Gaggauta Neman Gafara
shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareishi tare da wasiyansa iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira
Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,Shirin na yau zai bayyani kan gaggauta neman gafara a yayin sabo domin yin hakan na daga kyawawen dabi'un mumunai . amma kafin mu shiga shirin bari mu saurari tanadin da aka yi mana kan faifai.
*************************Musuc****************************
Masu Saurare, gaggauta komawa ga Allah domin neman Gafararsa a yayin aikata wani aiki mummuna na daga cikin alamar gaskiyar imanin mumuni, kamar yadda Shugaban Masu shiryarwa zababben Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka cikin wani Hadisi da Shekh Saduk ya ruwaito cikin Littafinsa Al-Amaly, inda Ma'aikin Allah (s.a.w) yake cewa:(duk wanda mumanan aiyukansa suka bata masa rai, kuma kyawawen aiyukan sa suka faranta masa rai shi Mumuni ne). har ila yau yayin da yake bayyana zababbun Bayi, Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(Zababbun Bayi sune duk lokacin da suka aikata aikata alheri ko kuma suka kyautata wani sai suyi farinciki, idan kuma suka yi wani munanar abu a bisa kuskure sai su gaggauta neman gafara a wajen Ubangijinsu).
Masu saurare, kamar yadda dabi'antuwa da wannan kyakkyawar dabi'a na daga cikin hanyoyin hudun da suke yin sanadiyar shiga cikin hasken Allah mai girma kuma hakan na nuna manya-manyar matsayin mumuni da martabarsa, Hakika Shekh Saduk cikin Littafinsa Alkhisal da Shekh Barki cikin Littafin Almahasin sun ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(Ababe guda hudu duk wanda ya kasance cikinsu yana cikin hasken Allah mai girma, na farko duk wanda karshen Al'amransa fadar Kalmar shahada wato shaidawa babu wani abin bauda sai Allah kuma Ni ma'aikin Allah ne, na biyu duk wanda wata musiba ta same shi zai ya ce daga Allah muke kuma gareshi za mu koma, na uku duk wanda wani Alheri ya same shi zai ce godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki, na huku duk wanda ya aikata wani kuskure zai nemi gafarar Allah kuma ya tuba a gare shi).
Masu saurare,babu wata bushara ko kuma albishir da aka baiwa masu dabi'ar Nadama a kan kurakuran da suka aikata kamar neman gafara ga Allah madaukakin sarki, a cikin Suratu Ali-imrana daga Aya ta 135 zuwa 136 Allah tabarka wa ta'ala ya ce:(Da kuma Wadanda suka aikata mumunan aiki ko suka cuci kansu, suka tuna da Allah, sannan suka nemi gafara game da laifukansu, ba kuwa mai gafarta laifinka sai Allah, ba kuma za su ci gaba bisa abin da suka aikata ba, alhali suna sane*Wadancan sakamakonsu shi ne gafara daga Ubangijinsu da Aljannoni (wadanda) koramu suke gudana ta karkashinsu, suna madawwama a cikinsu, Madalla da ladan masu aiki (na gari)) hakika cikin littafin kafi, an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Bakir (a.s) ya ce:(Israri ko kuma dagewa kan barna shine Bawa ya aikata wani laifi ko zunubi ba ya neman gafarar Ubangijinsa kuma ba ya yiwa kansa fada na ya tuba ga Allah madaukakin sarki),a cikin Tafsiru Majma'ul bayyan, an ruwaito hadisi daga Annabi Muhamadou Dan Abdullahi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(babu wani zunubi karami matukar Bawa zai dage wajen aikata shi, wato ci gaba da aikata zunubi komin kanantarsa, babu kuma wani zunubi babba tare da neman gafarar Ubangiji, babu mai dagewa kan aikata zunubi matukar yana Istigfar, ko da kuwa yana maimaita wannan zunubi so 70 a Rana).
***************************Musuc***************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, hakikanin istigfari shine yin nadama a kan laifi ko zunubin da bawa ya aikata, wato mumuni ya dabi'antu da dabi'ar damuwa a kan aikata mumunan aikin da ya aikata a baya kamar yadda aka bayyana a hadisin Ma'aikin Allah (s.a.w) a hadisin da muka kawo a baya, kuma wannan shi ne abinda Shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya tabbatar mana cikin hadisin da aka ruwaito a Littafin Kafi inda yake cewa (babu wani Bawa da zai aikata zunubi ya yi nadama a kan abinda ya aikata sai Allah tabaraka wa ta'ala ya yafe masa tun kafin ya nemi gafarar, kuma babu wani Bawa da Allah zai yi masa Ni'ima zai ya fahimci cewa wannan ni'ima daga Ubangiji ne ba wai dibarunsa ne sai Allah ya gafarta masa tun kafin ya gode masa), A bangare guda sheihin Malamin nan Muhamad bn Mas'oud Al'ayyashi cikin Tafsirinsa ya ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:(Allah ya yi rahama ga bawan da bai yardewa kansa ba Iblisi ya kasance masa aboki a harakokin Addininsa, Hakika Littafin Allah, tsira ne daga hallaka,Basira na daga makabtar bata, dalili ne na shiriya, waraka ne kuma ga abinda ke cikin zukata. yayin da ya umarce ku da neman gafara gami da tuba Allah madaukakin sarki ya ce:(Kuma wadanda idan suka aikata wata alfahasha ko suka zalunci kansu sai su tuna da Allah,saboda su nemi gafarar zunubansu ga Allah. Kuma wane ne ke gafara ga zunubai, face Allah? Kuma ba su dage a kan abinda suka aikata ba,alhali kuwa suna sane) suratu Ali Imara Aya ta 136. Sannan Imam (a.s) ya ci gaba da cewa duk wanda ya yi wani mugun abu ko ya zalunci kansa sannan ya nemi gafarar Allah zai samu Allah mai gafara, mai jin kai, wannan kuma shi ne Umarnin da Allah ya yi na neman tuba a gareshi bayan da ya gindaya sharadi na Tuba shin yin nadaba ga laifin da bawa ya aikata.
*********************Musuc
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.