An kafa sabuwar Gwamnati A kasar Tunisiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i10324-an_kafa_sabuwar_gwamnati_a_kasar_tunisiya
Sabuwar Gwamnatin hadin kan kasa ta kama aiki a Tunusiya
(last modified 2018-08-22T11:28:51+00:00 )
Aug 29, 2016 17:18 UTC
  • An kafa sabuwar Gwamnati A kasar Tunisiya

Sabuwar Gwamnatin hadin kan kasa ta kama aiki a Tunusiya

Kamfanin dillancin labaran France Press daga birnin Tunus ta ce sabuwar Gwamnatin hadin kan kasar ta samu amincewar 'yan Majalisa da kuri'a 167 daga cikin kuri'u 217 na 'yan Majalisun dokokin kasar a 'yan kwanakin da suka gabata.

Da yake jawabi ga manema labarai gabanin kama aiki gadan-gadan, sabon Firaministan kasar Youssef Chahed mai shekaru 41 a Duniya ya sha alwashin jajircewa wajen kawo sauyi da sasauci a rayuwar kuncin da al'ummar kasar suka tsinci kansu a ciki, sakamakon rashin aikin yi da tabarbarewar tattalin arziki yana mai cewa:Gwamnatin hadin kan kasa ba za ta zamo gwamnati mai tsuke bakin aljihu ba, ko kuma rage ma'aikata. Za mu koma mu tsuke bakin aljihu ne kawai in mun rasa mafita."

Chahed shi ne Firaminista mafi karancin shekaru da aka taba rike wannan mikami a Tunisiya, tun bayan da kasar ta samu 'yancin kanta daga Faransa a shekara ta 1956, kana Firaminista na bakwai da aka yi a kasar cikin kasa da shekaru shida.

A cikin sabuwar gwamnatin hadin kan kasar ta Tunisiya dai, har da mata da matasa.