Yin Tunani Kan Karshen Al'amura kafin Aikatawa
shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira
Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,Shirin na yau zai yi bayyani kan yin tunani ga karshen al'amari wato kafin aikata wani aiki da Mutum ke son aikatawa ya yi tunani kan karshen al'amuransa inda akwai alheri ya aikata, idan kuma babu alheri ya kaurace masa domin tsira daga sakamakon karshensa ,yin hakan na daga kyawawen dabi'un musulinci . amma kafin mu shiga shirin bari mu saurari tanadin da aka yi mana kan faifai.
*************************Musuc****************************
Masu saurare, wannan dabi'a ta yin tunani kan abinda zai biyo baya na karshen sakamakon al'ami kafin gudanar da ko wani irin aiki akasin dabi'ar aiki da gaggauna ne da bai samu yabo ba a musulinci, Hakika Shekh Abu Ja'afaru Barki yardar Allah ta tabbata a gareshi cikin Littafin sa Almahasin ya ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Bakir (a.s) ya ce:(wani Mutum ya zo wajen Ma'aikin Allah tisra da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidana tsarkaka ya ce masa Ya Ma'aikin Allah ka yi mani wasici, sai Ma'aikin Allah ya ce masa shin a shirye kake da ka karbi wasici na ?a fada masa wannan jumula har so uku shi kuma mutuman yana cewa Na'am ya Ma'aikin Allah, sai Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce masa duk aikin da za ka aikata ka yi tunani kan sakamakon da zai bayar, idan ka tabbatar mai amfani ne to sai ka aikata, idan kuma ka fahimci cewa zai cutar ka kaurace masa wato kadda ka aikata shi).Masu saurare hakika tabbatuwa da wannan dabi'a ta yin nazari da tunai na sakamakon karshen aiki kafin aikata shi shi ke samarwa zuciya tabbaci gami da konciyar hankali daga duk wani tsoro ko fargaba, Shekh Hasan bn Muhamad Attusy cikin Littafinsa Al'amaly ya ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:(mai saukin fishi ba shi da aboki, mai hasada ba shi da wadata,wanda ba ya tunani da nazari kan sakamakon karshen al'umura kafin aiki ba zai kasance mai Magana daya ba, ma'ana mai dagewa da kuma yin tsayin daka dangane da abinda ya fada ko kuma ya aikata, ba zai kasance mai Magana daya ba, domin yin nazari da tunani kafin aikata wani aiki, shike samar da nutsuwa a cikin zukuta), Hakika Masu saurare dabi'antuwa da wannan dabi'a na tunani da yin Nazari kan abinda zai biyo baya kafin aikata duk wani aiki yana kiyaye Mutum daga cutuwa, yin nadama gami da duk wani abin gyama, kamar yadda shugabanmu shugaban mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya yi ishara cikin wasiyar da ya yi ma dansa Muhamad bn Hanafiya wacce aka ruwaito cikin Littafin Man La Yahdurul Fakih inda yake cewa:(duk wanda ya saurari ra'ayoyin mutane daban-daban zai gano gurin kuskure, duk wanda ya shiga cikin wani al'amri ba tare da ya yi nazari kan sakamakon karshensa, hakika zai hadu da abinda ba zai yi masa dadi ba, yin tunani da nazari kafin aikata duk wani aiki shi zai amintar da kai daga yin nadama, mai hankali shi ne wanda ya wa'azantu daga abubuwan da suka faru a baya), a cikin Littafin Nahjul-balaga, Imam Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya bayyana cewa:(Harshen mai hankali yana bayan zuciyarsa, shi kuma zuciyar wawa tana bayan harshensa) abinda Imam (a.s) yake nufi da wannan hikima shine mai hankali ba ya fadar Magana sai ya yi tunani a zuciyarsa idan ta kasance mai amfani sai ya fada idan kuma ya fahimci cewa ba za ta amfanar ba hasali ma tana iya janyo izgili sai ya yi shuru domin hakan shi ya fi, shi kuma Wawa duk abinda ya zoma masa ba tare da ya yi tunani ba sai ya fada, daga baya kuma ya kasance mai nadama a kan abinda ya fada da fatan Allah madaukakin sarki ya kiyaye mu da irin wannan dabi'a ta wawaye domin albarkar Alkur'ani da sunan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi da kuma na iyalan gidansa tsarkaka.
*****************************Musuc****************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai yi bayyani kan mahimancin adalci, domin shi ma daga cikin wasiyoyin da Allah tabarka wa ta'ala ya yi a cikin ayoyi da dama na Littafinsa mai tsarki wato Alkur'ani mai girma, cikin Suratu An'ami Aya ta 152 Allah tabarka wa ta'ala ya ce:(Kuma kada ku kusanci dukiyar maraya sai da kyakkyawar niyar har sai ya kawo karfinsa, kuma ku cika ma'auni na mudu da nauyi bisa adalci, ba Ma dorawa rai sai abin da yake iyawa.Idan kuma kuka ba da shaida, to ku fadi gaskiya ko da kuwa a kan dan'uwa ne.Alkawarin Allah kuma ku cika (shi), da wannan (Allah) Ya yi muku wasiya don ku Wa'azanta), Masu saurare wannan Aya mai girma ta Ambato misalan aiyukan mutane da maganganunsu inda Allah tabaraka wa ta'ala yake yi musu wasiya na su yi riko da Adalci a dukkaninsu gaba daya.baya ga haka wannan Aya tana ishara ne kan dabi'antuwa da kyawawen dabi'u na tabbatar da misdakin cika alkawarin Ubangiji, kamar yadda hakan na daga cikin kyawawen dabi'un da aka yi umarni da su. Hadisai da dama sun shiryar da mu a kan mu dabi'antu da dabi'ar adalci a Magana da aiyuka, kuma hakan shi ke sanya mutum ya dandana dadin imaninsa, a cikin Littafin Kafi, an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) ya ce:(Adalci ya fi Ruwa ga mai tsananin jin ishurwa dadi, mafi yalwar adalci shine wanda aka yi a cikin ko koma ko da ya kasance a kan ka ne) har ila yau Imam (a.s): (Adalci ya fi zuma dadi, ya fi kumfa laushi ya fi turaren miski gamshi), sirin dake cikin wannan kyakkyawar dabi'a mai girma ta Adalci shi ne yana samarwa mutun nutsuwa da amsar kirar Lafiyayar fitirarsa ,samun sanhi da konciyar hankali a zuciyarsa .kamar yadda yake nisantar da mutum daga damuwa gami da juyayi na zalinci, kamar yadda dabi'antuwa da wannan dabi'a ta adalci na daga cikin misdakin riko da tsoron Allah.a cikin Littafi Kafi an ruwaito Hadisi daga Imam Sadik (a.s) ya ce:(ku ji tsoron Allah ku yi adalci, domin ku kuna yin batanci ga mutanan da ba sa adalci)
Masu Saurare, a cikin Littafin Kafi an ruwaito Hadisi daga Shugabanmu Imam Kazim (a.s) ya ce:(Hakika Allah tabaraka wa ta'ala ya karfafa mumuni da Ruhi daga garesa wanda ya kan je masa a ko wani lokacin da yake kyautatawa yana kuma aiyukan alheri gami da tsaron Allah, ya kan kuma kushewa a lokacin da yake sabon Allah yana fice gona da iri, shi wannan ruhi yana farin cikin a yayin da Mumuni ke kyautatawa ya kan kuma yin kara a yayin da yake aikata munana). Wasu hadisan kuwa suna yi mana hannunka mai sanda dangare da mumunan sakamako na rashin yin adalci, a cikin Littafin Kafi, an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Muhamad Bakir (a.s) yayin da yacewa daya daga cikin sahabansa:( ka fadawa mabiyanmu cewa hakika babu wanda zai samun abinda ke wajen Allah sai da aiki, kuma ka fada mabiyanmu wanda ya fi ko hasara daga cikin mutane ranar Alkiyama wanda yake da'awar adalci sannan kuma ya saba a kan waninsa) har ila yau cikin Littafin na Kafi, an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Sadik(a.s) yayin da yake fassara Aya ta 94 cikin suratu Shu'ara inda Allah madaukakin sarki ya ce:( Sannan aka kikkifa su cikinta(watau) su da batattu) su ne mutanan da suke da'awar adalci da bakunansu sannan suka saba hakan ga waninsu)
*******************************Musuc********************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.