kuma da irin mumunan sakamakon da tattare da wanda ya yanke shi.imma ya kasance zumunci na makusanta ne ,na abotaka ne ko kuma na iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka ne, kamar yadda hadisai da dama suka Ambato, a cikin Tafsiril Gummy na shekh Aliyu bn Ibrahim AlGummy an ruwaito hadisi daga shugabanmu Babban Hasan Alkazim (a.s) yayin da yake bayar da amsar kan fadar Allah madaukakin sarki (Da wadanda suke sadar da abin da Allah ya yi Umarni da sadar da shi(shi ne Zumunci) suke kuma tsoron Ubangijinsu,kuma suke tsoron mummunan hisabi) suratu Ra'adi Aya ta 21sai Imam kazim (a.s) ya ce:(Hakika Zumunci ga iyalan gidan ma'aikin Allah tsarkaka ya nada babban matsayi a wajen Allah, yana cewa Ya Ubangiji ka yi salati ga wanda ya sadani, kuma ya yanke ga wanda ya yankeni, kuma wannan zumnci na gudana ga ko wani irin zumunci) ma'ana abinda ake nufi ya shafi har da zumunci na nasaba. Da ya kamata ya kasance da niyar sada zumuncin muhamadiya na wulaya, ma'ana da niyar da'a ko biyayya ga Allah tabaraka wa ta'ala da Ma'aikinsa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka domin Allah ya yi Umarni da sada zumunci a gare su.kuma hakika Allah ya galgadi bayinsa kan yanke zumunci ko wani iri sannan ya sanya hakan a matsayin misdikin fasadi a diron kasa, a cikin suratu Muhamad Aya ta 22 Allah madaukakin sarki ya ce: :(Shin to watakila kun kusanta idan kuka bada baya (kuka ki yin yakin) kada ku zo ku rika yin barna a bayan kasa ku kuma yanke zumuntarku?)har ila yau an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Bakir (a.s) ya ce (Babana Aliyu bn Husain (a.s) ya fada mini cewa ya kai dana na haneka da abotaka da mai yanke zumunci domin na same shi La'ancecce ne a cikin Littafin Allah mai tsarki sai ya karanto wadannan Ayoyi (Shin to watakila kun kusanta idan kuka bada baya (kuka ki yin yakin) kada ku zo ku rika yin barna a bayan kasa ku kuma yanke zumuntarku?wadancan su ne wadanda Allah ya tsinewa sai ya kurumtar da su ya kuma makantar da maganansu(da ji ko ganin gaskiya) suratu Muhamad Aya ta 22 da kuma ta 23,har ila yau cikin wani hadisi Annabi Muhamad(s.a.w) ya ja hankalin Al'ummarsa kan su guji yanke zumunci domin hakan na daga cikin zunuban da suke haramtawa mutum rabauta da gidan Aljanna. A cikin Littafin Al-istisas an ruwaito hadisi daga ma'aikin Allah (s.a.w) na cewa:(mai yanke zumunci ba zai shiga Aljanna ba), har ila yau yanke zumunci na daga cikin zunuban dake gadarwa mai shi talauci, a cikin Littafin Alkhisal an ruwaito hadisi daga shugaban mumunai Aliyu bn Abi talib (a.s) na cewa (yanke zumunci na gadarwa mai shi talauci), a cikin wata riwaya ta daban kuwa da shekh Mufid ya ruwaito cikin littafinsa mai suna Amaly, shugaban mumunai Aliyu bn Abi talib (a.s) ya ce:(abubuwa guda uku mai yinsu ba zai mutu ba har sai ya ga mumunan sakamakonsu, kiyayya da bata da dalili, yanke zumunci,da kuma rantsuwa kan karya, idan kuma mutum ya na so ya gaggauta samun ladan biyayya ga Ubangiji ya gaggauta sada zumunci, hakika wasu Mutane sun kasance fajirai sai suka zada zumnucinsu Dukiyarsu sai ta yalwata, kuma hakika rantsuwa kan karya da yanke zumunci ya sanya rahamar dake cikin gida ta kushe) kamar yadda yanke zumuncin na daga cikin zunuban dake yin sanadin gaggauta saukar da Ukuba ko azaba ga mai yinsa, a cikin Littafin Khisal an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Bakir (a.s) ya ce:(ababe guda hudu suna yin sanadiyar gaggauta saukar azaba da ukuba ga mai yinsu, Mutuman da ka kyautata masa sai ya mayar maka da mumuna, mutuman da ba ka kinsa sai yake kiyayya da kai ba tare da wani dalili ba,rashin cika alkawari,sai kuma yanke zumunci ga mutuman da yake sada zumunci ) da fatan Allah madaukakin sarki ya tsaremu da irin wadannan munanan dabi'u.
********************Musuc****************************
Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai fara da ruwayar sikatu Islam Kulaini wacce ya ruwaito cikin Littafinsa kafi daga Umar bn Yazid ya ce na tambayi Imam Sadik (a.s) kan fadar Allah madaukakin sarki (Da wadanda suke sadar da abin da Allah ya yi Umarni da sadar da shi(shi ne Zumunci) suratu Ra'adi Aya ta 21 sai Imam (a.s) ya amsa da cewa wannan Aya ta sauka kan Zumuncin Iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka, kuma na iya kasancewa kan makusantanka, kada ka kasance ga wanda ke ganin cewa Ayar kur'ani ta sauka a kan abu guda kacal, ma'ana kada ga kasance mai katange Ayar kur'ani ga misdaki guda kacal) har ila yau cikin Littafin kafi, an ruwaito hadisi daga Hajami bn Hamid ya ce na cewa babban Abadillahi Imam Sadik (a.s) idanya kasance makusanta ba sa kan Addinin da neke kan sa ba, shin suna da hakki a kaina? Sai Imam (a.s) y ace masa tabas domin shi hakin Zumunci babu abinda yake sanya a yanke sa, kuma idan sun kasance kan Addinin da kake kansa to hakin zumunci su ya ninka a kanka, domin a kwai hakin zumunci na kusanci da kuma hakin zumunci na musulinci).Hakika Masu saurare hadisai da dama su yi kira tare da tabbaci wajen dabi'antuwa da wannan kyakkyawar dabi'a tare kuma da bayyana irin albarkatun dake tattare da shi, ta hanyoyi a aikace daga ciki a kwai tambayar lafiyar makusanta da gaishe su, a cikin Littafin Kafi, an ruwaito hadisi daga shugaban mumunai Aliyu bn Abi talib (a.s) ya ce:(ku sada zumuncinku ko da da sallama ne, Allah tabaraka wata'ala na cewa(ku ji tsoron Allah wanda kuke tambayar(taimako a tsakaninku) da Shi, kuma (kuji tsoron hakkokin)Zumunta. Hakika Allah ya kasance mai kiwo ne a gareku) karshen farkon suratu Nisa'i), Imam Sadik (a.s) ya ce:(hakika sada Zumunci da biyayya na saukaka hisabi kuma suna kiyaye yin sabo, ku sada zumunci ga makusantanku kuma ku girmama 'yan uwanku ko da da yi musu sallama ne ko kuma amsa sallamarsu)ma'ana ya meda sallama da mfi kyau kamar yadda Alkur'ani mai tsarki ya yi umarni.a cikin Littafin Kurbul Isnad, Imam (a.s) yayi nuni ga fiyayeyyen tabbacin wannan dabi'a mai kyau shine kokari wajen kore cutarwa ga makusanta ko da na cikin zukata ne, Imam (a.s) ya ce:(ka sada zumunci ko da shayar da ruwa ne kuma mafi fifiko wajen zada zumanci daina cutar da Dan uwanka).abinda babu kokwanto cikinsa shine mafi girman tabbacin sada zumunci da yafi lada, sada zumunci ga wadanda suka fi cutar da kai daga cikin makusanta, a cikin Littafin Kafi, an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:(hakika wani mutum ya je wajen ma'aikin Allah (s.a.w) ya ce masa ya ma'aikin Allah zuriyarmu sun yi watsi da ni sun yanke zumunci da ni babu abinda suke face zaki da batanci gareni shin nima in yi watsi da su? Sai ma'aikin Allah y ace masa idan kana so Allah ya yi watsi da ku gaba ko? Sai mutuman nan ya ce to ya ya zan yi?sai ma'aikin Allah ya ce ka ziyarci duk wanda ya daina ziyartarka ka sada zumunci ga duk wanda ya yanke zumuncinsa gareka, ka baiwa duk wanda ya hanaka, ka yi afuwa ga duk wanda ya zalumceka,idan ka aikata haka, sai ya zamanto ka sauke nauyin da ya rataya a kanka garesu)
*********************Musuc**********************************
Masu saurare, ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo jiki a nan za mu dasa Aya sai kuma a muku mai zuwa da yardar Allah za a jimu da ci gaban shirin, a madadin wadanda suka taimakawa shir