May 15, 2018 16:47 UTC
  • Gwamnati Ta Gurfanar Da Sheikh Zakzaky A Gaban Kotu A Kaduna

Gwamnatin Nijeriya ta gurfanar da shugaban Harkar Musulunci a Nijeriya (Islamic Movement) Sheikh Ibrahim El-Zakzaky tare da mai dakinsa malama Zeenatu Ibrahim a gaban babbar kotun jihar Kaduna cikin matsanancin tsaro.

Kafar watsa labaran Premium Times ta ce an kawo Sheikh Ibrahim El-Zakzaky tare da mai dakin nasa ne kotun da misalin karfe tara na safiyar yau Talata, bayan an kawo su Kaduna din a daren jiya daga Abuja inda ake tsare da shi tun bayan da jami'an tsaron suka kama shi a gidansa da ke Zariya sama da shekaru biyu da suka gabata.

Lauyan Sheik El-Zakzaky din, Maxwell Kyom, ya shaida wa kafar watsa labaran ta PREMIUM TIMES cewa gwamnatin tana zargin Shehin malamin ne da laifin taro ba bisa ka'ida ba, kulla makirci da kuma kisan kai wanda ke dauke da hukuncin kisa.

Mr. Kyom ya ce ba a sami damar ci gaba da sauraran karar ba saboda mutum biyu da ake cikin wadanda ake zargi din ba su kasance a kotun ba, don haka ya bukaci da a dage sauraren karar wanda alkalin kotun mai shari'a Gideon Kurada ya bukace shi da ya rubuto bukatar tasa a rubuce. To daga karshe dai an dage sauraren kara har zuwa ranar 21 ga watan Yuni mai kamawa.

Wannan dai shi ne karon farko da gwamnatin ta gurfanar da Sheikh Zakzaky din a gaban kotun tun bayan da ta kama shi a shekara ta 2015 kuma take ci gaba da tsare shi duk kuwa da umurnin da wata kotu a Abuja ta bayar na a sake shi.

Rahotanni sun ce an tsaurara matakan tsaro a kotun da hana duk wani wanda ba ma'aikacin kotun shiga ba duk kuwa da cincirindon da mabiyar Sheikh Zakzaky din suka yi a gaban kotun a daidai lokacin da wasu suke ci gaba da zanga-zangogi a wasu sassa na kasar da nufin a sako malamin na su wanda gwamnatin ta kama shi bayan dirar mikiyar da sojoji suka yi masa da mabiyansa lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar daruruwan mutane ciki kuwa har da 'ya'yansa guda uku.

 

Tags