Mali : Sojoji Sun Karbe Ikon Yankin Boni
Rahotanni dake cin karo da juna daga Mali na cewa sojojin kasar sun karbe ikon yankin Boni daya fada hannun mayakan jihadi.
Kanfanin dilancin labarai na faransa AFP ya rawaito cewa mayakan jihadi sun fice daga yankin a cikin daren jiya juma'a wayewar safiyar wannan Asabar, kafin daga bisani sojojin Mali su dawo yankin a wajajen karfe takwas na yau kamar yadda wata majiyar soji ta tabbatar.
Ko baya ga hakan wata majiyar tsaro a tawagar MDD a kasar ta mali ta tabbatar da wannan labarin, bayan da wasu jiragan sama masu saukar ungulu tare da haddin gwiwar rundinar sojin kasar suka yi shawagi a yankin na Boni da mayakan jihadi suka kwace.
Saidai a cewar wasu rahotanni mayakan jihadin sunyi garkuwa da wani wakilin al'umma yankin wanda suke zargi da baiwa dakarun kasar bayanai ta wayar tarho.
Wasu bayanai na daban sun ce kura ta lafa a yankin koda yake al'umma na cikin zamen dar-dar.
A jiya ne dai mayakan jihadi da suka farmawa ma'aikataun gwamnati suka kuma kwace ikon garin na Boni dake jihar Mopti dake tsakiyar kasar bayan da sojoji suka arce daga yankin.