Ana Shirin Rantsar Da Shugaban Zambiya Bayan Watsi Da Karar Abokin Hamayya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i10633-ana_shirin_rantsar_da_shugaban_zambiya_bayan_watsi_da_karar_abokin_hamayya
Kotun kundin tsarin mulkin kasar Zambiya ta yi watsi da karar da dan takarar da ya sha kaye a zaben shugaban kasar da aka gudanar Hakainde Hichilema lamarin da zai share fagen rantsar da shugaban kasar Edgar Lungu a wani wa'adi na shekaru biyar a kan karagar mulkin kasar
(last modified 2018-08-22T06:58:53+00:00 )
Sep 05, 2016 11:41 UTC
  • Ana Shirin Rantsar Da Shugaban Zambiya Bayan Watsi Da Karar Abokin Hamayya

Kotun kundin tsarin mulkin kasar Zambiya ta yi watsi da karar da dan takarar da ya sha kaye a zaben shugaban kasar da aka gudanar Hakainde Hichilema lamarin da zai share fagen rantsar da shugaban kasar Edgar Lungu a wani wa'adi na shekaru biyar a kan karagar mulkin kasar

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya bayyana cewar a kwanakin baya ne dai Mr. Hichilema ya bukaci da a yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Augustan da ya gabata da kuma shirya wani sabon zaben bayan da yayi ikirarin an tafka magudin zaben lamarin da kotun ta yi watsi da shi.

Jim kadan bayan watsi da karar da kotun ta yi a yau Litinin, gwamnatin kasar  Zambiya ta sanar da cewa a ranar da cewa  za a rantsar da shugaba Edgar Lungu da mataimakinsa a ranar 13 ga watan nan na Satumba a birnin Lusaka, babban birnin kasar don fara wa'adin mulkinsu na shekaru biyar masu zuwa.

Hukumar zaben kasar ECZ ta sanar da cewa shugaba Lungu shi ne ya lashe zaben da aka yi din a ranar 11 ga watan Augustan da ya gabata inda ya samu kashi 50.35 na kuri'un da aka kada kana shi kuma babban abokin hamayyarsa na jam'iyyar UPND Mr. Hakainde Hichilema ya zo na biyu inda ya samu kashi 47.35 cikin dari na kuri'un da aka kada.