Zanga-zangar neman sakin Sheikh El-zakzaky A Afirka Ta kudu
Mutanen Kasar Afirka Ta Kudu Sun gudanar da Zanga-zangar neman sakin shugaban harkar musulunci na Najeriya Sheikh Yakubu Ibrahim el-zakzaky.
Tashar telbijin din Press tv, ta watsa rahoto akan zanga-zangar da mutanen Afika ta kudu suka yi, suna masu neman a sakin sheikh Yakubu Ibrahim El-zakzaky da ake tsare da shi a Najeriya.
Masu Zanga-zangar dai sun taru a bakin ofishin Jakadancin Najeriya da ya ke a birnin Pretoria dauke da kwalayen da aka rubuta yin kira da a saki malamin na addinin musulunci.
Kusan watanni biyu kenan da sojojin Najeriya su ka kai hari a cibiyar kungiyar 'yan'uwa musulmi da ke birnin Zari'a a jahar kaduna, tare da rushe gidan sheik Ibrahim Yakubu el-zakzaky.
Kawo ya zuwa yanzu kungiyar ta fitar da sunayen mutane fiye da 700 tsakanin wadanda aka kashe da kuma wadanda ake tsare da su.