Najeriya : Kotu Ta Bada Umarnin Likitocin Sheikh Zakzaky, Su Duba Shi
(last modified Tue, 22 Jan 2019 17:34:52 GMT )
Jan 22, 2019 17:34 UTC
  • Najeriya : Kotu Ta Bada Umarnin Likitocin Sheikh Zakzaky, Su Duba Shi

Wata kotu a birnin Kaduna dake tarayya Najeriya, ta bada umarnin likitocin jagoran harkar musulinci ta IMN, cewa da Sheih Ibrahim Zakzaky dasu duba lafiyarshi.

Tun dai watan Disamba na shekara 2015 ne ake tsare da Sheikh Zakzaky, bayan rikicin da ya faru a garin Zaria, wanda a yayinsa aka kashe masa mabiya kimanin 300.

Lauyan malamin, ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa, sun bukaci likitocin Sheik Zakzaky dasu duba shi, duba da yadda yanayin lafiyarsa ke kara tabarbarwa, don saboda bai samun cikakiyar kula ta lafiya da yake bukata.

A don haka a cewarsa, a zaman da akayi yau Talata, kotu ta bada umurni na malamin ya gana da likitocinsa.

Ana dai zargin Sheikh Zakzaky da kisan kai da tara jama'a ba bisa ka'ida ba.

A watan Nowanba na shekara 2018 kotu ta yi watsi da bukatar bada belin Sheikh Zakzakin.

Tun dai lokacinda aka tsare shi, mabiyansa ke ci gaba da gudanar da zanga zanga a Abuja da wasu manyan biranen kasar domin neman a sake shi.