Kungiyar EU Ta Yi Zargin Tafka Magudi A Zaben Shugaban Kasar Gabon
A daidai lokacin da ake jiran fitar da sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a kasar Gabon a hukumance, masu sa ido daga kungiyar Tarayyar Turai sun bayyana cewar akwai yiyuwar an tafka magudi a zaben shugaban kasar.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya bayyana cewar tawagar mutane 73 da suka sa ido kan zaben shugaban kasar Gabon din karkashin jagorancin 'yar majalisar kasar Bulgariya Mariya Gabriel, ta bayyana damuwa kan yadda aka gudanar da zaben da tace ake nuku-nuku a cikinsa.
Har ila yau shugabar tawagar masu sanya ido na kasashen Turai din ta zargi hukumar zaben kasar da boye bayanai na adadin masu kada kuri’u da yawan mazabu tana mai cewa mako guda kafin gudanar da zaben rabin mutanen da suka yi rajista ne kawai suka samu katin zaben su.
Wadannan kalaman suna zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kasar Ali Bongo da babban abokin hamayyarsa kuma tsohon shugaban kungiyar tarayyar Afirka, Jean Ping suke ikirarin lashe zaben.
Mista Ping ya kirayi shugaban Bango da ya amince da shan kaye, a daidai lokacin da bangaren shugaba Bangon kuma suke ikirarin shi ne ya lashe zaben.