Ministan Tsaron kasar Mali ya yi murabus
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i10564-ministan_tsaron_kasar_mali_ya_yi_murabus
An sauke Ministan tsaron Mali daga kan mikaminsa sanadiyar matsalar tsaro a tsakiyar kasar
(last modified 2018-08-22T06:58:52+00:00 )
Sep 04, 2016 01:19 UTC
  • Ministan Tsaron kasar Mali ya yi murabus

An sauke Ministan tsaron Mali daga kan mikaminsa sanadiyar matsalar tsaro a tsakiyar kasar

Kamfanin dillancin Labaran kasar Faransa ya habarta, kwana guda, bayan wani hari da wasu 'yan bindiga masu da'awar Jihadi suka kai garin Boni, inda suka kwace iko da garin na wani lokaci.ya yi sanadiyar sauke Tieman Hubert Coulibaly Ministan tsaron kasar Mali daga kan mikaminsa.

Wani Jami'in Ma'aikatar tsaron kasar ya shaida cewa matsalar tsaron baya bayan nan da ta mamaye tsakiyar kasar ne ya yi sanadiyar sauke Coulibaly daga kan mikaminsa saboda kasawar da ya yi wajen tabbatar da tsaro da kuma kare kasar daga mamayar masu da'awar Jihadi.

Rahoton ya ce Gwamnatin ta Mali ta gabatar da Mista Abdoulaye Idrissa Maiga tsohon ministan kasa a matsayin wanda zai maye gurbin kujerar Tieman Hubert Coulibaly a ma'aikatar tsaron kasar.

A ranar Juama'ar data gabata ne sojojin Malin suka fice daga garin Boni, bayan harin da 'yan bindigar suka kai, inda suka bude-wuta a kan wasu gine-gine, tare da banka wa wasu daga ciki wuta, A ranar Assabar kimanin karfe takwas na safe Sojojin Mali da na Majalisar Dinkin Duniya sun kwace garin daga hanun mayakan.

Rahoton ya ce'yan bindigar sun sace wani jami'in gwamnati a yayin ficewar su daga cikin garin na Boni.