Nov 27, 2018 04:23 UTC
  •                    Sabon Takunkumin Amurka Akan Iran

Sabon Takunkumin Amurka Akan Iran

 

Masu sauraro barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wata fitowar ta shirin mu leka mu gani. Shiri ne wanda mu ka saba kawo muku batutuwa daban-daban da su ka shafi fuskokin rayuwa.

 

To a yau shirin namu zai yi dubi ne dangane da sabon takunkumin da Amurka ta kakabawa Iran.

 

Da fatan za a kasance a tare da mu domin jin yadda shirin zai gudana.

                              ****

 

Duk wata dama da shugaban Amurka Donald Trump ya samu, sai ya yi amfani da ita domin sukar yarjejeniyar Nukiliyar Iran, wacce yake bayyanawa a matsayin yarjejeniya mafi muni a tarihi. A karshe kuwa a ranar 8 ga watan Mayu na 2018 ya sanar da ficewar kasarsa daga cikin yarjejeniyar.

Abin da ya biyo baya shi ne kakabawa Iran takunkumai da Amurkan ta yi t agefe daya wanda ya kunshi kaso na farko da na biyu.

Kason a farko shi ne wanda ya kunshi kwanaki 90 sai kuma ta biyu da ya kasance bayan kwanaki 180.

Na farko ya fara ne a ranar 6 g awatan Agusta, yayn da biyu y afara daga ranar 5 ga watan Nuwamba.

A ranar 2 ga watan Nuwamba shugaban kasar ta Amurka Donald Trump ya fitar da bayani yana mai cewa wannan shi ne takunkumi mafi tsanani wanda Amurka ta taba kakabawa Iran.

Sai dai Trump din ya riya cewa takunkumin ba zai shafi abiinci, magani da kayan noma ba.

Amma abida ya faru a baya ya tabbatar da cewa; Amurkan ta samar da wani yanayi wanda ya hana shigo da magani da wasu kayan abinci da amfanin gona zuwa cikin Iran.

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pampeo tare da shugaban Baitul Malin Amurka, sun sanar da fara aiki da takunkumin akan Iran a ranar 2 ga watan Nuwamba. Abin da Amurkan take son cimmawa a wannan tsakanin shi ne dakatar da sayar da man fetur din Iran a duniya baki daya. Haka nan katse duk wata mu'amala a tsakanin Bankunan Iran da sauran na duniya, wanda a karshe zai kai ga durkushewar tattalin arzikin Iran.

A hakikanin gaskiya Amurkan ta bude yakin tattalin arziki ne da Iran.

Brain Huk wanda yana cikin masu tafiyar da harkokin takurawa Iran a Amurka, ya bayyana cewa wannan karon Amurka da gaske take dangane da takunkuman da ta kakabawa Iran.

Kasashen duniya da dama sun bayyana damuwarsu akan matakin da Amurkan ta dauka akan Iran tare da yin gargadi akan abin da zai je ya dawo. Rasha ta bayyana cewa abu ne mai yiyuwa takunkumin ya sa Iran ta fice daga cikin yarjejeniyar Nukiliya wanda a karshe zai jefa yarjejeniyar NPT ta kayyade yaduwar makaman Nukiliya cikin hatsari.

A cikin watan Satumba na wannan shekarar ta 2018 Trump ya bukaci dukkanin kasashen duniya da su daina sayen man fetur din Iran kafin ranar 5 ga watan Nuwamba, sai dai wannan wa'adin da Amurkan ta gindaya ya fuskanci koma baya.

Kasashen China da India su ne na farko wajen sayen mafi yawan man fetur din Iran, ba su mika kai ga kiran na Amurka ba suna ci gaba da saye. Haka nan kasashen Rasha da Trukiya suna ci gaba da mu'amala da Iran ta fuskar gas da Man fetur. Wannan ne ya tilasta gwamnatin Trump ta rusuna da cewa ba za ta iya tsayar da kwararar man fetur din Iran a kasuwannin duniya ba.

 

Dangane da haka ne mai ba da shawara akan harkokin tsaro a fadar White House, John Bolton ya fada a ranar 31 ga watan Oktoba cewa; Za a kakaba takunkumin ne ta yadda ba zai cutar da kawayen Amurka ba. Bolton ya kara da cewa: Gwamnatin Amurka ta fahimci cewa wasu kasashen ba za su iya yanke sayen man fetur daga Iran ba kai tsaye.

 

Gabanin wannan lokacin Bolton ya ce kafin ranar 5 ga watan Nuwamba yana son ganin an dakatar da sayen man fetur din Iran baki daya.

Wannan ne ya sa fadar white house ta fara nesanta kanta daga matakin farko na son ganin ta yanke sayar da man fetur din Iran baki daya.

Siyasar da Amurkan ta fito da ita, ita ce bukatar kasashen su rage yawan man fetur din da suke saya daga Iran ba dainawa baki daya ba. Idan suka yi hakan Amurkan za ta daga musu kafa ta basu lasisin ci gaba da sayen man daga Iran.

 

Kasashe 3 daga cikin kasashe 5 da su ka fi sayen man fetur din Iran, wato China, Indiya da Turkiya, sun ki yarda da bukatar ta Amurka. Korea ta Kudu kuwa bukatar Amurkan ta yi da ta daga mata kafa.

A hakikanin gaskiya Amurkan ta fahimci cewa ba za ta iya dakatar da cinikin man fetur din Iran ba, don haka ta riya cewa za ta dagawa wasu kasashe kafa kan batun.

 

Daga lokacin da Amurkan ta sanar da fara aiki da bangare na biyu na takunkumin da ta kakabawa Iran wanda ya shafi man fetur a ranar 5 ga watan Nuwamba, kasuwar man fetur ta fuskanci matsala. Lamarin da ya sanya damuwa a tsakanin kasashen duniya saboda yana a matsayin kada karaurawa ce ta hatsarin da ka iya faruwa a kasuwar man fetur.

 

Kakabawa Iran takunkumin man fetur da hana ta sayar da shi, yana nufin tashin gwauron zabbi na farashin man fetur.

Gwamnatin Trump ta yi mafarkin ganin cewa babu wata kasa da take sayen man fetur din Iran. Da kuwa hakan ta faru, to da an fusakanci koma baya mai girma a cikin kasuwar man fetur ta yadda hatta kasashe kamar su Saudiyya ba za su iya cike gurbin abin da aka rasa ba.

Wani kwararre a fagen man fetur Bjornar Tonhaugen ya ce; Da kamar wuya ace za a dakatar da cinikin man fetur din Iran baki daya.

Siyasar Trump ta son ganin farashin man ya yi sauki tana cin karo da yadda ake samun karuwar farashin nasa a cikin watannin bayan nan. Kuma a fagen siyasar Amurka gabanin yin zaben yan majalisa abu ne mai matukar.

Grant Smith kwararre a fagen siyasar Amurka ya bayyana cewa; hauhawar farashin man fetur a gab da zaben zango na tsakiya na 'yan majalisar dokoki da aka yi, shi ne ya tilasa Trump ya ja da baya akan saiysarsa dangane da Iran. Shi ne abinda ya sa gwamnatin ta Trump ta sanar da daga wa kasashe 8 kafa dangane da sayen man fetur din Iran.  Wannan ya taimaka aka sami dan koma baya kadan a farashin man fetur din a kasuwannin duniya.

Saboda Iran ce kasa ta uku a jerin kasashen kungiyar OPec da su ka fi fitar da man fetur, rage yawan man da take sayarwa zai shafi kasuwar duniya.

Iran ta bayyana cewa za ta iya ci gaba da fitar da abin da yah aura ganga miliyan daya a kasuwa.

Ridha Fadedar wanda shi ne shugaban kasuwar makamashi na Iran ya bayyana cewa; A cikin tsarin kungiyar Opec, Iran ce ta uku bayan Saudiyya da Iraqi wajen sayar da mai. Don haka rage yawan man da Iran take fitarwa ba shi da yawa."

Kwararru da fagen man fetur suna bayyana cewa idan har Amurka ta cimma burinta na dakatar da cinikin man fetur din Iran baki dayansa, to man fetur na ajiya zai kare, wanda hakan zai haifar da rashin daidaito a cikin kasuwar duniya. Rashin daidaito kuwa zai haddasa hauhawar farashin man.

 

Hukumar makamashi ta duniya tana bayyana cewa; An sami daidaito na wani lokaci a cikin kasuwar mai, amma abu ne mai yiyuwa a karshen 2018 wato lokacin aiki da takunkumi akan Iran, kasuwar man za ta ga fadi tashi.

 

Wannan gargadin yana nuni ne da rashin gaskiyar abin da Amurkan take riaywa na cewa idan aka dakatar da cinikin man fetur din Iran, babu abin da zai faru a cikin kasuwannin duniya na mai.