Aug 21, 2016 13:39 UTC

shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira

Jama’a Masu saurare Asslama alekum barkanku da warhaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin zababbun aiyuka, shirin da ke yin dubu ga ayoyin kur'ani mai tsarki gami da hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka wadanda suke bayyani dangane da zababbun aiyuka da kuma kyawawen ayyukan musulnci da sune Allah madaukakin sarki ya sanya a matsayin kyakkyawar hanyar  samar da rayuwa mai kyau a zaman duniya da na lahira,Shirin na yau zai yi bayyani kan dabi'ar yiwa kai Adalci domin shi ma na daga cikin kyawawen dabi'un da Allah madaukakin sarki ya yi wasici a kansa, amma kafin shiga shirin bari mu saurari wannan.

****************************Musuc***************************

Masu saurare, dabi'ar yiwa kai Adalci shine mu'amalar Mutum tare da Mutane ta kasance cikin adalci da insafi ta yadda Bawa kadda ya yarda son kai da son zuciyar ya nisantar da shi daga fadar gaskiya ko kuma aikata ta , kuma wannan na daga cikin kyawawen dabi'un da Allah tabaraka wa ta'ala ya yi umarni da shi, sannan ya sanya shi daga cikin alamomin tsoron Allah, A cikin Suratu Ma'ida Aya ta 8 Allah Tabaraka wa ta'ala ya ce:(Ya Ku wadanda kuka ba da gaskiya, ku zama masu tsayawa sosai da hakkokin Allah, masu bada shaidar gaskiya kada kin wasu Mutane ya hana ku yin adalci, Ku yi adalci, shi ya fi kusa da tsoron Allah, kuma ku ji tsoron Allah, Hakika Allah masanin abin da kuke aikatawa ne) Maliman Tafsiri da dama sun bayyana cewa wannan Aya ta sauka ne domin yin umarni da kiyaye adalci a wajen mu'amala da kafirai, kuma dabi'antuwa da wannan dabi'a wasiyar Ubangiji ne wajen mu'amala da Mutane gaba daya. Masu saurare daga cikin albarkar dake tattare da yiwa kai adalci da insafi, hakika zababben Allah mai shiryarwa Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi, Shugabanin aiyuka, a riwayar da aka ruwaito cikin Littafin Kafi na Sikatu Islam Kulaini ya ce (Shugaban Aiyuka shine yiwa kai adalci a mu'amala tare da Mutane, daidaiton dan uwa saboda Allah, da kuma ambaton Allah cikin ko wani hali ko yanayi) domin haka wannan dabi'a mai girma na daga dabi'o'in da suke yi wa mai su sanadiyar rabauta da karamcin Allah madaukakin sarki da kuma samun kusancinsa, kamar yadda Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) ya yi ishara da hakan cikin hadisin da aka ruwaito a Littafin Al-Amaly na Shekh Saduk inda ya ce:(Ababe guda uku sune suka fi kusantar da  hallitu ga Allah ranar Alkiyama har sai an kamala musu hisabi, na farko mutuman da bai yi amfani  da karfin milki ,ko dukiya da sauransu ba wajen  tsoratar da na kasa da shi a yayin da ya yi fishi, na biyu Mutum man da yake tafiya tare da Mutane biyu bai karkata ga daya daga cikinsu, na uku Mutuman da yake fadar gaskiya a kan waninsa da kuma kansa) kamar yadda dabi'antuwa da wannan dabi'a mai girma na yin sanadin samun daukaka daga Allah madaukakin sarki, kuma na daga cikin tabbacin tawadu'I da kuma kaskantar da kai saboda Allah, Cikin Littafin Kafi An ruwaito hadisi daga Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya na cewa ( Ku saurara!duk wanda yake yiwa Mutane Adalci da insafi daga kansa wato ya fara da kansa babu abinda Allah zai kara masa face buwaya da kuma girma). Masu saurare, dabi'ar fara yiwa Mutane Adalci da Insafi daga kai na daga cikin alamar Imani, Hakika cikin Litattafan Kafi da Khisal, an ruwaito hadisi daga Mai gaskiya Amintacce tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:( duk wanda ya girmama fakiri da dukiyarsa ya kuma yiwa Mutane adalci da Insafi daga kansa shi ne Mumunin gaskiya) kamar yadda daga cikin albarkar dake tattare da wannan dabi'a yalwantar Arziki, da kuma rabauta da yardar Allah madaukakin sarki kai har da ma yardar Mutane, a cikin Littafin Almahasin, an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) ya ce:(duk Bawan da ya yiwa kansa Nasiha, ya kuma doru a kan  gaskiya, kuma ya dauki gaskiya a duk inda take, Allah zai bashi ababe guda biyu, Arziki daga Allah ya kuma fadadar da shi, Yarda daga Allah ta kuma isar masa).har ila yau cikin Littafin Kafi, Imam (a.s) ya ce:(duk wanda ya yiwa Mutane Adalci da Insafi daga kansa Allah zai yardar da shi ). Har ila yau daga cikin albarkar dake tattare da wannan Dabi'a, rabauta da mafi girman matsayi na gidan Aljanna, kamar yadda Shugabanmu, Imam Bakir (a.s) ya bayyana cikin riwayar da aka ruwaito cikin Littafin Kafi (Hakika Allah Tabaraka wa ta'ala yana da Aljanna wacce babu wanda zai shiga sai masu dabi'u uku, daya daga cikin su, shi ne wanda ya hukunta kansa da gaskiya), A cikin Littafin Amaly na shekh Tusy, an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:( duk wanda yake so Allah ya saukar da shi a Aljanna to ya kyautata dabi'unsa, ya kuma yiwa kansa Adalci, ya kuma ji kan Maraya, ya baiwa mai rauni, ya kuma yi tawadu'I da kaskantar da kai saboda Allah n da ya halice shi).

****************************Musuc****************************

Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai yi bayyani kan kaucewa abinda ke kaskantar da Bawa daga Zunubai, ma'anar hakan shi ne Mutum ya nisanci aikata duk wani zunubi komin kanantarsa, ya kuma kauracewa duk wani sharri komin kankantar sa, domin yin hakan na daga cikin kyawawen dabi'u da Allah madaukakin sarki ya yi wasici a kansa, cikin Littafin Man La Yahduruhul-Bakih na Shekh Shekh Saduk, an ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(Kada ku rena sharri ko da kuwa ya kasance karami ne a idanuwanku, kada kuma ku dauki aikin alherin da kuka yi babba ko da kuwa ya kasance mai girma a idanunku, domin kuma babu babban zunubi matukar ana Istigfari wato ana neman gafarar Ubangiji, kuma babu karamin zunubi matukar aka dage wajen ci gaba da aikata shi), a cikin Littafin Nahjul-balaga, an ruwaito hadisi daga Shugaban Muwahidai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya ce:(mafi tsananin zunibi wanda mai yinsa ya dauke sa a rene).A cikin Littafin Kafi an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce (ku ji tsorin zubunan da aka kankantar da su,domin ba a yin gafara a kansu, sai aka tambaye shi wasu zunubai aka kaskantar da su?sai ya ce zunubin da mutun zai aikata ya ce na ji dadi da ba wancan zunubi ne na aikata ba) wato hakan shi zai sanya Bawa ya kasa neman gabarar Ubangijnsa, domin yana ganin sa a matsayin karami sai ya ci gaba da aikatawa ba tare da yana neman gafara ba.

Masu saurare, Ma'aikin Allah (s.a.w) ya sanar da mu tasirin rashin dabi'antuwa da dabi'ar kaucewa zunubai da aikata shari komin kankantarsa a aikace cikin hikima, hakika cikin litattafan Kafi da Tafsiru Ayyashi, an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik(a.s) ya ce (hakika Ma'aikin Allah (s.a.w) ya sauka a wani yanki na sahara sai ya ce wa sahabansa a je a hado ita ce, sai suka ce ya Ma'aikin Allah Ai wannan kasa sahara ce babu ita ce a cikinta, sai Ma'aikin Allah ya umarce su da ko wannansu  ya je ya kawo wanda ya samu komin kankantarsa . Kowannansu ya samo wasu 'yan kuntaye, sai ya ce musu to haka ne zunubai ke taruwa domin haka ku kiyaye aikata zunubain da kuka daukansa a rene,domin duk abinda Mutum ya aikata za a rubuta a littafinsa, kuma wannan shine ma'anar fadar Allah madaukakin sarki(Mu kuma rubuta irin abubuwan da suka gabatar a rayuwarsu da kuma hanyar da suka bi,ko wani abu kuma mun kididdige a cikin Lauhul-mahafuz), wannan shi ne ma'anar hadisin da Imam Musa Alkazim (a.s) ya bayyana mana inda yake cewa (kada ku dinga kallon aikin alherin da kuke aikatawa mai girma kuma kada ku rena zunubi komin kakkantarsa domin shi zununbi kadan ya kan taru har ya zama mai yawa, kuma ku ji tsoron Allah cikin sirri har ku baiwa kanku insafi da Adalci).

*********************** Musuc*******************************

Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.