Aug 03, 2018 17:44 UTC
  •                   Musuluntar Wani Matashin Kasar Amurka

Musuluntar Wani Matashin Kasar Amurka

Kumaji da naci wajen neman jawabi akan rayuwa kaco kau, da kuma son sanin kowane ne mutum sannan menene makokarsa? Sannan kuma da kokarin samun jawabi daga akidu daban-daban da r'ayoyi mabanbanta, za su iya kai mutum ga cin karo da gaskiyar da yake nema. Wannan ne godaben da Benjamine Kwiecien ya hau yake tafiya akansa. A karshe kuwa ya gano addinin musulunci wanda ya ba shi jawabin dukkanin tambayoyin da yake da su.

 

Tare da cewa Benjamine ya taso ne a gidan da suke din darikar katolika ta addinin kirista, sai dai ba masu riko da addini ba ne. Ya fadi cewa tun yana matashi tambayoyi masu yawa su ke yawo a cikin kwakwalwarsa akan daga ina mu ka fito? Me kuma mu ke yi a cikin wannan duniyar sannan ina ne makoma?

 

Banjemine ya ci gaba da cewa; Ba na samun jawabi kamar yadda ya dace akan tambayoyin da nake yi."

 

Dangane da akidar kiristanci da daukar annabi Isa (a.s) a matsayin Ubangiji, Benjamine ya ce; " Sabanin sauran mutane, ina son yin nazari domin samun jawabi. Don haka ina son sanin wanene Ubangiji? Daga ina Bible ya zo? Kuma wane sako ne a cikinsa?

 

Benjamine ya ce; Hatta wadannan tambayoyin bai sami jawabinsu ba kamar yadda ya dace har zuwa lokacin da ya shiga jami'a ya fara karatu akan addinan duniya. Darussa ne wadanda za su iya zamar masa kyakkyawar masoma ta samun jawabin da yak enema akan halitta da mutu.

 

Karatun da Benjamine ya rika yi bai takaita a cikin na jami'a ba kadai, ya rika yin nazari da bincike nashi na kashin kanshi na lokaci mai tsawo. Ta kai shi ga iya riskar inda bayanai a cikin addinai daban-daban suke da rauni da inda su ke da karfin hujja.

Dangane da addinin yahudanci yana cewa: Da gaske ne cewa a bisa tushe yana cikin saukakkun addinai, amma sannu a hankali daga baya an cakuda shi da kabilanci da karkatar da shi daga asalinsa, don haka ba zai zama karbabbe ba. Domin suna cewa Allah ya aiko mala'ika wurin annabi Musa ya shaida masa cewa; Allah ya daukaka yahudawa akan dukkanin al'ummu sannan kuma zai basu nasara akansu. Wannan en ya sa suke jin cewa wajibi ne su dannen dukkanin al'ummu saboda su mulki duniya."

Wani daga cikin addinan da Benjamine ya yi nazari da bincike akansu shi ni addinin musulunci. Yana fadin cewa: "Dukkanin addinan da na yi nazari akansu, na ci karo da rauni wanda nake samun kafar yin suka, amma da na zo kan musulunci da littafinsa mai tsaro ban ci karo da irin wannan raunin ba. Kuma shi ne addinin da na aminta da shi. Kuma koyarwar da dokokinsa sun dace da hankali. Na kuma kasa gano inda zan yi suka a cikinsa."

Wannan bawan Allah dan kasar Amurka ya dauki lokaci mai tsawo yana nazari akan al'kur'ani mai girma.

 

Benjamine ya shiga fagen nazarin alkur'ani mai girma na tsawon shekara guda ba tare da ya san cewa; shi ne mu'ujiza mafi girma da musulunci yake takama da ita ba. Kuma kowane mahaluki da zai bude shafukansa ya karanta ba tare da wata manufa ba, to zai fisgu zuwa kan tafarkin shiriya.

 

Sannu a hankalin Benjmine ya fara jin yana son al'kur'ani. Ya bayyana cewa:

 

" Nutsuwar da nake samu idan ina karanta al'kur'ani ban sami kwatankwacinta ba idan ina karanta wani littafi. Don haka a dare da rana nake daukar al'kur'ani in karanta saboda in sami nutsuwa. Wannan nutsuwar da kuma debe kewar da nake samu daga al'kur'ani sun sa mani kaunar addinin musulunci."

 

Al'kur'ani mai girma ya sake tabbatar da mu'ujuzarsa akan Benjamine ya zamar amsa hanyar shiriya. Ya sa shi jin cewa a shirye yake ya karbi addinin musulunci.

 

Dalili na biyu baya ga al'kur'ani mai girma da ya sa Benjamine son karbar musulunci shi ne karanta tarihi da halayen annabi Muhammad (s.a.w.a) da ya yi.

 

Ya sha jin labarai akan annabi Muhammadu (s.a.w.a) da kyawawan halayensa daga bakin abokansa musulmi. Akan haka ne yake cewa:

 

"Labarun da nake ji dangane da annabi Muhammadu suna da jan hankali a wurina. Kuma labarum kyawawan halayensa da na ji sun zamar mani kafar kai wa ga shiriya."

 

A karshe bayan daukar shekaru uku yana nazari da bincike Benjamine ya kai ga karbar addinin musulunci.

 

                            ****

 

Yadda ya karbi addinin musulunci labari ne mai jan hankali. A karon farko ya je wata cibiyar addinin musulunci da take a birnin Los Angeles na Amurka. Ya ba da labarin abin da ya faru kamar haka:

 

" Lokacin da na isa wajen sai na fahimci cewa cibiya ce ta mabiya mazhabar shi'a. Da farko na yi shakku da jin takaicin da ya sa ban yi dogon nazari ba akan banbancin da yake a tsakanin shi'a da sunna. Sai tunani ya zo min cewa in koma gida domin ban gama shiryawa ba. Amma nan da nan na sauya tunanina na yanke shiga ciki domin in ga wane irin banbanci ne yake tsakanin shi'a da sunna.

 

Wani dattijo mai ilimin addinin musulunci kuma mai wayewa ya kwatantawa Benjamine da yi masa bayani akan addinin musulunci ta yadda ya zauna masa a zuciya. Nan take ya yi Kalmar shahada ta shiga addinin musulunci.

 

Acan ya hada da wani malami dattijo da ya ba shi Kalmar shahada. A cikin wannan cibiyar ne ya fara yin salla. Dangane da yadda ya fara yin salla, Benjamine yana fadin cewa:

 

" A cikin wannan cibiyar ta shi'a ne fara yin sallata ta farko; na ji cewa na gamsu daga abin da na aikata."

Bayan idar da salla, dattijon ya gayyaci Benjamine zuwa addu'ar daren juma'a ta Du'au Kumyl. Ya kuwa amsa gayyata ya je wurin addua a wannan daren. Bayan kammala adduar wacce Kumayl ya rawaito daga Imam Ali (a.s), dattijon ya gabatar da jawabi akan Imam Ali (a.s) da ya bayyana a matsayin mafi kasantuwa akan tafarkin shiriya bayan manzon Allah (s.a.w.a) Mutum ne mai hakuri wanda a kodayaushe yake girmama kowa da kowa. Na ji cewa ina son in zama mai aiki da halayensa."

 

Bayan musuluntarsa, wata kafar ta nazari da bincike ta bude a gaban Benjamine. Ya bayyana cewa: Lokacin da na musulunta ba ni da masaniya akan ahlul bayti, (a.s). Abin da kawai na sani shi ne cewa; Ahlul Byti (a.s)suna daratta  Imam Ali bayan annabi, amma ban san su wanene ahlul bayti ba. Ko kuma me ya sa suke da muhimmanci a cikin addinin musulunci.

A dalilin haka bayan musulunta ta na mai da hankalina wajen yin nazari da bincike akan ahlul bayti (a.s). Bayan da na fahimci matsayar ahlul bayti (a.s) zuciyata ta kaunace su na kuma kaunaci mazhabarsu.

Benjamine ya kamu da kaunar ahlul bayti (a.s) musamman Imam Husain ( a.s). Yana bayyana cewa:

"Imam Husain ya sadaukar da kansa da iyalansa domin addinin musulunci. Ba a yi galaba akansa ba, shi ne wanda ya sami nasara a filin daga…. Lokacin da na fara jin labarin Karbala na ji cewa lallai na gamsu da mazhabar ahlul byati.

Daga cikin fatan da Benjamine yake da shi da akwai ziyartar Karbala wurin hubbaren Imam Husain.. Haka nan yana fatan ya rayu ya ga bayyanar Imam Mahadi (a.s) da zai shimfida hukumar adalci a doron kasa. Ya kuma kawar da zalunci.

 

Rayuwar Benjamine ta sami sauyi ta kowace fuska. Hatta gabanin ya yi Kalmar shahada ya kasance mai aiki da wasu dokokin musulunci. Yana fadin cewa:

" Gabanin in musulunta ina aiki da dokokin musulunci masu yawa. Wannan ya sa iyalaina suna yin mamaki. Ba na cin naman alade ko shan giya. Ba kuma na yi caca."

Musuluntar da ya yi ta ja hankalin iyaye da danginsa. Yana bayyana cewa:

Daya daga cikin 'yan'uwana mata, wacce ta fahimci cewa da akwai sauyi a salon rayuwata, ta tambaye ni, ka musulunta ne? Na ba ta jawabin cewa kwarai na musulunta. Daga nan dukkaninsu sun fahimci cewa lalai na zama musulmi.

Kamar yadda ake tsammani, iyaye da dangin Benjamine sun tasirantu da parpagandar nuna kin jinin musulunci. Don haka a matakin farko suka zama masu adawa da musuluntarsa. Sai dai kyawawan halaye na musulmi suna iya yin tasiri wajen sauya ra'ayin mutane.

Benjamine ya ba da labarin cewa:

" Iyalaina da suka fahimci sauyi halayena bayan gushewar lokaci mai yawa sun gasmu. Mahaifiyata ta yi farin ciki akan yadda rayuwa ta sauya ta yadda ba ni yin caca, kuma ba ni fita shan giya. Wannan ya sa yadda suke kallon musulunci ya sauya… Ina matukar kokarina domin in zama kyakkyawan jakadan addnin musulunci."

 

Tags