Kasar Togo ta tura Dakaru zuwa kasar Mali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i10066-kasar_togo_ta_tura_dakaru_zuwa_kasar_mali
Togo ta tura Dakarun ta zuwa kasar Mali
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Aug 23, 2016 14:44 UTC
  • Kasar Togo ta tura Dakaru zuwa kasar Mali

Togo ta tura Dakarun ta zuwa kasar Mali

Kamfanin dillancin Labaran Xin Huwa na Kasar China ya habarta cewa tawagar Dakarun tsaron kasar Togo ta isa arewacin Mali A yau Talata domin hadewa da Kungiyar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya wacce ake kira da Munusma.

Ana sa ran  sabuwar tawagar Dakarun tsaron Togon da yawan su ya kai dari  takwas da 50 za su maye gurbin Dakarun na togo da wa'adin aikin su ya kare kalkashin kungiyar ta Munusma.daga cikin Dakarun na Togo a kwai jami'an 'yan sanda da Likitoci kuma ana sa ran za a rarraba su a cibiyoyin Majalisar Dinkin Duniya dake yankunan Sevare, Gossi da kuma Kidal domin gudanar da aiyukan su a can.

Tun bayan da  kungiyoyin 'yan tawaye da kuma masu da'awar jihadi suka mamaye arewacin kasar Mali a shekarar 2012, kasar ta shiga cikin wani yanayi na rashin tsaro, a watan Avrilun shekarar 2013, Dakarun Majalisar Dinkin Duniya suka fatattaki 'yan tawaye da masu da'awar jihadi a arewacin kasar.

Amma duk da irin Dakarun wanzar da zaman lafiyar da aka jibke a kasar, har yanzu kasar na fuskantar matsalar tsaro.