Aug 03, 2018 18:07 UTC
  •                                     Shekaru 40 Na Cin Nasarar Juyin Musulunci                                                          ( 1)

Shekaru 40 Na Cin Nasarar Juyin Musulunci ( 1)

A jawabin da ya yi na sabuwar shekarar hijira shamshiyya ta bana 1397, jagoran juyin musulunci ya tabo sauye-sauye da su ka faru a cikin shekaru 40 daga cin nasarar juyin musulunci a fagagen siyasa da tattalin arziki da kuma daukakar da alúmmar Iran ta samu a wannan lokacin.

Jagoran ya yi ishara da ayyukan da juyin ya yi a cikin shekaru 40 da kuma yadda ya dakile makarkashiyar Amurka a cikin wannan yankin sannan ya kara da cewa; Ta fuskar kwararrun da ake da su a fagen jamiói da makamashi na mai da gas da kuma kirkira da kere-kere, da akwai dama mai girma da ake da ita a cikin Iran, kuma ta hanyar dogaro da su, za a iya kafa gagarumin ci gaba.

Daya daga cikin batutuwa masu muhimmanci da jagora yake yin ishara da su, shi ne tsarin da juyin musulunci yake tafiya akansa na alúmma da demokradiyya da kuma cin gashin kai na siyasa.

Tun da fari, juyin musulunci na Iran ya ginu ne bisa ginshiki na demokradiyya, ta yadda ya bude shafinsa na farko da kada kuriár raba gardama dangane da tsarin da alúmmar kasa suke son ya tafiyar da su.  Abin da ya rika biyo wa baya shi ne gudanar da zabuka a tsawon shekaru 40 na cin nasara. Kuma a wannan tsakanin an kafa gwamnatoci masu mabanbantan raáyi da mahanga. Domin a karkashin tsarin musulunci na Iran, raáyin alúmma wani ginshiki ne.

A cikin shekaru masu yawa, nazari aka ci gaba da bunkasar ayyukan siyasa yana daga cikin jigon da ya ja hankalin manazarta da masana. A cikin kasashe masu tasowa tattauna wannan batu yana da muhimmanci, domin a cikin wadannan kasashen koma baya da ake da shi ta fuskar siyasa, yana da tasiri a cikin fagage daban-daban na rayuwa.

Ci gaba da bunkasar ayyukan siyasa yana tattare a cikin fuskoki biyu; Shigar alúmma a dama da su a cikin fagen siyasar, sannan kuma da yadda ake yin gasa da hamayya mai tsafta ta siyasa ba da gaba ba.

A cikin kasashen da suka ci gaba, fiye da shekara dari da suka shude ne aka sami sauyin da shi ne ya haifar da ci gaba da bunkasar ayyukan siyasa da ake da su a yanzu.

Ci gaban da ake samu na siyasa yana da maánoni daban-daban da masana suka ambata. Ga misali Losin Pay ya bayyana abinda hakan yake nufi da cewa; Wani yanayi ne mai fuskoki uku, daidaito, shigar alúmma a dama da su a cikin fagen siyasar, da samar da yanayi na siyasa wanda zai zo da zaman lafiya a cikin alúmma. Haka nan kuma yin ayyukan cibiyoyi mulki cikin kwarewa da cin gashin kai.

Sai dai duk da sabanin da ake da shi a tsakanin maánoni na ci gaban siyasa, baki ya hadu akan cewa ya kunshi; shigar alúmma a dama da su a cikin fagen siyasa.

Idan mu ka dauki cewa  shigar al'umma a dama da su shi ne ci gaba da bunkasar harkokin siyasa, haka nan kuma yin gasa da hamayya a tsakanin jam'iyyu da zummar kai wa mulki da tafiyar da kasa bisa manufa da kowace jam'iyya take da ita, a yanayi irin wannan za a iya cewa; Hamayya da goyayya ta siyasa sun ginu ne akan jam'iyyu da zabe da majalisar dokoki. Su ne kuma ginshikin tsarin demokradiyya.

Alaka a tsakanin kungiyoyi na al'umma wanda ake kira ; kungiyoyin farar hula' da kuma fagen siyasa yana a matsayin wani kyakkyawan misali.

 A bisa ka'idar tsarin demokradiyya, al'umma su ne wadanda ayyana makomarsu yake a hannunsu. Su ne masu shata salon rayuwar da za su yi, sannan kuma da ayyana hanyoyin kai wa ga fahimtar ma'anoni na bai daya a hankalce, da kuma a fagen aiki. Idan kuwa aka bai wa wannan al'ummar dukkanin kayan aikin da take bukatuwa da su, to shakka babu za ta yi zabi hanya mafi dacewa.

                                                     ****

Bayan kafuwar tsarin jamhuriyar musulunci a Iran, da kuma shimfida tsarin musulunci, an taso da nazari da bincike akan alakar siyasa da addinin musulunci.

Halarcin tsarin jamhuriyar musulunci ta Iran ya samo asali ne daga goyon bayan da yake samu da alumma. Hakan kuma ya fito fili a cikin zabuka masu 'yanci da ake yi da kuma tsarin shawara da ake da shi, a karkashin majalisa.

A jamhuriyar musulunci ta Iran ra'ayin mutane yana da maukar muhimmanci, kuma akan haka ne tsarin jamhuriyar musulunci yake tafiya. Mutane suna zabar wadanda za su wakilce su kama daga kan yan majalisar zuwa kan jagoran juyi duk al'umma ce take yin zabe.

Shi kuwa juyin musulunci na Iran tun farkon cin nasararsa ya bai wa al'ummar kasa damar su zabawa kansu nau'in tsarin da suke son ya mulke su ta hanyar kuriar raba gardama da aka kada. Abin da ya biyo baya shi ne gudanar da zabuka a fagage daban-daban. Daga kan 'yan majalisa masu wakiltar al'umma zuwa kan shugaban kasa. Hatta mukami na jagoran juyin musulunci zabarsa ake yi ta hanyar zabar majalisar kwararru wadanda su ke zabarsa kai tsaye sannan kuma su rika sanya idanu akan ayyukansa.

Jagoran juyin musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda ya gabatar da jawabin shiga sabuwar shekarar hijira shamshiyya ta 1397, ya ambato manufofin da jamhuriyar musulunci ta sanya a gaba take kuma aikata su a cikin shekaru 40 na rayuwarta. Jagoran ya zayyana abubuwan da suke a matsayin wani shashe na abubuwa masu kima na juyin. Daga cikinsu da akwai yanci da cin gashin kai da gaskata kai da demokradiyya da adalci.

Bugu da kari jagoran ya yi ishara da yadda makiya su ke parpaganda da zummar bakanta sunan jamhuriyar musulunci a duniya, musamman akan 'yanci. Jagoran ya ce a Iran babu wani mahaluki da ake tsare da shi  ko takura masa, ko yi masa barazana saboda ra'ayi ko tunaninsa.

Abubuwan da jagoran ya ambata suna a matsayin ruhin tsarin mulkin jamhuriyar musulunci ta Iran ne wanda yake magana akan 'yanci da cin gashin kai.

Gulam Riza Madani  wanda masanin dokokin kasa da kasa ne ya bayyana cewa; Hakkoki na tushe suna bayyana mahangar yadda salon mulki yake tafiya.

A bisa wannan mahangar, daya daga cikin muhimman jigon da manazarta suke yin nazari a kansa, dokoki na tushe a cikin kowace al'umma shi ne hakkokin da ake bai da daidaikun 'yan kasa, sannan kuma da kayyade karfin masu tafiyar da mulki. A karkashin wannan mahanga ana yin nazari akan alakar mutum da al'umma ta fuskar zamantakewa da kuma, daidaikun mutane da jama'a.

Montesquieu wanda shi ne marubucin littafin "Ruhin dokoki' ya bayyana 'yanci a matsayin aikata dukkanin abubuwan da doka ta bada dama.

Sanawarwar hakkokin bil'adama na kasar faransa wanda aka amince da shi a 1789 an bayyana hakkoki da cewa; Damar zartar da ayyukan da ba su cutar da wani."

Shi kuwa Hegel wanda sanannen malamin falsafa ne, ya yi imani da cewa;'yanci shi ne ginshikin rayuwa.

A karkashin juyin musulunci 'yanci ginshiki ne mai muhimmanci kuma yana cikin manyan manufofin da juyin musulunci ya sa a gaba. A cikin tsarin mulkin Iran an ware dokoki masu yawa wadana su ke magana akan 'yancin daidaikun mutane da al'umma da bangaren shari'a da kuma tabbatar da tsaron al'umma.

Tun farkon juyin musulunci ne yake ba da taken; Cin gashin kai, 'yanci da kuma jamhuriya."

 

A gabatarwa ta tsarin mulkin jamhuriyar musulunci ta Iran an rubuta cewa:

Salon hukuma ya samo tushe ne daga mahangar musulunci, kuma ba shi da alaka da salon mulki na damfara daidaiku ko wata kungiya akan al'umma, illa iyaka aiwatar da manufofi ne na siyasa na mutane masu mahanga guda domin isa ga manufar karshe wacce ita ce haduwa da Allah."

Daga nan abin da ya biyo baya shi ne ware fasali guda acikin tsarin mulkin wanda yake magana akan hakkokin al'umma. A cikin tsarin mulkin da akwai cikakken bayani akan hakkoki na koli na 'ya kasa, haka nan kuma abin da ya shafi 'yanci na daidaikun mutane.

An kuma shata layuka na iyakokin da ke tsakanin 'yancin da daidaiku suke da shi wajen fuskantar al'umma, da kuma iyakokin da al'umma suke da shi wajen fuskantar daidaiku.

Daga cikin hakkokin da tsarin mulki ya ambata da akwai kasantuwar mutane daidai da juna a gaba doka, haka nan hakkin kowa da kowa wajen hakkoki ba tare da la'akari da launin fata ko harshe ko asali.

Haka nan kuma dokoki sun ba da kariya ga daidaikun mutane akan hakkinsu na samun tsaro da kariya daga cin zarafi ko cutar da rayukansu da dukiyarsu. Hakkinsu ne kuma su mallaki matsuguni da tsaro daga leken asiri da hana azabtarwa, da kuma hakkin tofa albarkacin baki.

Wani sashen na dokoki ya bai wa mutane hakkin kafa kungiyoyi da jam'iyyu na siyasa da hakkin yin zanga-zanga da hakkin yin tunani da akida da hana binciken akidun mutane.Dukkanin wadannan suna a karkashin tsarin mulkin jamhuriyar musulunci ta Iran.

Wani aji na 'yanci shi ne wanda ya yi magana akan kafafen watsa labaru da, don haka kamar yadda mutane su ke da 'yanci, to su ma kafafen watsa labaru suna da nasu 'yancin kama daga kan jaridu da sauransu.

 

A karkashin tsarin jamhuriyar musulunci ta Iran batun kamalar mutum ne manufa ta koli da aka sa a gaba. Kamala kuwa tana samuwa ne a karkashin 'yanci. Sai dai 'yanci bai takaita a cikin fagen rayuwar yau da kullum kadai ba, yana a matsayin wata bai wa ce da Allah ya yi wa mutum saboda ya hau hanyar shiriya. Wannan ce manufa ta karshe wacce tsarin mulkin jamhuriyar musulunci ya doru akanta.

 

Tags