Sabuwar Gwamnatin Tunusiya Ta Bayyana Damuwa Kan Habakar Ayyukan Ta'addanci A Kasar
Sabon fira ministan Tunusiya ya bayyana cewa: Kasarsa tana cikin halin tsaka mai wuya a fagen yaki da ayyukan ta'addanci don haka zata yi amfani da dukkanin karfinta domin ganin ta murkushe duk wani nau'in ta'addanci a kasar.
A ziyarar da ya kai lardin Qasirain domin gani da ido a wajajen da aka kwama tsakanin jami'an tsaron kasar da gungun 'yan ta'addan kungiyar Uqbah bin Nafi'u a kwanakin baya: Fira minista Yusuf Assha'hid ya jaddada yin kira ga dukkanin bangarorin kasar da su hada kai da jami'an tsaron kasar domin ganin an kawo karshen ayyukan ta'addanci a duk fadin kasar.
Yusuf Assha'hid gwamnati tana tsananin takaicin ganin yadda matakan tsaro suke ci gaba da tabarbarewa a lardin Qasirain, don haka ya yi kira ga al'ummar lardin kan su bada cikakken hadin kai ga gwamnati musamman jami'an tsaron kasar domin murkushe 'yan ta'adda da kawo karshen ayyukan ta'addanci a yankunansu.