Mali: Ana Sukar Shugaban Kasar Da Gajiyawa Wajen Tafiyar Da Aiki
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i10585-mali_ana_sukar_shugaban_kasar_da_gajiyawa_wajen_tafiyar_da_aiki
An Sukar Ibrahim Bubakar Keita Da Gajiyawa
(last modified 2018-08-22T06:58:52+00:00 )
Sep 04, 2016 14:27 UTC
  • Mali: Ana Sukar Shugaban Kasar Da Gajiyawa Wajen Tafiyar Da Aiki

An Sukar Ibrahim Bubakar Keita Da Gajiyawa

Cibiyar Watsa Labarun Afirca Times ta ambaci cewa; Adaidai lokacin da shugaban kasar Mali Ibrahim Bubakar Keita ya shiga shekaru akan mulki, wani sashe na al'ummar kasar suna bayyana cewa ya gajiya wajen tafiyar da mulkinsa.

Daga cikin alkawullan zaben da shugaban Mali ya yi wa al'ummar kasar da akwai samar da aikin yi ga mutane dubu dari biyu, wanda kawo ya zuwa yansu,kididdigar hukuma ta ce  mutane 121,000 ne kadai su ka sami aiki.

Sai dai wata kungiya mai suna; "Bi-Ton" ta ce babu gaskiya acikin kididdigar ta gwamnati.

A fagen tsaro ma an tuhumi gwamnatin shugaba Ibrahim Keita da gajiyawa wajen tabbatar da tsaro duk da cewa an cimma yarjejeniyar sulhu da masu dauke da makakai.

Kawo ya zuwa yanzu, masu wuce gona da iri sun zama kalubalemai girma ta fuskar tsaro a gaban gwamnatin kasar.