Daruruwan Yara Yan Gudun Hijira Sun Bace A Kasar Britania
(last modified Sun, 04 Sep 2016 11:52:10 GMT )
Sep 04, 2016 11:52 UTC
  • Daruruwan Yara Yan Gudun Hijira Sun Bace A Kasar Britania

Wata Jaridar kasar Britania The Independant ta bada labari a shafinta na yanar gizo a yau Lahadi cewa daruruwan yara yan gudun hijira sun bace a kasar Britania.

Independant ta kara da cewa tun daga farkon wannan shekara ta 2016 zuwa yanzu yara yan gudun hijira 360 ne suka bace a kasar, kuma wannan yana nuna cewa akwai matsalat satar yara da kuma keta huruminsu.

Jaridar ta kara da cewa a cikin shekaru 5 da suka gabata yara kanana dubu 9,287 suka shiga kasar Britania ba tare da iyayensu ba, kuma ba tare da wani wanda yake kula da su ba.

Har'ila yau binciken da sashin aikata laifuffuka na tarayyar turai ta gudanar a farkon wannan shekara ya nuna cewa dubban yara yan gudun hijira ne suka bace a duk fadin kasashen nahiyar.

Matsalolin tsaro a kasashen Syria, Iraqi, Yemen, Nigeria da kuma Sudan na daga cikin matsalolin da suka jawo kwararar yan gudun hijira zuwa kasashen turai a cikin shekaru 5 da suka gabata.