Sabuwar Gwamnatin Tunisiya Ta Saba Layar Kama Aiki
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i10225-sabuwar_gwamnatin_tunisiya_ta_saba_layar_kama_aiki
Sabon Pira ministan kasar Tunisiya da ministocinsa sun saba layar kama aiki a fadar shugaban kasa.
(last modified 2018-08-22T11:28:50+00:00 )
Aug 27, 2016 18:58 UTC
  • Sabuwar Gwamnatin Tunisiya Ta Saba Layar Kama Aiki

Sabon Pira ministan kasar Tunisiya da ministocinsa sun saba layar kama aiki a fadar shugaban kasa.

Kamfanin Dillancin Labarun Faransa ya nakalto cewa; sabon pira ministan kasar Tunisiya, "Yusuf Shahid' da ministocinsa 26 da kuma mashawarta 14 sun saba layar kama aiki a gaban shugaban kasar Bajy Qa'ed al-Sibsy.

Ofishin shugaban kasar ta Tunisiya ya ce; A ranar litinin mai zuwa ce sabuwar gwamantin za ta fara aiki, bayan karbar madafun iko daga tsohuwar gwamnatin Habib al-Said da ministocinsa.

A ranar juma'ar da ta gabata ne dai mafi rinjayen 'yan majalisar kasar ta Tunisiya su ka kada kuri'ar amincewa da sabuwar gwamnati.