Kishin Da Musulinci Ya Amince Da Shi
A shirin da ya gabata mun yi bayyani kan mahimancin kishin da musulinci ya amince tare kuma da yin umarni da shi ganin mahimancin wannan maudu’I , a yau ma shirin zai dora daga inda muka tsaya a shirin da ya gabata
Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,A shirin da ya gabata mun yi bayyani kan mahimancin kishin da musulinci ya amince tare kuma da yin umarni da shi,ganin mahimancin wannan maudu’I , a yau ma shirin zai dora daga inda muka tsaya a shirin da ya gabata, amma kafin nan ga wannan.
******************************Musuc****************************
Masu saurare,ma’anar wannan kyakkyawar dabi’ar shine ya kasance Mutum ya mallaki wani hali da zai sanya shi ya canza domin tunkarar ko wata irin cutarwa ko cin zarafin ga huruminsa, daga cikin misdakin wannan yanayi, kishin iyalai, nisantar Alfahsha wacce ta bayyana da ta boye, hakan kuma shi ke sanya wa mutum ya dabi’antu da dabi’un Allah kyawawa, kamar yadda Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ke fadakar da mu cikin hadisin da aka ruwaito a Littafin Amali na shekh Saduk , cikin daya cikin Khudubobinsa Ma'aikin Allah (s.a.w) ya ce:(ku saurara! Hakika Allah madaukakin sarki ya haramta abinda yake haramun kuma ya shata iyakarsa, babu wani da ya fi Allah kishi, daga cikin kishinsa ya haramta Alfahsha ya kuma yi hani ga ko wani Dan Adam ya keta hurumin makobcinsa). Masu saurare, ba shakka wannan dabi’a ta kishi na daga cikin kyawawen dabi’un Annabawa (a.s) da ya kamata mu dabi’antu da su, sabanin hakan ya kan janyo fishin Ubangiji, A cikin Littafin Kafi an ruwaito Hadisi daga Ma’aikin Allah (S.a.w) ya ce:(Babana Annabi Ibrahim (a.s) ya kasance mai kishi, ni kuma na fishi kishi, Allah ka yanke hancin wanda ba shi da kishi daga cikin Al’ummata), dabi’antuwa da wannan kyakkyawar dabi’a nada lada makamancin na jihadi saboda Allah, a cikin Littafin Nawadir na Sayyid Kutubudin Rawandi an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah (s.a.w) ya ce:(An wajabta Jihadi a kan Mazaje daga cikin Al’ummata sannan kuma aka baiwa Mata zafin kishi, duk wanda ya yi hakuri daga cikinsu ,Allah zai bashi Ladan Shahidi), hakika cikin hanyoyin samar da hadisi na bangaren sunna da shi’a an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah (s.a.w) ya ce duk wanda aka kashe ba tare da haki ba shahidi ne).daga cikin misdakin kishi , kada Mutum ya dinka kasancewa da matan da ba muharamnsa ba , hakan kuma ya sabawa dabi’ar kishi, a cikin Littafin Biharu-Anwar an ruwaito Hadisi daga Ibn Abas ya ce:( Annabi Musa (a.s) ya kasance Namiji ne mai kishi ba ya tafiya da Mata saboda iyalinsa kadda ta gansa) har ila Yau masu saurare daga cikin misdakin Kishin da ake so kuma aka yaba da shi kokarin mutum wajen wadatar da bukatun iyalansa ta yadda ba za su yi kwadayin na waje ba, kuma wannan shine abinda masoyinmu Mustapa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya shiryar da mu, cikin wani hadisi da aka ruwaito a Littafin Kafi inda ya ce:(Shin ku na so in ba ku labarin mafi alkheri daga mazajanku!mafi Alkheri daga cikin mazajenku shine mai tsoron Allah, tsarkakekke, mai karamci ga iyalansa wanda ba ya hana iyalansa da kuma mutane ,arzikin da Allah madaukakin sarki ya hore masa). Dangane da wannan ma’ana shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya kwadaitar da mu wajen mu dabi’antu da wannan kyakkyawar dabi’a, cikin wani hadisi da aka ruwaito a littafin Safinatul Bihar, Imam (a.s) ya ce:(Hakika ko wani mutum a cikin gidansa da kuma Iyalansa a kwai bukatar ya dauki nauyin ababe guda uku ko da kuwa bai kasance daga cikin masu babban matsayi na rayuwa , na farko kyakkyawar mu’amala tare da iyalansa, na biyu ya wadatar da su daidai gwalgwado, na uku kyakkyawan kishi da zai kare martabarsa da na iyalansa) da fatan masu saurare mu samu Karin taufiki na dabi’antuwa da kyawawen dabi’un da Allah madaukakin sarki da Manzon sa ke so.
**************************Musuc********************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai yi bayyani dangane da dabi’ar Jarumtaka domin shi ma na daga cikin kyawawen dabi’un musulinci. ma’anar Jarumtaka shine Mutane ya dauki hakin sa duk da irin barazanar da zai fuskanta, wannan kuma shi ne abinda Ayoyi na 172 zuwa ta 174 cikin suratu Ali Imrana suka yi ishara da albarkatunsa da kuma kyakkyawan makomarsa,inda Allah madaukakin sarki ya ce:( Wadanda suka amsa wa (kiran) Allah da Manzonsa(wajen fita yaki) bayan miki ya same su (a yankin Uhudu) to wadanda suka kautata a cikinsu suka ji tsoron(Allah) suna da Lada mai girma*(Su ne) wadanda wasu mutane suka ce da su: Hakika mutanen (Makka) sun tara muku (runduna), sai ku tsorace su. Sai wannan ya kara musu imani, suka kuma ce “Allah ya ishe mu, kuma madalla da madogara* Sai suka komo da ni’ima daga Allah da falala, ba wani mugun abu da ya same su, suka kuma bi yardar Allah. Allah kuwa Ma’abucin falala ne mai girma) Masu saurare abinda za mu fahimta cikin wadannan Ayoyi masu albarka, dabi’antuwa da dabi’ar Jaruntakar imani na daga cikin alamar gaskanta dogaro da Allah madaukakin sarki, ma’ana karfafa ruhi a kan dogaro da Allah tabaraka wa ta’ala shi ke sanya mutum ya dabi’antu da dabi’ar Jaruntaka, hakan kuwa shi ne abinda Hadisin Imam Sadik (a.s) wanda aka ruwaito cikin Littafin Kafi na sikatul Islam Kulaini ya shiryar da mu,Abi Basir ya ruwaito hadisi daga Imam Sadik (a.s) ya ce:(babu wani Abu face ya nada Haddi ko iyaka? Abu Basir Yace: raina fansarka minene hadi ko iyakar tawakuli ko kuma dogaro ga Allah?sai Imam (a.s) ya ce masa Yakini ko kuma tabbaci sai Abu Basir ya ce minene iyakar tabbaci sai Imam (a.s) ya ce masa shine kada ka hada tsoron Allah tare da komai), Masu saurare daga cikin mahimin tabbatar da Jarumtaka shi ne fadar gaskiya ko da ta kasance a kanka kuma hakan na daga cikin tabbacin kyawawen dabi’u, hakika Shekh Saduk cikin Littafinsa na Ma’anil Akhbar ya ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik(a.s) inda a cikinsa aka ce wani Mutum ya cewa Imam Sadik (a.s) Ya Dan Ma’aikin Allah ba ni labarin kyawawen dabi’u sai Imam ya ce yin Afuwa ga wanda ya zalunceka, sada zumunci ga wanda ya yanke ziyartarka, ka baiwa wanda ya hanaka, fadar gaskiya ko da ta kasance a kanka), kamar yadda daga cikin misdakin Jarumtaka ,kamewa da kuma juriya a yayin da rai dake kokarin karkata zuwa ga bata
da kuma lokacin da zuciya ke wasi-wasi wajen aikata sabon Allah tare kuma da tilastawa kai wajen bin gaskiya, a cikin Littafin Ma’anil Akhbar an ruwaito hadisi daga shugaban mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya ce:(wanda ya fi kowa Jarumtaka daga cikin mutane, wanda ya yi galaba a kan son ransa), har ila yau cikin Littafin Guraru hikam, an ruwaito hadisi daga Imam Ali(a.s) ya ce:(mafi jarumtaka daga cikin Mutane, wanda ya yi galaba a kan Jahilci ta hanyar hakuri).daga cikin kyakyawan sakamako na dabi’ar Jarumtaka, kishi irin na Imani kamar yadda Imam(a.s) ya bayyana (kyakkyawan sakamakon Jarumta kishin Imani) har ila yau a wata riwayar ya ce:(Jarumta Ado ce, tsoro kuma Aibi ne)
*******************************Musuc*************************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku nag aba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.