Rikicin Bayan Zabe A Kasar Uganda.
Taho Mu Gama Tsakanin "Yan Sanda Da 'Yan Hamayyar Siyasar
Kamfanin Dillaancin Labarun Reuters ya nakalto cewa; Ajiya juma'a 'yansandan Uganda sunyi amfani da barkonon tsohuwa akan magoyan bayan dan hamayyar siyasa Kizza Basigye.
Baya ga babban birnin kasar Kampala, an yi taho mu gama a tsakanin magoya bayan 'yan hamayyar siyasa da kuma 'yansandan a garuru daban-daban na kasar.
'Yan hamayyar dai suna nuna kin amincewarsu ne da yadda aka gudanar da zaben shugaban kasa da aka sami jinkiri a wurare daban-daban.
Hukumar Zaben kasar dai ta bada hakuri ga al'ummar kasar saboda jinkirin aikewa da kayan aiki a mazabu.
Mutane miliyan 15 ne dai 'yan kasar ta Uganda su ka kada kuri'arsu, domin zabar sabon shugaban kasa da kuma 'yan majalisa 290.