Mutane Uku Sun Mutu A Rikicin Bayan Zaben Shugaban Kasar Gabon
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i10453-mutane_uku_sun_mutu_a_rikicin_bayan_zaben_shugaban_kasar_gabon
Rahotanni daga kasar Gabon sun bayyan cewar alal akalla mutane 3 sun rasa rayukansu kana wasu daruruwa kuma suna hannu 'yan sanda biyo bayan rikicin da ya barke a kasar bayan sanarwar da aka yi cewa shugaban kasar mai ci Ali Bongo shi ne ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar Asabar din da ta gabata.
(last modified 2018-08-22T06:58:51+00:00 )
Sep 01, 2016 12:51 UTC
  • Mutane Uku Sun Mutu A Rikicin Bayan Zaben Shugaban Kasar Gabon

Rahotanni daga kasar Gabon sun bayyan cewar alal akalla mutane 3 sun rasa rayukansu kana wasu daruruwa kuma suna hannu 'yan sanda biyo bayan rikicin da ya barke a kasar bayan sanarwar da aka yi cewa shugaban kasar mai ci Ali Bongo shi ne ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar Asabar din da ta gabata.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar rikici ya barke alal akalla yankuna 9 da suke makwabtaka da birnin Libreville babban birnin kasar Gabon din lokacin da magoya bayan dan takaran da ya sha kaye a zaben Jean Ping suka fito kan tituna a yau din nan Alhamis don nuna rashin amincewarsu da sakamakon zaben da aka sanar din; lamarin da ya sanya su fito na fito da jami'an tsaro.

Ministan cikin gidan kasar Pacome Moubelet ya ce mutane uku sun rasa rayukansu sannan kuma wasu guda 1,100 suna hannun 'yan sanda bayan da 'yan sandan suka fada musu da nufin tarwatsa su.

Tun da fari dai Mr. Jean Ping, wanda ya ce shi ne ya lashe zaben ya sanar da cewa  jami'an tsaro sun kashe mutum biyu sakamakon bude wuta da suka  yi a lokacin da suka kai hari helkwatar jam'iyyarsu a yau din nan Alhamis

Sakamakon zaben dai wanda aka sanar a jiya Laraba, ya bayyana shugaba Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben zaben da kaso 49.8, a inda shi kuma Jean Ping ya samu kaso 48.2.