Magance matsalar bayin Allah ta hayar basu abinda suke bukata
Shirin na yau zai yi bayyani kan magance matsalar bayin Allah ta hayar basu abinda suke bukata
Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,Shirin na yau zai yi bayyani kan magance matsalar bayin Allah ta hayar basu abinda suke bukata, domin hakan na daga cikin kyawawen dabi’un musulinci , kafin mu shiga cikin shirin ga wannan.
**************************Musuc*************************
Masu saurare dabi’ar Bayarwa na daga cikin kyawawen dabi’un Iyalan gidan Annabin Rahama amincin Allah ya tabbata a garesu, da Alkur’ani mai girma ya Ambato cikin suratu Insani yayin da yake godiya a gare su, kuma hakan na ishara kan cika alkawarin da suka yi na bakance bayan samun Lafiyar Hasanaini, Hakika cikin suratu Insani daga Aya ta 7 zuwa ta 9 Allah madaukakin sarki ya bayyana cewa:(Suna shukawa da alkashin da suka dauka na Bakance suna kuma tsoron wani yini wanda sharinsa ya kasance mai tartsatsi ne* Suna kuma ciyar da abinci tare da suna son sa, ga miskini da maraya da kuma ribatacce a yaki*(Suna cewa) Mu Kawai muna ciyar da ku ne saboda Allah, ba ma nufin sakamako ko godiya daga Wurinku), wadannan Ayoyi masu albarka sun yi ishara da mahiman abubuwa kamar kamar haka: suka ce ba sa bukatar sakamako ko godiya daga wajen Mutane kuma su sun bayar ne saboda Allah madaukakin sarki wanda hakan ke nuna karfin ikhlasinsu cikin aiyukansu kuma a bangare guda yin hakan shi ke samar da aminci daga fargaba da kuma yanayin ranar Alkiyama.
A cikin Tafsiru Mizan na Allama tabatabba’I yardar Allah ta tabbata a gare shi kalakshin tafsirin wannan Aya ya ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Ja’afaru Sadik (a.s) ya ce:(ma’anar wannan bangare na Ayar (Suna kuma ciyar da abinci tare da suna son sa) sun ciyar da abinci a yayin da suke tsananin bukatarsa suka sadokar da kai saboda miskini daga cikin miskinan musulmai, da maraya musulmai, da kuma daya daga cikin fursunan yaki , a yayin da suka ciyar da su, suka ce: (Mu Kawai muna ciyar da ku ne saboda Allah, ba ma nufin sakamako ko godiya daga Wurinku) Imam (a.s) ya ce Na rantse da Allah ba su fada musu haka a bayyane ba, sun yi wannan firici ne a zukantansu suna masu cewa ba ma bukatar wani abu da za ku saka mana da shi, ko kuma ku gode mana saidai mun ciyar da ku ne saboda Allah da kuma neman ladansa). wannan riwaya na ishara da cewa rashin neman taimako daga wajen mutane ba shi ke nuna cewa rashin bayyana halin da marassa ji ke yi ba , don haka abinda mumuni ya kamata ya yi matukar ya fahimci wanda yake cikin bukata to ya taimaka ma shi ba sai ya jira mabukacin nan ya meka hanunsa gare shi ba,domin abinda wanda Aya ta Ambato bayyanin harshensu amincin Allah ya tabbata a garesu, ba abin da suka fada ba kamar yadda wannan hadisi ya bayyana.kuma manufar Ambato halin harshensu, shi ne kodaitar da mumunai wajen dabi’antuwa da wannan kyakkyawar dabi’a, da kuma fadakar da su kan abinda ya kamata su yi na cewa kautar su ta kasance domin neman yardar Allah madaukakin sarki ba wai neman sakamako ko godiya ba. A bangare guda wasu hadisan sun bayyana cewa dabi’antuwa da wadannan kyawawen dabi’u ado ne ga mumuni, cikin Littafin Al-amaly na shekh Saduk an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Ja’afaru Sadik (a.s) yayin da daya daga cikin sahabansa ya tambayeshi wasu halaye ne suka fi kyau ga Mutum, sai ya ce:(kyakkyawar niya ba tare da fargaba ba, bayarwa ba tare da nemem sakamako ba, rashin shagaltuwa da jin dadin duniya).
**************************Musuc*****************************
Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai yi bayyani ne kan dabi’ar tausayi da kuma jin kai ga masu rauni gami da yi musu adalci domin hakan na daga cikin kyawawen dabi’un da Allah da Manzon ke so.Hakika Nassosi da dama na musulinci sun kwadaitar da mu da mu dabi’antu da wadannan kyawawen dabi’u. da farko za mu fara da Aya ta 36 cikin suratu Nisa’I, inda Allah madaukakin sarki ya ce:(Kuma ku bauta wa Allah kada ku tara komai da shi, kuma (ku kula) da kyautata wa ma’aifa, da dangi, da Marayu, da miskinai, da makobci na kusa, da makoci na nesa,da abokin tafiya, da matafiyi, da abin da hannayenku suka mallaka, (watau bayi).Hakika Allah ba ya son wanda ya zamanto mai takama mai fariya).abin fahimta a wannan Aya mai albarka shi ne taimako da kuma jin kan mai rauni ya kan yi sanadiyar tsiratar da Mutum fadawa cikin mumunar dabi’a ta alfahari, jiji da kai da kuma girman kai domin wadannan siffofi ne na makiya Allah, da fatan Allah ya tsare mu da su.
Masu saurare, daga cikin albarkatun dake tattare da wannan hali mai kyau, shine samun rabauta da rahamar Ubangiji.a cikin Littafin Al-amaly na shekh saduk an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Ja’afaru Sadik(a.s) ya ce:(duk wanda yake so Allah madaukakin sarki ya sanya shi cikin rahamarsa da kuma Aljannarsa, to ya kyautata dabi’unsa da kuma bayar da rabin ransa, ya jin kan marayya,ya taimakawa mai rauni kuma ya kaskantar da kai ga Allah da ya hallice shi) kamar yadda dabi’antuwa da dabi’ar tausayin masu rauni da kuma nisantar wulakantar su ko kuma zalintar su na daga cikin hanyoyin samun rabauta da mafi martaba na samun kusanci ga Ubangiji, a cikin Littafin Amaly na Shekh Saduk an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:(Masu irin wadannan halaye Uku daga cikin Bayi, sune suka fi kusanci ga Allah madaukakin sarki ranar Alkiyama har lokacin da za a kare Hisabi, Mutuman da bai yi amfani da karfinsa a yayin da yake cikin fishi ya cutar da wanda yake kasa da shi, Mutuman da yake tafiya tare da mutane guda biyu , bai karkata ga dayansu ba daidai iyawarsa, mutuman da yake fadar gaskiya ko da ta kama a karan kansa). Har ila yau masu saurare, dabi’antuwa da wannan dabi’a mai girma na daga cikin hakikanin Imani, ma’ana daga cikin alamomin Imani shine fadar gaskiya da sanya ta a cikin zukatan Mutane, wannan shine abinda shugabanmu Mai shiryarwa kuma zabebben Allah ya shiryar da mu cikin wasiyar da yayiwa Imam Aliyu bn Abi Talib Murtada (a.s), a cikin Littafi Khisal an ruwaito hadisi daga Ma’aikin Allah(s.a.w) ya ce:(Ya Ali Shugabanin Aiyuka guda uku ne.Adalcinka ga mutane daga kanka, rashin gwada banbanci cikin ‘yan uwanka saboda Allah madaukakin sarki, da kuma ambatonka ga Allah tabaraka wa ta’ala a ko wani hali,Ya Ali!uku na cikin hakikanin Imani, bayarwa ga fakirai, Adalcinka ga mutane daga kanka, da kuma watsa ilimi ga masu neman ilimin) da fatan Allah madaukakin sarki ya arzuta mu da irin wadannan kyawawen dabi’u domin karama da kuma girman Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka.
*******************************Musuc*************************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.