May 21, 2016 02:24 UTC

Shirin na Yau zai yi bayyani kan mahimancin kamewa daga roko ko kuma tambayar mutane tare da yin tawajihi ko kuma meka wuya ga Allah madaukakin sarki wajen neman bukata da kuma yawaita yin Addu'a a gare shi, domin yin hakan na daga cikin kyawawen dabi'un musulinci da Allah madaukakin sarki ke so ga bayinsa

Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,Shirin na Yau zai yi bayyani kan mahimancin kamewa daga roko ko kuma tambayar mutane tare da yin tawajihi ko kuma meka wuya ga Allah madaukakin sarki wajen neman bukata da kuma yawaita yin Addu'a a gare shi, domin yin hakan na daga cikin kyawawen dabi'un musulinci da Allah madaukakin sarki ke so ga bayinsa, kafin mu shiga cikin shirin ga wannan.
******************************Musuc*****************************
Masu saurare cikin Littfin Allah mai tsarki Aya ta 273 cikin suratu Bakara, Allah madaukakin sarki y ace:((ku fifita ciyarwar)ga fakirai wadanda suke tsare kansu saboda Allah, ba sa iya yawatawa cikin kasa (don neman abinci har) wanda bai sani ba rika tsammanin su mawadata ne don kamewarsu, ba sa naciya wajen rokon mutane. Abin da kuke ciyar na Alheri, hakika Allah yana sane da shi) Allama Tabrasi cikin Majma'ul bayan ya ruwaito wani hadisi  inda a cikinsa aka bayyana cewa:(hakika Allah ya na son ganin tasirin ni'imarsa ga bawansa, ya na kuma kin murtsike fuska da bacin rai (wato ba a so aga mutun kulun cikin bacin rai da murcike fuska babu walwala ko kadan a tare da shi)kuma ya na son mai hakuri mai kuma kamun kai daga cikin bayinsa, yana kuma fishi da fasiki mai aikata alfahasha, mai yawan tambaya). Masoyin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a garshi tare da iylan gidansa tsarkaka ya bayyana cewa hakika Allah madaukakin sarki ya ki ga bayinsa da su roki mutane sai kuma ya so hakan ga kansa wato Allah ya na son bayinsa su tambaye shi kadai domin girmama a gare su.a cikin Littafin Kafi an ruwaito hadisi daga ma'aikin (s.a.w) ya ce:(Hakika Allah tabarka wa ta'ala ya sowa kansa wani abu sannan ya kisa ga  bayinsa,ya kiyewa bayinsa tambaya (wato duk yadda bawa yake za ka ka yana kin mai yawan tambaya), kuma Allah ya ce babu abinda ya fi so kamar bawansa ya tambayesa kada dayanku ya ji kumya wajen tambayar Allah wani abu daga falalarsa) masu saurare kamun kai wajen tambayar mutane shine bayyanar izzar mumuni  wajen Allah madaukakin sarki kamar yadda shugabanmu Imam Sadik(a.s) ya yi ishara cikin hadisin da aka ruwaito cikin Littafin kafi, inda yake cewa(Hattara da rokon Mutane domin yin hakan kaskanci ne a Duniya da kuma kirar talauci kuma hakan na janyo dogon hisabi a ranar Kiyama). Har ila yau cikin littafin Kafi, an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Bakir (a.s) ya ce:(Da Mutane sun san abinda ke cikin roko da bas u roki kowa ba, kuma da mai bayarwa ya san abinda ke cikin bayarwar da bai hanawa duk wanda ya tambaye shi ba), Allah tabarka wata'ala ya na son mumunin da zai dabi'antu da dabi'un Allah madaukakin sarki sai ya kasance hanunsa ne a sama har kulun, wato ya kasance daga cikin masu bayarwa da kuma cikin masu kokari wajen biyan bukatun Mutane ba mai roko mai yawan tambaya ba.a cikin Littafin Kafi, an ruwaito hadisi daga masoyin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(hannu ko kuma kudura kasha uku ne, kudurar Allah madaukakin sarki wacce ita ce sama da komai, sai kuma mai binta wato hanun mai bayarwa sai kuma hanun mai karba  da shi ne karshen kasa, ku rage roko daidai kwalkwado) sannan ma'aikin Allah sai ya bayyana cewa kamun kai kunyar mumuni ne wacce Allah madaukakin sarki ke so, a yayin da roko ya zmanto cin mutunci ga kunya kuma shi ba ya wadatar da komai ga mai yinsa domin arzikin da Allah madaukakin sarki ya kaddara masa zai same shi ta ko wani hali. Ma'aikin Allah (s.a.w) ya ce:(ku saurara!Arziki na lullube da hijabi, duk wanda yake so ya kiyayye kunyarsa sai ya dauki arzikinsa, wato ya kiyaye rokon mutane sai arzikinsa ya same a cikin ko wani hali, kuma duk wanda yake so ya ci mutuncin hijabin wato hijabin kunya wajen rokon mutane ya kuma dauki arzikinsa).sannan kuma tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi da iyalan tsarkaka yayi kira da riko da mafi fifikon kamun kai daga rokon mutane ko da kuwa Bawa ya shiga cikin mawuyacin hali ya yi tawakuli da Allah tabarka wa ta'ala.inda ya ce (Na rantse da wanda raina ke hanunsa, da dayanku zai dauki ikiya ya cikin cikin daji ya tara itace ya shiga kasuwa da su ya sayar da mudu guda na dabino ya dauki kashi daya daga cikin uku ya yi sadaka da sauren ya fiye masa tambayar mutane su bashi ko kuma su hana shi).
*************************Musuc************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai yi bayyani ne kan mahimancin yiwa juna kauta saboda tana farfado da soyayya tsakanin mutne sannan tana sanya soyayya cikin zukata tana kuma kore kumshin zuciya, a cikin Littafin kafi an ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce (ka kasance masu wa junanku kauta sai soyayar dake tsakaninku ta karu, yiwa juna kauta na kore kumcin zukata), an samo hadisi daga shugaban mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya ce:(kautar da zan yiwa Dan uwa na musulmi ta amfane shi ta fiye min abin so ga sadakar da zan yi da makamancinta). Imam Sadik (a.s) ya ce:(daga cikin girmamawar mutum ga Dan uwansa musulmi shine idan ya yi masa kauta to ya amince da ita) hakika masu saurare kauta komin kankantarta nada tasiri sosai wajen karfafa zaman Al'umma da kuma sanya soyayya da alaka mai karfi, Ma'aikin Allah (s.a.w) ya ce:(kuyi wa junaku kauta koda da dan itaciyar Sadir ne domin ita kauta tana raya soyayya da kauna), Imam Bakir (a.s) ya ce:(Ma'aikin Allah (s.a.w) yana karbar kauta amma ba ya karbar sadaka kuma yana cewa kuyiwa junaku kauta domin ita tana kore kumcin kiyayya da hasada). Masu saurare daga cikin misdakin ihklasi ga Allah maduakakin sarki,bayar da kauta ga wanda bai taba baka kautar komai ba, kuma kada ka yi kwadayin nan gaba zai mayar maka da wani abu sakamakon kautar da kayi masa, a cikin Littafin Man La Yahduruhul fakih, an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Ali Murtadha (a.s) ya ce:(ka ziyarci wanda ba ya ziyartarka, ka kuma bayar da kauta ga wanda baya yi maka kauta). Mafi kuma fiyeyyar kauta wacce aka yita saboda Allah, an ruwaito hadisi cikin Littafin Alkhisal daga Ma'aikin Allah (s.a.w) ya ce:(kauta nada fuskoki guda uku ta farko kautar da aka bayar domin kariya, sai kuma kautar da  a kayi domin kare wani shari, sai kuma kautar da aka bayar saboda Allah madaukakin sarki) kamar yadda dabi'antuwa da wannan kyakkyawar dabi'a ta kan zamanto sanadiyar saukar Albarkatun samai kuma sabanin haka zan zamanto sanadiyar saukar bala'I kamar fari da saurensu, wannan shine abinda hadisin da aka ruwaito cikin Littafin Uyunul Akhbarurridha ya yi ishara da su.Imam (a.s) ya ruwaito hadisin ne daga iyayensa daga ma'aikin Allah (s.a.w) ya ce:(Al'umma ta ba za ta kushe ba cikin Alkheri matukar ta kasance cikin son juna, baiwa juna kauta, rikon Amana, ku nisanci aikata haramun kuma ku kirmama baki,ku tseda salla ku kuma bada zakka, idan suka ki aikata yin hakan za su jarabu da karamcin ruwa gami da fari).
*******************************Musuc*************************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku nag aba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.