Kungiyar Hamas ta buda ofishin ta a kasar Aljeriya
Kungiyar kwakwarmayar musulinci ta Palastinu Hamas ta bude ofishin ta a kasar Aljeriya
Kamfanin dillancin labaran Irna na kasar Iran ya habarta ce a wannan Litinin Gwamnatin Aljeriya ta amince da bude ofishin kungiyar kwakwarmayar musulinci ta Palastinu wato Hamas a Alje babban birnin kasar.
A nasu bangare magabatan kungiyar ta Hamas sun bayyana shirin su na fara gudanar da aiyukan su a kasar, Rahoton ya ce masu sharhi kan gabas ta tsakiya da kasashen larabawa sun ce mataki da Gwamnatin Aljeriya ta dauka zai sanya fishi ga magabatan haramcecciyar kasar Isra'ila.
Ko baya ga wannan, shiga zaben kananen hukumomin da kungiyar kwakwarmayar musulinci ta Hamas tayi a yankin zirin gaza da yammacin kodin Jodan ya kara yanjo fishi na magabatan haramcecciyar kasar Isra'ilan.