Tunani tare da daukan Darusa dangane da abinda ya wakana
Shirin na Yau zai yi bayyanni kan mahimancin tunani tare da daukan Darusa dangane da abinda ya wakana
Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,Shirin na Yau zai yi bayyanni kan mahimancin tunani tare da daukan Darusa dangane da abinda ya wakana, abin nufi ya Kasance tunani mai kyau abinda ko wani Dan Adam zai sanya gaba domin yay i kokari wajen anfanuwa da da tarbiya a aikace kan abinda ya Ji ya kuma gani, baya ga hakan ya bada himma wajen yin tunani ga abubuwan da suka gyrara zuciyarsa , ya rika sauraren wa’azin da zai dinga sanya shi kyawawen aiyuka da kuma Nisantar aiyuka munana. Amma kafin mu shiga cikin shirin ga wannan.
****************************Musuc*******************************
Masu saurare, Hakika Ayoyi da dama kai tsaye ko kuma ta hanunka mai sanda sun Umarce mu da yin tunani mai kyau, a shirin na za mu takaita da wadannan Ayoyi masu albarka wato Aya ta 190 da kuma ta 191 cikin suratu Ali Imaran inda Allah madaukakin sarki yake siffanta Bayinsa Salihai yana mai cewa:(Hakika a cikin Halittar Sammai da Kassai da sabawar Dare da Rana, lallai a kwai Ayoyi ga ma’abota Hankula.*(Su ne) wadanda suke Ambaton Allah a tsaye da kuma a kishingide,suke kuma tunani a kan halittar sammai da Kassai (suna cewa) Ya Ubangijinmu, ba ka halicci wannan a banza ba, tsarki ya tabbata a gare ka, ka tserar da mu azabar wuta), Hadisai da dama sun bayyana cewa duk tunanin da yake tare da daukan darasi yana da tasiri mai girma a wajen tsarkake zukata baya ga haka mafi girman abinda Bawa sai samu shine ladan Ibada,misali a cikin Littafin Almahasin An ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) daga Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:( tunani na Aya guda ya fi tashin Dare wato ya fi mutune ya kwashe tsahon Dare yana salla, sai aka tambaye shi yaya zai yi tunanin? Ya dinga yin tunanin gidajen da suka rushe ko kuma suka Lalashe yana tambayar kansa ina wadanda suka zauna a cikinsa, ina kuma wadanda suka ginaku? Minene ya sanya ba kwa Magana ne).Masu saurare idan wannan tunani shi zai sanya Bawa ya dinga tunawa da mahalinsa kuma ya gyara zamansa ta yadda zai kara azama wajen ci gaba da kyawawen aiyuka da kuma nisantar munana,A cikin Littafin Amaly, shekh Saduk yardar Allah ta tabbata a gareshi ya ruwaito hadisi, inda a cikin sa aka bayyana cewa Haruna Abas ya rubuta wasika zuwa ga Imam Abil Hasan Musa bn Ja’afar (a.s) ka yi mini dan takaiceccen wa’azi ko kuma Nasiha a takaice, sai Imam (a.s) ya amsa masa da cewa:(babu abinda idanuwanka za su gwada maka face a mau’iza a cikinsa), kamar yadda wasu hadisan suka bayyana cewa wannan dabi’a mai kyau na daga cikin hanyoyin da suke kiyaye rayuwar zukata a aikace.A cikin Littafin Kafi shekh Kulaini ya ruwaito Hadisi daga Shugabanmu Imam Sadik(a.s) y ace:(Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib(a.s) ya kasance yana cewa Ka dinka tunatar da zuciyarsa wajen yawaita yin tunani ka kuma kebe wani bangare na dare domin yin ibada kuma ka ji tsoron Allah mahalicinka) domin haka tunani shine mafi fifikon misdaki na Ibada, a cikin Littafin Kafi, an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Ridha (a.s) ya ce:(Yawan Azumi da Salla bas hi ne Ibada, tunani cikin Al’amuran Allah madaukakin sarki shine Ibada). Har ila yau cikin Littafin na Kafi an ruwaito hadisi daga Imam Sadik (a.s) y ace:(fifiko ibada Dawwama cikin yin tunani ga Allah da kuma kudurarsa) har ila Yau Imam (a.s) y ace:(yin tunani yana kai Bawa ga yin biyayya da kuma aiki da ita) Imam (a.s) ya ce:(ya kasance mafi yawan Ibadar Abi Zar yin tunani da kuma daukan darusa).
****************************Musuc***************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai yi bayyani ne kan mahimancin Kishi,amma ba mumunan kishi irin na wasu Mata ba da yake kaisu da hallaka,kishin da ake nufi wanda zai sanya mutum cikin halin da zai kare duk abinda zai cutar da huruminsa kama daga Addini zuwa ga iyalinsa.wannan dabi’a na daga cikin kyawawen dabi’un Allah madaukakin sarki da kuma Annabawa ma’asumai kamar yadda Annabi Muhamad (S.A.W) ya bayyana cikin hadisin da aka ruwaito cikin Tafsirin Al-Ayyashi inda yake cewa:(babu wani da ya fi Allah madaukakin sarki kishi, kuma wanene wanda ya fi kishi ga wanda ya haramta Al-fahasha wacce ta bayyana da ma wacce ta buya) domin haka ne ma wannan dabi’a ta kan kasancewa sanadiya ga Bawa ya rabauta da soyayyar Ubangiji, a cikin Littafin Kafi an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:(Hakika Allah Tabaraka wa ta’ala Mai kishi ne ya na son duk wani mai kishi saboda Kishinsa ya haramta Alfahsha wacce ta bayyana daga ciki da ma wacce take boye).Masu saurare, dabi’antuwa da wannan dabi’a mai girma na daga cikin hanyoyin rabauta da karfafa ruhin Imani cikin zukata da kuma tsarkaka daga Nifaki ko kuma munafici, kamar yadda Hadisin Nabawi da aka ruwaito cikin Littafin (Al’imama wal Tabsira) inda a cikinta Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(Kishi daga Imani ne, mumunar Magana ko Alfahsha na daga cikin alamar nifaki ko kuma munafici), A cikin Littafin Alkhisal, an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka inda aka zo masa da wani adadi daga cikin mushirikai da ya wajabta a kashe su, sai yayi afuwa ga daya daga cikinsu, sai wanda aka yiwa Afuwar ya tambayeshi sanadiyar da ya sanya yayi masa Afuwa, sai Ma’aikin Allah (S.A.W) ya ce hakika kanada wasu siffofi guda biyar da Allah madaukakin sarki da kuma ma’aikinsa suke so, na farko tsananin kishi a kan muharaminka, na biyu kyauta da kuma Karamci, na uku kyawawen halaye, na hudu, gaskiyar harshe, wato mai gaskiya ne duk abinda harshensa ko bakinsa zai fada gaskiya ne, na biyar kuma Jarumtaka, wato shi Jarimi ne) bayan da wannan Mutum ya ji haka sai ya musulinta ya kuma kyautata musulinta ya yi yake tare da Manzon Allah har ya yi shahada).
Masu saurare, daga Albarkatun dabi’antuwa da wannan dabi’a rabauta da soyayar waliyan Allah masu gaskiya,Hakika cikin Littafin Kafi an ruwaito Hadisi daga Shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:( Mu muna son wanda ya kasance mai hankali, mai ganewa,masanin hukuncin Addini, mai hakuri,mai siyasa a mu’amalarsa da Mutane, mai gaskiya da kuma cika alkawari, Hakika Allah madaukakin sarki ya kebantar da Annabawansa da kyawawen dabi’u, duk wanda ya samu kansa da shi sai ya godewa Allah bisa wannan kauta da ya bashi, wanda kuma bashi da su ya gaggauta komawa ga Allah ya roke sa da su, sai Rawin wato wanda ya ruwaito hadisin ya tambayi Imam Sadik (a.s) wane ne wadannan dabi’u? sai Imam (a.s) ya ce masa sune Tsoron Allah,dangana, Hakuri, godiya, kunya, Karamci, kishi, biyayya, gaskiyar Magana,tsananin hakuri, da kuma rikon Amana).
*******************************Musuc*************************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku nag aba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.