Kasashen Chadi Da Canada Sun Jaddada Bukatar Karfafa Dangantakar Kasashen Biyu
Gwamnatocin Kasashen Canada da Chadi sun jaddada bukatar karfafa dangantakar kasashen biyu, a taron kungiyar kasashe 20 da ke gudana a halin yanzu a kasar China.
Shafin yanar gizon labarai na Africa Time ya bayyana cewa shugaban kasar Chadi Idris Deby ya gana da Priministan kasar Canada Justin Trudeau a birnin Hang-Zhou na kasar China inda ake gudanar da taro kungiyar kasashe 20 na 11 a yau Talata.
Labarin ya kara da cewa Ministan tattalin arziki na kasar Chadi Maryam Mohammad Noor da kuma karamin ministan harkokin wajen kasar ta Chadi Kade Dilguem Elisabeth duk sun sami halattar ganawar shugabannin biyu.
A cikin watan Febrerun shekara ta 2015 ne gwamnatin kasar Chadi a karon farko ta bude ofishin jakadancinta a birnin Otawa na kasar Canada don karafafa dangantarkar kasashen biyu.