Mar 21, 2017 07:35 UTC
  •  Azabar Al'ummar Musulmin Rohinga Na Kasar Myanmar.                                    (  2)

Azabar Al'ummar Musulmin Rohinga Na Kasar Myanmar.

Idan za mu yi bita a takaice na abinda ya gabata, za mu fara ne da cewa; al'ummar Rohinga suna daga cikin mazauna na asali a yankin da su ke. Daruruwan shekaru su ka yi a wannan wuri gabanin kafa kasa dunkulalliya mai suna Burma ko Myanmar a yanzu.

Sun karbi addinin musulunci, kuma a halin da ake ciki a yanzu kawo 70 % na mazauna yankin musulmi ne.

Marubuta tarihin shigar musulunci yankin, suna ambatar cewa; tun a karnin farko na bayyanar musulunci ya isa wannan yankin. Al'ummun kasashen Iran da kuma larabawa da su ke tafiye-tafiye da a ruwa, sun rika watsa sakon addinin musulunci.. Yankin Arkhane kuwa  shi ne inda su ka rika ratsawa domin isa cikin yankuna kudancin Asiya da zummar isar da sakon addinin musulunci. A can ne kuma su ke yada zango domin hutawa. Don haka yankin farko da ya zama na musulmi a kusa da Sin, shi ne wannan yankin na Arkhane.

'Yan kasuwar kasar Sin, a wancan zamanin, sun yi rubuce-rubuce da su ka rika ambaton; mazaunin Iraniyawa da ke kan iyakar Myanmar ta yanzu da kuma gundumar Yunin, da ke kudu maso yammacin kasar  ta Sin.

Wata mahangar ta tarihi kuma tana bayyana mutanen Rohinga da cewa; su mutane ne musulmi da su ke da tushe na Ariyanci.  Kuma an yi wani zamani da su ke da tsarin sarauta nasu a karkashin mulkkin Sulaiman Sha wanda ya kasance daga 1430 zuwa 1784. Sarautar tasu ta rayu na tsawon shekaru 350.

Bayan Sarkin Sulaiman a matsayin sarki na farko, Rohinga sun yi sarakuna musulmi 48 bayansa. An yi kudaden da aka rubuta Kalmar shahada a jikinsu.

Baya ga wanann, yankin ya shahara da harkar kasuwanci saboda iyakokin ruwa da ya ke da su. Tafikin Kaladan, ce mafi girma a gundumar, domin yana kwararowa ne daga kan duwatsun Himilaya, Da akwai dazuka masu duhu da su ka lulluba yankin na tsawon kaso 70%.

Har zuwa shekarar 1774 musulmin Rohinga da su ke rayuwa a wannan yankin ba su da wata matsala. Amma daga lokacin da wani mabiyin addinin Bhudda mai suna; Bhuddapaya, wanda ya sami karfin iko.

Musulmin Rohinga sun kasance masu rayuwa da makwabtansu da ba musulmi ba cikin zaman lafiya da lumana. Amma wancan mutumin mai suna Bhuddah –Paya  ya dora harsashin kiyayya da musulmi. Lokacin da ya isa wajen da musulmi su ke ya rusa tsarinsu na sharia da musulunci. Daga wancan loakcin ne kuma sabani ya fara kunno kai a tsakanin musulmi da yan bhuddah. Har zuwa shekarar 1824 da Ingila ta mamaye kasar, ta hade ta da Idiya.

A shekarar 1942 Birtaniya ta ingiza mabiya addinin bhuddah akan su fadawa musulmin Rohinga. An zubar da jinin musulmin da su ka kai 100,000. Sai dai duk da haka, musulmin ba su ja da ba baya ba wajen fada da 'yan mulkin mallaka. A karshe kuwa hakan ya tilastawa 'yan mulkin mallakar ficewa da baiwa kasar 'yanci a 1948.

Bayan kafa gwamnatin soja a kasar ta Myanmar a 1962, an ci gaba da cutar da musulmin na Rohinga.  Janar-janar din farko da su ka yi mulki a cikin kasar, sun hana musulmi zuwa aikin haji.  A shekarar 1978 kuwa sojojin kasar su ka fara kai wasu hare-hare ayankin musulmin da su ke kira da sunan: " Macijan Sarki." A sanadiyyar haka, kusan muslmin kasar 200,000 ne su ka gudu su ka bar kasar.

Wani kwararre akan tarihin Rohinga dan kasar Turkiya, Salkom Kolak Unglu, y ace; Tun bayan samun yancin kasar, Sojoji sun maida musulmi abokan gabarsu, don haka siyasarsu ita ce ta fada da su domin shafe su daga cikin kasar.

Manufar gwamnatin kasar ita ce shafe musulmi daga cikin kasar, da kuma maida ita ta addinin Bhuddha. Don haka su ke son tilasta su su rungumi addinin na Bhudda ko kuma a kore su, su fice daga kasar.

Shugaban kasar na farko,  U.Un, shi ne wanda ya kafa tubulin waccan siyasar, ya kuma sanya addinin Buddha amatsayin addinin gwamnati da kasa. A 1962, kuwa da Janar N. Win ya zama shugaban kasa, an kori dukkanin musulmin da su ke a cikin sojan kasar ta Myanmar. A 1982 kuwa an raba dukkanin musulmi da hakkin zama 'yan kasa.

Daga nan ne siyasar shafe musulmi daga cikin tarihin kasar ta Myanmar ta fara.