May 21, 2016 02:21 UTC

A shirye shiryenmu da suka gabata mun yi bayyani kan mahimancin kyakkyawan dabi'ar sada Zumunci a yau ma shirin namu zai ci gaba da wannan maudi'in saboda mahimancinsa

Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,a shirye shiryenmu   da suka gabata mun yi bayyani kan mahimancin kyakkyawan dabi'ar sada Zumunci a yau ma shirin namu zai ci gaba da wannan maudi'in saboda  mahimancinsa, amma kafin nan bari mu saurari tanadin da a kayi mana a kan faifai.

 

******************************Musuc*****************************

 

Masu saurare, shirin namu na yau zai fara da wasiyar muhamadiya wacce aka ruwaito cikin Littafin kafi na shahararen malamin nan sikatu islam kulaini yardar Allah ta tabbata a gareshi,Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya bayyana cewa:(na yi wasici ga Al'ummata wadanda suke gurin nan da wadanda ba sa nan,wadanda ke cikin tsatson mazaje da kuma mataye har zuwa ranar Alkiyama na su sada zumunci, ko da ya kasance cikin shekara so guda, domin hakan shine Addini).masu saurare, hakika dabi'antuwa da dabi'ar sada zumunci yana daga cikin hanyoyin da suke yi sanadin samun rabauta ranar Alkiyama, kamar yadda Ma'aikin Allah (S.a.w) ya bayyana mana a yayin da yake cewa:(hakika ranar Alkiyama Siradi ya kan yi sauki ga masu sada zumunci da masu cika Amana, idan gungun wadannan mutane  su fice sai shiga Aljanna, idan kuma mai cin Amana mai kuma yanke zumunci ya iso duk aiyukansa ba za su amfane shi ba a wannan lokaci sai ya fada cikin wuta). Har ila yau cikin Littafin kafi an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik(a.s) ya ce:(farkon abinda zai yi magana ranar Alkiyama daga cikin gabobin mutum, shini zumunci, sai ya ce Ya Ubangiji duk wanda ya sadani a Duniya ka sada shi a yau tsakaninka da shi, duk kuma wanda ya yankeni a Duniya ka yanke tsakaninka da shi a yau ).wannan a Lahira kenan, amma a nan Duniya , hakika nasossi da dama sun yi bayyani kan girman albarkatun dake tattare da mai dabi'ar zada zumunci, daga cikin su Karin yawan kwanuka ko kuma shekaru cikin Lafiya da alheri, shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:( hakika mutuman dake sada zumunci kuma babu abinda ya rake a shekarunsa face shekaru uku, Allah madaukakin sarki zai kara masa su, su zamanto shekaru 30 domin hakika Allah madaukakin sarki yana aikata abinda yake so, kuma da mutum zai kasance abinda ya rage cikin shekarun sa, shekaru 30 sai ya yanke shi watau zumunci ya fasa ziyartar kowa, Allah zai mayar masa da su, su koma shekaru uku , kuma hakika Allah madaukakin ya aikata abinda yake so).cikin wasiyarsa da sheikh Kulaini ya ruwaito cikin Littafinsa mai suna kafi, Shugaban mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya gwadaitar da masu Arziki sada zumunci ga makusantansu talakawa a cikin wani bangare na wannan wasiya Imam (a.s) ya ce:(duk wanda ya bayar da abin hanunsa cikin kyautata, Allah madaukakin sarki ya yi rantsuwa zai rubunya masa abinda ya bada a nan Duniya, ranar Lahira, babu dayanku da zai kasance mai girman kai da ji ji da kai cikin zatinsa da kuma ganin kansa ya fi kowa a cikin danginsa matukar dai  yana kauta cikin dukiyarsa, kada dayanku ya gafala ga masu bukata cikin makusantansa, kada ya gafala wajen tushe hanyar da ba za ta amfane shi ba,idan ya rike hannu,bay a bayarwwa  to kada ya cutu idan dukiyarsa ta hallaka) masu a nan wasiya Imam (a.s) ya na jan hankali ga masu kudin da suke rike hanunsu, alhali ga 'yan uwansa cikin talauci wanda hakan shi zai janyo hallakar dukiyar da rushewarta).

 

********************Musuc****************************

 

Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban zai yi bayyani kan dabi'ar sulhu ko sasantawa a tsakanin Mutane domin shima na daga cikin kyawawen dabi'un musulincin da Allah madaukakin sarki yake so ga bayinsa,Hakika Allah madaukakin sarki ya gwadaitar da bayinsa a kan su dabi'antu da wannan kyakkyawar dabi'a cikin ayoyi da dama na Alkur'ani mai girma, inda ya bayyana cewa yin hakan na kasancewa daga cikin hanyoyin samun yardarsa da kuma rabauta da Lada mai girma, a cikin Suratu Nisa'I Aya ta 114, Allah madaukakin sarki ya ce:(babu alheri ga yawancin ganawarsu sai dai (ganawar) wanda ya yi Umarni da sadaka ko kuma wani aiki na gari, ko kuma sulhu tsakanin Mutane, duk wanda ya aikata wannan don neman yardar Allah, to za mu ba shi lada mai girma), kuma hadisai sun bayyana cewa dabi'antuwa da dabi'ar kokarin yin sulhu tsakanin Mutane na daga cikin mafi fifikon aiyuka bayan tabbatar da tsaida farillai, kuma wannan shine abinda masoyinmu,mai shiryarwa zabebben Allah Annabi Muhamad (s,a.w) ya shiryar da mu, hakika shekh Tusy yardar Allah ta tabbata a gareshi cikin Littafinsa Al'amaly ya ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik shi kuma daga ma'aifansa daga Ma'aikin Allah (s.a.w) ya ce:(babu wani aiki da mutum da ya aikata mafi alheri bayan tsaida farillai, kamar sulhu tsakanin Mutane, ya fadi alheri, kuma ya wanzar da alheri), fadar ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka (ya fadi alheri, kuma ya wanzar da shi) ya na ishara ne kan matsayi da kuma  Albarkatun dake tattare da aikaka  aiki mai kyau na yin sulhu tsakanin mutane da hakan zai kasance ciro ne ga aiyukan alheri, ya kuma watsa soyayya da kauna a tsakanin Mutane.Masu saurare, kamar yadda kokarin sulhu tsakanin Mutane na daga cikin Sadakokin da Allah madaukakin sarki yake so, tasirinsa ya fi sadakar da dukiya ko abinci da mutum zai bayar, wannan shine abinda shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya yi ishara da shi cikin hadisin da Shekh Mufid yardar Allah ta tabbata a gareshi ya yi ishara da shi, inda ya ce Imam (a.s) ya ce:(Sadakar da Allah madaukakin sarki yake so, sulhu tsakanin Mutane idan sun samu rashin jituwa, a kusantar da su idan sun nisanta junansu).

 

Har ila yau Masu saurare, dabi'antuwar da wannan dabi'a ta sassanta Mutane na daga cikin alamar Imani kamar yadda Ayar farko ta cikin suratul Anfali ta yi ishara da hakan (saboda ku ji tsoron Allah , ku kuma gyara tsakaninku), kuma daga cikin misdakin samun ceton da Allah madaukakin sarki ya yi umarni da shi, kokari na nisantar  rarraba kawunan mutane, yin hakan shine abin da Allah madaukakin sarki ke fishi da shi, kamar yadda wannan Aya mai albarka ta bayyana a cikin suratu Nisa'I Aya ta 85 Allah madaukakin sarki ya ce :(wanda ya yi ceto(tsakanin mutane)ceto na gari, to zai samu rabonsa daga gare shi(ladan ceton).wanda kuwa ya yi ceto(tsakanin mutane) ceto mumuna (watau bata tsakaninsu), to zai samu rabonsa(na zunubi) wannan aiki.Allah kuwa Ya kasance Mai iko ne a bisa komai). Masu saurare wannan ceto da kuma kokari wajen sulhu tsakanin mutane na daga cikin mafi fifikon misdakin Sadaka, a cikin Littafin Idatu Da'I an ruwaito hadisi daga ma'aikin Allah (s.a.w) ya ce:(mafi fifikon sadaka ita ce sadakar harshe. Sai aka ce ya Ma'aikin Allah wacecce sadakar harke? Sai ya ce ita ce ceton da ya kasance aniywa wanda ke cikin kanki aka fitar da shi ,kuma ta kasance garkuwa na zubar da jinni,ta kuma janyo kyautatawa ga Dan uwanka, sannan kuma ta kasance garkuwa ga duk wani abin ki) watau ana nufin abin ki a nan, kiyayya da kuma yanke alaka tsakanin Mutane.da fatan Allah madaukakin sarki ya yi mana Karin taufiki domin dabi'antuwa da kyawawen dabi'u tare kuma da kokari da ceton da aka yaba da shi na sulhu tsakanin mutane domin shi Allah mai ji kuma mai karbar Addu'a ne.

 

*****************************Musuc******************************

 

Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku nag aba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.