Dabi'ar Gaskiya
Shirin na Yau zai yi bayyanni kan dabi'ar gaskiya a fadar baki ko kuma a aikace, kazalika ya kamata aiyukan mutum su yi daidai da akidarsa da kuma fadarsa
Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,Shirin na Yau zai yi bayyanni kan dabi'ar gaskiya a fadar baki ko kuma a aikace, kazalika ya kamata aiyukan mutum su yi daidai da akidarsa da kuma fadarsa, amma kafi mu shirin ba ri mu saurari wannan.
*************************Musuc*****************************
Masu hakika, dabi'ar gaskiya na daga cikin alamomin Imami, kuma ta haka ne ake gane Mumuni na gaskiya, kamar yadda shugabanmu Annabi Muhamadou (s.a.w) ya shiryar da mu, a hadisin da aka ruwaito cikin littafin Uyunul Akhbaru Ridha (a.s) yayin da yake bayyani kan sanin masu kiran kansu masu Imani, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(kadda ku dibi yawan sallarsu , azumunsu ko kuma yawan hajjinsu, amma ku dubi gaskiyar maganarsu da kuma cika amanarsu) har ila Yau wannan dabi'a ta gaskiya wasila ce ta samun rabauta a Duniya da Lahira kamar yadda shugaban Muwahidai kuma shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya bayyana cewa:(ku riki gaskiya domin ita ce ke ceton mutum) wannan hadisi an ruwaito shi ne cikin littafin Khisal yayin da yake ishara ga wannan Aya ta 119 cikin suratu Ma'ida inda Allah madaukakin sarki ke cewa:(Wannan ita ce ranar da Masu gaskiya Gaskiyarsu za ta amfane su,suna kuma da aljannoni wadanda koramu suke gudana ta karkashinsu suna madawwama a cikinsu har abada. Allah ya yarda da su,su kuma sun yarda da shi.wannan shi ne babban rabo) a cikin Littafin Kafi an ruwaito wani hadisi mai tasirin gaske da yake bayyani kan girman albarkar dake tattare da dabi'ar gaskiya, Abdull...bn Ya'afur ya aikewa Imam Sadik (a.s) sakon gaskuwa, sai Imam (a.s) ya cewa Dan aiken ( Aminci ya tabbata a gareka da kuma gare shi idan ka koma wajen Abbdall.. ka meka gaisuwa ta gare shi kuma ka ce masa Ja'afar bn Muhamad ya ce masa ya dubi girman matsayin da Aliyu bn Abi Talib(a.s) ya kai a wajen Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iylan gidansa tsarkaka ya yi riko da shi, Hakika Aliyu bn Abi Talib(a.s) ya samu matsayin da wani bai same shi a wajen Ma'aikin Allah (s.a.w) saboda gaskiyar maganarsa da kuma rikon amanarsa), Masu saurare wannan hadisi ya yi ishara da cimma babban matsayi na kamala ta hanyar dabi'antuwa da wadannan kyawawen dabi'u guda biyu, wato gaskiya da kuma rikon Amana,kuma ba shaka wadannan dabi'u na daga cikin fitattun dabi'un Annabta kamar yadda hadisin Imam Sadik (a.s) da aka ruwaito cikin Littafin Kafi ya yi ishara da hakan(Hakika Allah madaukakin sarki bai tayar da wani Annabi ba face sai don gaskiyar Magana da kuma rikon Amana zuwa ga mai biyayya da fajiri).A cikin wani hadisin na daban da aka ruwaito cikin Littafin Kafi, Shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya sanar cewa daga cikin tausayin Allah madaukakin sarki ga bayinsa ya sanya dabi'antuwa da dabi'ar gaskiya sanadin rabauta da shiriyarsa na tsarkakakkun aiyuka, Imam (a.s) ya ce:(duk wanda ya kasance mai gaskiyar zance, aikinsa ya tsarkaka, duk wanda ya kautata niyarsa ya kara yawan arzikinsa, duk wanda ya kautata biyayarsa ga iyalan gidansa za a kara masa yawan shekarunsa) har ila yau cikin Littafin na Kafi an ruwaito hadisi daga Imam Sadik (a.s) ya ce ( hakika Bawa zai kasance ya na gaskiya a dukkanin Al'amuransa har sai an rubuta a wajen Allah yana cikin masu gaskiya, kuma wani Bawa zai dinga yin karya har sai an rubuta a wajen Allah yana cikin masu karya, idan Bawa ya yi gaskiya sai Allah madaukakin sarki ya ce ya yi gaskiya kuma ya yi biyyaya, idan kuma ya yi karya sai Allah madaukakin sarki ya ce ya yi karya kuma ya fajirirce wato ya zamanto fajiri).
***********************Musuc*************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai yi bayyani kan mahimancin dawwama a kan godiyar Allah domin yin hakan na daga cikin kyawawen dabi'un musulinci.a cikin Littafin Kafi Sikkatul Islam Kulaini ya ruwaito hadisi daga Abi Basir ya ce na cewa Babban Abdallah Imam Sadik (a.s) shin godiya ta nada iyakar da Bawa zai yi a ce masa mai godiya? Sai Imam (a.s) ya amsa masa da cewa ( Na'am ya godewa Allah bisa duk wata ni'ima da ya arzuta shi da ita, ta 'ya'ya ne ko kuma dukiya ce, kuma idan ya kasance ga ni'imar da Allah ya arzuta shi ta dukiya ce to ya fitar da Hakkinta, dangane da wannan Allah madaukakin sarki ya ce:(Muna tsarkake Wanda Ya hore mana wannan, ba mu zamanto masu ikon sarrafa shi ba) suratu Zukhrufi Aya ta 13 kuma A cikin suratu Kasasi Aya ta 24 Allah tabarka wa ta'ala ya ce: (Ya Ubangijina Hakika Ni mabukacin wani alhairin da za ka saukar mini ne!) kuma a wani gurin na daban y ace:(kuma ka ce Ubangijina ga shigar da ni mashiga ta gaskiya, kuma ka fitar da ni mafuta ta gaskiya, kuma ka bani hujja mabayyaniya daga gareka) suratu Isra'I Aya ta 80, Masu saurare ya bayyana cikin wannan hadisi cewa Ayoyin da Imam (a.s) ya yi istidlali da su ,dabi'antuwa da dabi'ar dawwama a godiyar Allah madaukakin sarki shine mafi koluluwa daraja na godiyar Allah tabaraka wa ta'ala kuma wannan siffa ce ta 'yantattu wajen bautarsu ga Allah madaukakin sarki.kamar yadda wannan hadisi ke bayyana mana hanyoyin dabintuwa da wannan kyakkyawar dabi'a shine Ambato tare da tunawar da kai hakikanin cewa Allah shine farkon ko wata irin Ni'ima tare da bayyana irin girmanta da kuma albarkantunta, a cikin Tafsirul Ayyashi an ruwito hadisi daga Imam Sadik(a.s) ya ce:(Ambaton Ni'ima shine ka ce godiya ta tabbata ga Allah wanda ya shiryar da mu da Addinin Mususulinci kuma ya sanar da mu Alkur'ani ya kuma bamu Annabi Muhamadou tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka, kuma bayan wannan ka fadi fadar Allah madaukakin sarki (Mu na tsarkake Wanda ya hore mana wannan,ba mu zamanto masu ikon sarrafa shi ba, Kuma hakika lallai zuwa Ubangijinmu za mu koma) suratu zuhruf Aya ta 13 taufiki da dabi'antuwa da wannan dabi'a mai girma shine mafi girma daga ko wata Ni'ima da za a godewa Allah abin godewa, hakika cikin littafin Kafi an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Ridha (a.s) ya ce:(duk wanda ya godewa Ubangiji a kan wata Ni'ima hakika ya gode masa kuma godiyar ta fi wannan Ni'imar) Imam Sadik (a.s) ya ce:(babu wata Ni'ima da Allah zai horewa Bawa karama ce ko babba, da zarar ya ce godiya tattaba ga Allah sai An tabbatar kuma ya cika wannan godiya ta shi a garesa). Har ila yau Imam (a.s) ya ce :(duk wanda aka horewa wata Ni'ima kuma ya yi godiya a cikin zuciyarsa hakika ya cika godiyarta). Masu saurare haki ne ga ko wani Bawa da Allah madaukakin sarki ya horewa wata Ni'ima ya gode masa, a cikin Littafin Kafi, an ruwaito hadisi daga Hamad bn Usman ya ce Imam Sadik (a.s) ya fita daga Masallaci yayin da dabbarsa ta bace ya na mai cewa idan Allah ya dawo min da ita zai yi masa godiya hakikanin godiya, Rawin ya ce bayan wani lokaci sai aka zo da dabbar da ta bace,sai Imam (a.s) ya Alhamdu lillah wato godiya ta tabbata ga Allah, sai wani daga cikin sahaban Imam (a.s) ya ce Raina fansarka ka ce zaka godewa Allah hakikanin godiya, sai Imam (a.s) ya ce ba ka ji ba Nace Alhamdulillah ba). Kamar yadda dabi'antuwa da wannan kyakkyawar dabi'a na godewa Ubangiji karama ko babba, na daga cikin hanyoyin rabauta da gidan Aljanna,a cikin Littafin Kafi an ruwaito hadisi daga Imam Sadik (a.s) ya ce:(hakika shan ruwan dayanku na yi masa sanadiyar rabauta da gidan Aljanna, wato a yayin da ya dauki abin shan ruwan ya kai bakinsa ya fadi bismillah bayan kuma ya sha daga cikinsa ya ce Alhamdulillah, ya kuma karar da ruwan yayin da yake bukatarsa (ma'ana kadda ya cika cikinsa sosai da hakan ya sabawa koyarwa musulinci) sannan ya godewa Ubangiji, hakan zai yi masa sanadin rabauta da gidan Aljanna) da fatan Allah madaukakin sarki ya arzuta mu da wannan kyakkyawar dabi'a domin albarkin shugaban kyawawen dabi'u da kuma iyalan gidansa tsarkaka.