Godiyar Allah a ko wani Hali 2
shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira
Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,a shirin da ya gabata mun yi bayyani kan mahimancin dawwama a kan godiyar Allah madaukakin sarki cikin ko wani hali, ganin mahimancin maudi'in shirin na yau ma ci gaba da wannan maudi'I, amma kafin nan bari mu saurai tanadin da aka yi mana a kan faifai.
*************************Musuc*****************************
Masu saurare, dabin'atuwa da dabi'ar godiyar Allah na daga cikin dabi'un shugaban kyawawen dabi'u Muhamadu dan Abdullahi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, a cikin Littafin Kafi, an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:(Ma'aikin Allah (s.a.w) ya kasance idan wani al'amari na firin ciki ya same shi sai ya ce godiya ta tabbata ga Allah a bisa wannan Ni'ima, idan kuma wani Al'amari na fakin ciki ya same shi sai ya ce godiya ta tabbata ga Allah a ko wani hali), A cikin Littafin Uyunu Akhbaru Ridha (a.s) an ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah (s.a.w) ya ce:(duk Allah madaukakin sarki ya yi masa Ni'ima to ya gode masa, duk kuma wanda yake neman wani Arziki to ya yawaita yin Istigfari ma'ana ya yawaita neman gafara a wajen Ubangijinsa, duk wanda wani al'amari ya yi tsanani a gunsa sai ya dinga yawaita fadar La Haula wala kuwata illa billahi ma'ana babu wani ƙarfi fãce daga Allah.)
Masu saurare, daga cikin misdakin dabi'ar godiyar Allah a yayin da Bawa ya rabauta da Ni'imarsa, cikin Littafin Amaly na shekh Saduk an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:(wata Rana Ma'aikin Allah (s.a.w) yana tafiya tare da sahabansa cikin garin Madina sai aka gay a sauka daga bisa dabbarsa sannan ya kai goshinsa kasa wato yayi sujjada kuma ya tsawita sujjadar, sannan ya tashi ya har dabbarsa, sai sahabansa suka ce Ya Ma'aikin Allah mun ganga ka, ka sauka daga bisa dabbarka ga yi sujjada kuma ka tsawaita yin sujjadar ko minene dalilinka na yin hakan? Sai Ma'aikin Allah (s.a.w) ya ce Mala'ika Jibrilu ne ya zo min da aiken sallama daga wajen Ubangijina kuma ya bani albishin cewa ba zai kunyata ni ba cikin Al'ummata, sai na ga ba ni da Dukuya barantana iniyi sadaka, ba ni da bawa ko baiwa barantana inyi 'yantar da su, sai na amsa wannan kauta da in godewa Ubangijina madaukakin sarki). A cikin wannan hadisi mai albarka za mu fahimci cewa yin sadaka a yayin saukar wata Ni'ima na daga cikin misdakin godiyar Allah, kamar yadda yin sujjadar Shukur na daga cikin misdakin wannan dabi'a, haka zalika maimaita yin sujada a yayin saukar wannan Ni'ima kamar yadda shugaban kyawawen dabi'u masu girma yake yi, a cikin Littafin Kafi, an ruwaito Hadisi daga Shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:(Hakika Ma'aikin Allah (s.a.w) ya kasance cikin bulaguro a kan taguwarsa sai ya sauka ya yi sujada har so biyar, yayin da ya hau taguwarsa sai aka ce ya Ma'aikin Allah mun ga yi wani abu da ba mu taba ganinka ka yishi a baya ba? Sai Ma'aikin Allah (s.a.w) ya ce Na'am hakan ne Mala'ika jibrilu ne ya tarbeni ya kuma bani albashi daga Allah madaukakin sarki sai na yi sujjadar godiya a ko wani albishir guda). Masu saurare wannan hadisi yana ishara a kan gaggauta yin godiya a yayin da bawa ya rabauta da wata Ni'ima daga Mahalicinsa kuma duk lokacin da aka maimata masa ni'imar ya godewa Allah ko da kuwa yana cikin lafiya ne kamar yadda muka ga Ma'aikin Allah yayi a cikin wannan Hadisi, har ila yau a cikin wani hadisin na daban da aka ruwaito cikin Littafin Kafi daga Hisham bn Ahmar ya ce: na kasance ina tafiya tare da baban Hasan Imam Kazim (a.s) a gefen garin Madina sai ya sauka daga kan dabbar da yake kai ya fadi ya yi sujada kuma ya tsawaita wannan sujjada, bayan ya dago kansa sai na ce masa kaina fansarka Hakika nag a ka fadi ka yi sujjada ga Ubangijinka kuma ka tsaiwaita ta ko minene dalilin yin hakan? Sai ya ce Hakika na tuna wata Ni'ima ce da Allah madaukakin sarki ya arzuta ni da ita sai na so in godewa Ubangijina a kan hakan), har ila yau Masu dabi'antuwa da wannan dabi'a na daga cikin hanyoyin da suke tsirar da Mutane yin mantuwa, gafala gami da fadawa cikin yanayi na tanadin Allah kadan kadan, a cikin Littafin Kafi, an ruwaito hadisi daga Umar bn Zaid ya ce Na cewa babban Abdallah Imam Sadik (a.s) hakika ni na Tambayi Allah madaukakin sarki da ya arzuta ni da kudi, ya arzutani,na roke shi da ya arzuta ni da Da ya arzutani, na roki shi ya arzuta ni da gida ya arzutani sai na ji tsoron cewa kamun Allah ne da kadan kadan, sai Imam (a.s) ya ce masa matukar dai da godiyar Allah, hakan ba zai tabbata ba har abada).
**********************Musuc****************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai bayyani ne kan yiwa Ubangiji godiya a yayin da Bawa da ga dan uwansa cikin ibtila'I na rashin lafiya ne, talauci ne ko kuma wata matsalar rayuwa ce, a cikin Littafin Kafi, an ruwaito hadisi daga Shugaban mu Muhamadou dan Abdull….tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(idan ku ka ga wadanda aka jarabcesu da wani bala'I na rayuwa kadda ku yi da su domin yin hakan na bakan ta musu rai).har ila yau a cikin Littafin Kafin an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Bakir (a.s) ya ce:(idan ka ga mutuman da Allah tabaraka wa'ala ya jarabce shi da wani ibtil'I, ka fadi so uku cewa Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya warkar da ni daga abin da ya jarabce ka da ya so da ya jarrabe ni da irinsa, sannan Imam (a.s) ya ce duk wanda ya fadi haka irin wannan ibti'I ba zai same shi har abada ba) Masu saurare, abin fahimta ga wannan hadisi da ya gabata shine dabi'antuwa da dabi'ar godiyar Allah tabarka wa ta'ala hanya ce ta kare Bala'I, daga cikin Adabin dabi'antuwa da wannan dabi'a yak an ceto da mai shi wajen fadawa cikin daudar izgili, girman kai ko ji-ji da kai. Hakika cikin Littafin Kafi an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Sadik(a.s) ya ce:(idan ka ga wani Mutum da aka jabbeshi da wani abu kai kuma Allah ya Ni'imceka da Ni'imarsa sai ka ce:(Ya Ubangijna ban a izgili, kuma ba na alfahari, saidai ina gode maka bisa girman Ni'imarka da ka bani) A wani hadisi da daban kuwa za mu fahimci cewa ziyartar wadanda Allah ta'ala ya Jarabce su da wani bala'I na daga cikin babbar martaba na godiyar Allah, kuma hakan ya kan tunatar da Mutum ga Lutufin Ubangiji na Ni'imar da ya yi bawan sa, wannan shine abin da Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya yi ishara da shi a hadisin da Shekh Tusy ya ruwaito cikin Littafin Amaly,(duk wanda bai san falalar Allah tabaraka wa ta'ala a kansa, sai kawai a abincinsa ko abin shansa to hakika iliminsa ragegge ne kuma azabarsa ta kurato), a cikin litattafan Alkhisal da Mahasin, an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Bakir (a.s) ya ce:(Bawa yana cikin Ababe guda uku, ibtila'I, karshen kwanukansa , ko kuma cikin wata Ni'ima ta Ubangijinsa, idan ya samu kansa cikin Ibtila'I daga Allah hakuri wajibi ne a gare shi, idan lokacin sa ya yi meka wuya shi ne abinda ya dace gareshi,idan kuma ya ni'imtu da wata Ni'imar Ubangiji sai ya godewa Allah madaukakin sarki)
*******************************Musuc*************************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.